Everton ta yi tayin sayen Balogun daga Monaco
Everton ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan gaba na Monaco, Folarin Balogun — wanda kulob ɗin na Faransa ya ƙiyasta darajarsa ta kai fam miliyan 40.
Everton na son ƙarfafa ɓangaren ƴan wasanta na gaba kafin a rufe kasuwar musayar ƴan wasa a ranar Talata, inda take zawarcin Balogun da kuma ɗan wasan gaba na Tottenham, Richarlison.
Ana ganin Richarlison na da shakku game da komawa Everton, kulob ɗin da ya baro domin komawa Spurs a shekarar 2022.
Sai dai Everton na ci gaba da nuna sha'awarta ta sayen ɗan wasan gaba na Amurka, Balogun, kuma ta riga ta gabatar da tayi ga ɗan wasan mai shekara 25.
Ana jiran a ga ko tayin ya isa ya gamsar da Monaco har ta amince ta saki Balogun.
Amma tsohon ɗan wasan na Arsenal ya zama babban ɗan wasan da Everton ke son ɗauka kafin ƙarshen kasuwar wannan bazarar.
Balogun ya kasance cikin wani babban cece-kuce a lokacin gasar cin kofin duniya, inda aka kore shi daga filin wasa saboda mummunan ƙetar da ya aikata a wasan da suka buga da Bosnia-Herzegovina a zagayen ƴan 32 na gasar, kuma ya kamata a ce an dakatar da shi nan take.
Sai dai kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ya dage dakatarwar tasa na tsawon shekara guda — matakin da ya jawo suka sosai, musamman bayan da aka gano cewa Shugaban Amurka Donald Trump da jami'an Fadar White House sun yi tunkari hukumar FIFA domin neman a sassauta hukuncin da aka yi wa ɗan ƙasar Amurkar.