Wane ne ke jagorantar Najeriya idan Tinubu da Shettima ba sa nan?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Tafiya hutun da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi a farkon makon nan yayin da mataimakinsa Kashin Shettima ke halartar taron Tarayyar Afirka a ƙasar Angola ta sake dawo da muhawarar da ake tafkawa akai-akai a ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a kafar sada zumunta jagoran adawa na na ƙasar Atiku Abubakar ya ce "duk da cewa babu giɓi a dokance, amma akwai giɓi a jagoranci na siyasa".

Wannan kalami nasa sun ja hankali tare da haifar da muhawara a fagen siyasa da na shafukan sada zumunta. Inda ake tambayar wane ne ke jagorantar Najeriya a loakacin da shugaban ƙasa da mataimakinsa ba sa ƙasar?

Tambaya mai sarƙaƙiya

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana tafiyar Tinubu a matsayin "hutun aiki." Inda fadar ta dage kan cewa shugaban zai ci gaba da ayyukansa, ministocinsa da manyan hafsoshin tsaro za su riƙa ba shi bayanai kowace rana kuma zai iya ɗaukar matakai masu muhimmanci daga duk inda yake.

Hadiman shugaban ƙasar na cewa bai watsar da jagorancin ƙasar ba duk da cewa ba ya nan.

Me doka ta ce?

Me doka ta ce?

Sashe na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa a duk lokacin da shugaban ƙasar ya tafi hutu ko ya gaza sauke nauyin da ke kansa, zai miƙa takarda a rubuce ga shugaban majalisar dattijai da na wakilai yana sanar da su.

Wani masanin shari'a kuma malamai a makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya Slaiman Santuraki ya ce: "Gyaran da aka yi wa sashe na 145 a bayan halin da aka shiga a lokacin Yar'adua da Jonathan shi ne 'idan shugaban ƙasa zai tafi hutu ko zai yi wani abu da zai sa ba zai iya gudanar da aikinsa na shugaban ƙasa ba, shi ne ya rubuta wa majalisa takarda cewa ba zai iya gudanar da aikinsa ba, mataimakin shugaban ƙasa zai riƙe muƙamin har sai ya dawo'.

"Sai kuma ƙaramin sashe na 2 na wannan sashe wanda ya ce 'idan har bai iya yin hakan ba ko kuma ya ƙi ya yi hakan, bayan kwana 21 to a lokacin majalisar dattijai da ta wakilai za su iya amincewa ta hanyar rinjaye, dokar da za ta bai wa mataimakin shugaban ƙasa damar riƙe muƙamin shugaban ƙasa har sai shugaban ƙasar ya dawo ya tura takarda cewa ya dawo," in ji Sulaiman Santuraki.

Da zaran shugaban ƙasa ya miƙa takarda ga majalisar dokoki, mataimakin shugaban ƙasar zai zama mai riƙon muƙamin shugaban ƙasa har sai lokacin da shugaban ƙasar ya sake tura wata takardar wadda za ta mayar da ragamar ƙasar a hannun shugaban ƙasa.

A bayanan da ake da su, waɗanda al'umma ke da masaniya a kai, ba su nuna cewa Tinubu ya tura irin wannan takarda ba game da tafiyar tasa ta wannan karo.

Saboda haka a yanzu Tinubu shi ne ke jan ragamar ƙasar bisa doka, a ko ina yake a duniya. Mataimakin shugaban ƙasa ba zai zamo shugaban riƙo kawai daga lokacin da shugaban ƙasa ya yi tafiya zuwa wata ƙasa.

Sai dai da alama muhawarar da ake yi a ƙasar a wannan lokaci ba game da abin da doka ta ce ba ne kawai. Ya shafi halin da ake ciki da kuma abubuwan da suka faru a shekarun baya.

Ba a manta abin da ya faru lokacin Yar'adua ba

Muhawara game da rashin kasancewar shugaban Najeriya a gida na da alaƙa da takun-saƙar da aka tafka a lokacin mulkin Umaru Yar'adua.

A ƙarshe-ƙarshen shekarar 2009, Umaru Yar'adua ya yi wata tafiya zuwa Saudiyya domin jinya ba tare da ya miƙa takardar da kundin tsarin mulki ya tanada ba ga majalisar dokoki.

Yayin da rashin lafiyarsa ta yi ƙamari kuma lokacin jinyarsa ya tsawaita, ƙasar ta shiga ruɗani game da wanda a lokacin doka ta bai wa ikon jagorantar ƙasar.

Lauyoyi da da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun riƙa musayar yawu sannan ƴan siyasa suka riƙa nuna fargaba game da 'giɓi da aka samu' a shugabanci.

Lamarin ya yi ƙamari sosai ta yadda har sai da majalisar dokokin ƙasar ta ƙaƙaba 'dokar buƙata' a watan Fabarairun 2010, inda aka bai wa mataimakin shugaban ƙasa Goodluck Jonatahn ikon jan ragamar ƙasar.

Abubuwan da suka faru a lokacin sun sauya yadda ƴan Najeriya ke kallon tafiye-tafiyen shugaban ƙasa kuma tun daga wancan lokaci duk wata tafiya zuwa ƙasar waje da shugaban ƙasa mai ci zai yi sai an fara yin tambayoyi game da tanadin doka.

Tsarin Buhari da Osinbajo

Sai dai gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta fuskanci wata alƙibla.

Buhari ya miƙa wa mataimakinsa riƙon mulki sau da dama a lokacin tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen ƙetare.

Osinbajo ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa musamman a lokacin da Buari ya kwashe dogon lokaci yana jinya a shekarar 2017.

An yi wa wannan hakan kallon wani mataki na kauce wa faruwar abin da ya faru a lokacin Yar'adua da kuma nuna misali na bin doka.

Sai dai ko a lokacin mulkin Muhammadu Buhari an riƙa yin tambayoyi a lokacin da shugaban ƙasar da mataimakinsa ba sa cikin ƙasar a lokaci guda.

A watan Satumban 2022 Shugaba Buhari ya yi tafiya zuwa New York na Amurka domin halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin da shi kuma Yemi Osinbajo ya halarci janazar Sarauniya Elizabeth a Birtaniya.

Lamarin ya janyo suka da muhawara a tsakanin al'umma kan ko ya cancanta shugaban da mataimakinsa su kasance a wajen ƙasar a lokaci guda.

Masharhanta sun yi bayanin cewa kundin tsarin mulki bai buƙaci tilas sai shugaban ƙasa ko mataimakinsa sun kasance a cikin ƙasa a kowane lokaci ba.

Wannan lamarin ya yi kama da abin da ke faruwa a yanzu.

Tsarin Tinubu

Tun bayan hawansa kan mulki a watan Mayun 2023, Tinubu bai yi koyi da Buhari ba a wannan fanni na miƙa wa mataimakinsa mulki idan zai yi tafiya.

Masu sukar shugaban ƙasar na cewa domin martaba sashe na 145 na kundin tsarin mulki ya kamata shugaban ƙasa idan zai je hutu ya miƙa riƙon mulki a hukumance ga mataimakinsa.

Amma masu goyon bayan shugaban ƙasar na cewa shugaban zai iya sauke nauyin da ke kansa sanadiyyar ci gaban zamani, kuma kundin tsarin mulki bai wajabta wa shugaban ƙasa miƙa riƙon mulki kawai domin zai fita daga ƙasar ba.

Mene ne halasci ko haramcin ƙin bai wa mataimaki riƙo?

Wasu masu sharhi kan kundin tsarin mulki na ganin cewa babu wani giɓi matuƙar shugaban ƙasa zai iya gudanar da ayyukansa, a ko ina yake.

Saboda haka idan za a duba tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, shugaba Tinubu ne zai ci gaba da jan ragamar ƙasar har sai lokacin da ya miƙa takarda ga majlisar dokoki cewa ya miƙa riƙon mulki a hannun mataimakinsa, ko kuma idan majalisar ta ga ya wuce wa'adin da ya kamata, sannan ta zartar, bisa rinjaye ƴanmajalisa cewar an damƙa ragamar mulki ga mataimakinsa..