Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 31 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman MINJIBIR

  1. Pezeshkian ya gana da Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif a gefen taron Shanghai

    Masoud Pezeshkian ya gana da Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, a gefen taron kungiyar hadin kan Shanghai (SCO) da aka gudanar a Kyrgyzstan.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, IRNA, ya ce ba tare da bayar da cikakkun bayanai ba cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

    Pakistan ita ce babbar mai shiga tsakani a tattaunawar Iran da Amurka, kuma jami'an kasashen biyu suna ganawa akai-akai tun bayan taron Islamabad.

    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, Shugaban Rasha Vladimir Putin, Masoud Pezeshkian da wasu sama da shugabanni goma sha biyu sun hallara a Kyrgyzstan domin halartar taron kwanaki biyu na Kungiyar Hadin Kan Shanghai.

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, shi ma yana tare da Mista Pezeshkian a wannan tafiya.

  2. 'An sayar da kujerun aikin Hajjin 2027 gaba ɗaya a Kano'

    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa an sayar da dukkan kujeru 3,050 da aka ware wa jihar domin gudanar da aikin Hajjin shekara ta 2027.

    Babban Daraktan Hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle, ya ce an samu nasarar ne bayan kira ga maniyyata da ke buƙata da su aika masu sakonni su biya kuɗaɗen Hajji tare da kammala takardunsu.

    Ya kuma ce akwai sama da mutum 200 da ke jiran samun gurbi idan wasu suka gaza cika sharuddan tafiya.

    Matawalle ya gargaɗi waɗanda suka biya kuɗin hajji amma har yanzu ba su gabatar da fasfofinsu na intanet (e-passport) ba da su yi hakan kafin ranar 5 ga Satumba, yana mai cewa duk wanda ya gaza zai iya rasa kujerarsa duk da ya biya kuɗin hajjin.

    Ya ce hukumar na shirin inganta ayyukan Hajjin 2027, ciki har da rage yawan gidajen da ake saukar da alhazai a Saudiyya domin sauƙaƙa kulawa da su da samar musu da abinci, kula da lafiya da sauran buƙatu.

  3. Ƙungiyar tsaron Saudiyya Pakista da Turkiyya sun gana a karon farko

    Ministocin harkokin waje da manyan jami’an tsaro daga Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun taru a Istanbul a ranar Litinin, 31 ga Agusta, domin halartar taron farko na wani kwamitin da aka kafa a ƙarƙashin Yarjejeniyar Tsaro ta Makka.

    Daga cikin jami’an da suka halarci taron akwai Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud, Ministan Harkokin Wajen Pakistan Muhammad Ishaq Dar, Ministan Tsaron Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, Babban Hafsan Sojin Pakistan Field Marshal Asim Munir, Babban Hafsan Sojin Turkiyya Janar Selçuk Bayraktaroğlu, da Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif.

    Kasashen nan uku masu rinjayen al’ummar Musulmi mabiya Sunni, wadanda ke kawance da Amurka, sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Tsaron Juna ta Makka kimanin makonni uku da suka gabata a birnin Makka na Saudiyya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce kasashen sun hada kai ne sakamakon damuwa kan yakin Iran da sauran rikice-rikicen yankin, ciki har da harba makaman linzami da Iran ta yi kan kasashen da ke fitar da man fetur a yankin Tekun Fasha.

    An bayyana manufar Yarjejeniyar Tsaro ta Makka da cewa ita ce “ƙarfafa matakan kariya na bai ɗaya domin daƙile duk wani nau’in hari.” Kamar tanadin kariyar haɗin gwiwa da ke cikin Mataki na 5 na Yarjejeniyar NATO, yarjejeniyar ta tanadi cewa duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashe uku za a ɗauke shi tamkar hari ne kan dukkaninsu.

    Wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta shaida wa Reuters cewa “batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa da ƙasa za su kasance cikin ajandar taron.”

    Kara karantawa: Yarjejeniyar Makka; an gudanar da taron haɗin gwiwa na farko tsakanin Turkiyya, Pakistan da Saudiyya a Istanbul.

  4. Hotunan yadda ake taimakon waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa da tallafi a Nepal

    Ga wasu hotunan da ke nuna yadda sojoji ke jagorantar ayyukan ceto da raba kayan agaji ga dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Nepal.

    Ana ganin jami’an tsaro suna raba abinci, ruwa da sauran kayan masarufi, yayin da suke taimakawa wajen kwashe mutanen da suka maƙale zuwa wuraren da suka fi tsaro.

    Haka kuma hukumomi da kungiyoyin agaji na ci gaba da tallafa wa iyalan da suka rasa muhallansu domin rage wahalhalun da bala’in ya jawo.

  5. Yadda sarki Sanusi ya jagoranci hawan sallar Gani a jihar Kano

    Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya jagoranci sallar Gani karo na farko a birnin Kano.

    Ɗaruruwan mutane ne suka hau dawakai kuma suka caɓa ado domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

    Sallar Gani wata tsohuwar al'ada ce da Masarautar Kano ke gudanarwa domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

    A bana, hawan ya gudana na tsawon kwanaki biyu, inda Sarkin Kano ya zagaya sassa daban-daban na birnin tare da rakiyar masu sarauta, mahaya da kuma dubban masu kallo da suka fito domin shaida bikin.

    Hawan na bana ya jawo hankalin al'umma sosai, inda manyan baƙi da matasa da tsofaffi suka hallara domin nuna farin cikinsu.

    Rahotanni sun bayyana cewa a yayin hawan, Sarkin Kano ya yi addu'o'i ga al'ummar Kano da Najeriya baki ɗaya, musamman na zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali.

  6. Amurka ta samu galaba a kan Iran a hukumance - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa an samu galaba a kan Iran a yaƙin da ake yi, yana mai bayyana cewa ƙasar ta shiga wani hali na rauni da rikice-rikice da ya sa ba za ta iya taka muhimmiyar rawa a duniya ba.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Iran "kasa ce da ta gaza gaba daya", yana mai zargin cewa ba ta da ƙarfin rundunar ruwa da ta sama, kuɗinta ya yi rauni, ba ta iya biyan jami'an tsaro albashinsu, sannan hauhawar farashi ya yi ƙamari yayin da shugabanninta suka kasa wakiltar ƙasar yadda ya kamata.

    Trump ya kuma zargi gwamnatin Iran da amfani da ƙarfi kan masu zanga-zanga a cikin ƙasar, yana mai cewa an kashe mutane da dama, kuma ya kamata a gurfanar da shugabannin ƙasar a gaban kotu bisa zargin aikata laifukan yaƙi da kuma cin zarafin bil'adama.

  7. Ƙorafe-ƙorafen Najeriya kan Afirka ta Kudu da Tinubu ya gabatare a taron AU

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da ƙorafi a wajen taron Tarayyar Afirka AU akan hare-haren ƙyamar baƙi da na nuna wariya da ake yi wa 'yan ƙasashen Afirka a Afirka ta Kudu.

    Shugaba Tinubun, wanda mataimakinsa Kashim Shettima, ya wakilta a wajen taron, ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan hare-hare na barazana ga haɗin kai da zaman lafiya a nahiyar.

    Shugaban na Najeriya, ya kuma ce irin waɗannan hare-hare suna tauye ƙoƙarin gina nahiyar Afirka mai cike da haɗin kai da zaman lafiya, tare da yin kira ga shugabannin Afirka su ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.

    Tinubu ya kuma buƙaci a sanya batun cikin ajandar zama na 40 na Babban Taron Shugabannin Tarayyar Afirka domin a tattauna hanyoyin magance matsalar da hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare nan gaba.

  8. Yadda iyalai ke alhinin ‘yan uwansu da suka mutu a ambaliyar ruwa a Nepal

    Ga wasu hotunan da ke nuna irin baƙin cikin da iyalai ke ciki bayan rasa ‘yan uwansu a ambaliyar ruwa mai tsanani da ta yi sanadiyyar asarar rayuka a Nepal.

    Ana ganin mutane suna taruwa domin yin addu’o’i da jana’iza, yayin da wasu ke kuka da jimamin waɗanda suka rasa, a cikin wani yanayi na baƙin ciki da ambaliyar ta haifar a al’ummomin da abin ya shafa.

  9. Gaske ne Opay zai dakatar da aiki a watan Satumba?

    Alamu na nuna cewa cikin ƴan Najeriya da dama ya ɗuri ruwa bayan wani saƙon bogi da ya yi yawo a kafafen sada zumunta ya yaɗa cewa kamfanin zai dakatar da aiki a ranar Litinin.

    A ranar 30 zuwa 31 ga Agustan 2026, wani saƙo na bogi ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana cewa OPay zai dakatar da harkokinsa daga ranar 1 ga watan Satumban 2026, kuma ya buƙaci kwastomomi su cire kuɗaɗensu.

    Sai dai OPay ya fito fili ya musanta wannan rahoto, yana mai cewa ƙarya ce kuma an ƙirƙiri labarin ne domin yaudarar jama'a.

    Ba a dai san takamaiman wanda ya ƙirƙiri wannan saƙon na bogi ba, amma akwai wasu dalilai da ake yawan ganin irin waɗannan jita-jita suna yaɗuwa.

  10. Iran ta musanta iƙirarin Trump na kai harin da ya lalata tsibirin Kharg

    Kamfanin Man Fetur na Ƙasar Iran (NIOC) ya musanta iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump cewa tsibirin Kharg ya lalace sakamakon hari, yana mai cewa tsibirin na cikin kwanciyar hankali kuma harkokin man fetur na ci gaba kamar yadda aka saba.

    Shugaban kamfanin, Hamid Bord, ya bayyana kalaman Trump a matsayin "marasa ma'ana", yana mai cewa babu wata matsala da ta shafi ayyukan man fetur a tsibirin.

    Bord ya ce Kharg ya sha fuskantar hare-hare daga Amurka da Isra'ila a lokuta daban-daban, amma ma'aikatan masana'antar mai da abokan hulɗarsu sun tabbatar da cewa ayyukan samar da mai ba su tsaya ko na ɗan lokaci ba.

    Ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta, an ci gaba da gudanar da ayyuka a tsibirin ba tare da tangarda ba.

    Trump dai ya wallafa wani bidiyon da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI a kafar sadarwarsa ta Social Truth, inda ya yi iƙirarin cewa tsibirin Kharg ya watse gaba ɗaya.

    Sai dai kawo yanzu babu wani rahoto da ke nuna cewa an kai hari kan tsibirin ko kuma an samu wata barna a wurin.

  11. Nepal na fasa hanyoyin ƙarƙashin ƙasa domin ceto mutanen da suka maƙale

    Mahukunta a Nepal na fasa wasu hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke cikin tsaunuka domin isa ga ɗaruruwan mutanen da ake zargin sun maƙale a ramukan tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta Trishuli-3A da ke gundumar Rasuwa.

    Ana kyautata zaton cewa da yawa daga cikin mutum 933 da ake nema har yanzu suna cikin ramukan, lamarin da ke ƙara tsananta damuwa kan yiwuwar ceton waɗanda ke raye.

    Da misalin ƙarfe biyu na daren Litinin ne aka gudanar da wani fashewa da aka tsara a wurin aikin domin samar da damar shiga ramukan.

    Hakan na zuwa ne bayan ofishin firaministan Nepal ya sanar a ranar Lahadi cewa ana ƙara ƙaimi wajen ayyukan ceto a tashar Trishuli-3A, ciki har da amfani da fashe-fashe domin buɗe hanyoyin shiga.

    Jami’an ceto sun kuma yi amfani da manyan injinan tona ƙasa guda biyu wajen haƙa rami mai zurfin kusan mita 10.

    Rundunar sojin Nepal ta ce ana ci gaba da aikin kwashe ruwa, laka da tarkacen da suka mamaye cikin ramin Trishuli-3A sakamakon ambaliyar ruwan ta da auku domin sauƙaƙa ayyukan ceton.

  12. Tinubu ya zaɓi ya yi hutu a daidai lokacin da matsaloli ke addabar ƙasar - Atiku

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar ya soki tafiyar da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi zuwa Turai na tsawon makwanni uku, yana mai cewa Tinubu ya zaɓi ya yi hutu a daidai lokacin da ƙasar ke cikin mawuyacin hali da ke buƙatar shugabanci.

    Atiku ya ce duk da cewa shi ma ya taɓa yin tafiye-tafiye da zama a ƙasashen waje, akwai bambanci mai girma tsakanin tafiyar mutum mai zaman kansa da ta shugaban kasa mai ci.

    A cikin sanarwar da ya fitar, Atiku ya ce ‘yan Najeriya na fama da tsadar rayuwa, inda farashin man fetur ya kai matakin da ya gagari talakawa, yayin da iyalai da dama ke fama da matsalar ciyar da kansu.

    Ya kuma yi nuni da yadda kudin sufuri suka ƙaru, lamarin da ya sanya yin tafiya zuwa ƙauyuka da garuruwa ya zama ƙalubale ga mutane da dama.

    Atiku ya ƙara da cewa "matsalar tsaro na ci gaba da jefa rayukan ‘yan Najeriya cikin hadari inda a irin wannan lokaci ne ya kamata shugaban kasa ya kasance tare da al’ummarsa."

    Ya ce abin mamaki ne yadda Shugaba Tinubu ya bar ƙasar zuwa Turai a daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, yake wata tafiya ta aiki a ƙetare.

    Atiku ya ce shugabanci ba kawai mallakar ikon riƙe muƙami ba ne, har ila yau yana buƙatar sanin lokacin da kasa ke buƙatar shugabanta ya kasance a gida.

    Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza gano irin wahalhalun da ‘yan kasa ke ciki, yana mai cewa idan aka ba shi dama zai mayar da Najeriya kasa mai saukin rayuwa ga jama’arta.

  13. Shawarwarin da Tinubu ya bai wa ƙasashen Afirka a taron AU

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci ƙasashen Afirka su ɗauki wasu matakai domin inganta haɗin kai da tsaron nahiyar.

    Shugaba Tinubu, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta a taron AU a aka gudanara a Luada, ya bayyana wasu shawarwari da ya ce idan nahiyar ta ɗauka za u taimaka mata.

    Shawarwarin sun haɗa da:

    • Kawo ƙarshen rikice-rikice

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ya kamata Afirka ta ɗauki mataki na ƙashin kanta wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen da ake a wasu ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya, kamar yadda ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaba Tinubun Abdulaziz Abdulaziz ya shaida wa BBC.

    Haka kuma ya nemi haɗin kan kasashen Afirka wajen magance matsalolin tsaro da ke damun wasu ƙasashen Afrika .

    Bola Ahmed Tinubu, ya ce Najeriya ta goyi bayan amincewa da shirin aiki na Luanda, inda ya bayyana shi a matsayin wata hanya mai amfani ta ƙarfafa matakan hana barkewar rikice-rikice.

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce hana rikice-rikice tun kafin su auku ya fi sauki kuma ya fi ɗorewa fiye da ƙoƙarin magance su bayan sun ɓarke.

    • Rage dogaro kan wasu ƙasashe

    Abdulaziz Abdulaziz, ya ce shugaban na Najeriya ya buƙaci a rage yawan dogaron da ake yi kan wasu ƙasashe domin kawo wa Afirka ɗauki.

    ''Ya ce yawan dogaron da ake musammam a ɓangaren tsaro, na iya raunana hanyoyin ƙungiyar AU wajen hana rikice-rikice da kuma manufar cewa 'yan Afirka ne ya kamata su jagoranci warware matsalolinsu."

    Tinubu ya kuma yi kira ga ƙasashen da ke ƙera da fitar da makamai su ƙara haɗa kai da sauran ‚ƴan'uwansu na Afirka wajen samar ko kuma ƙera makamai domin amfanin kasashensu.

    Shugaba Tinubu ya buƙaci shugabannin Afirka su sake jajircewa wajen samar da mafita ta cikin gida, da ƙarfafa haɗin gwiwa, da kuma raba alhakin tunkarar ƙalubalen tsaron da ke addabar nahiyar.

  14. Fiye da mutum 2000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a Yobe

    Fiye da mutum 2,000 ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP daga jam’iyyun APC, ADC da NDC a ƙaramar hukumar Nangere da ke jihar Yobe, gabanin babban zaɓen shekarar 2027 kamar yadda Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

    An karɓi sabbin mambobin ne a wani taro da aka gudanar a Sabon Garin Nangere, inda mamban kwamitin amintattu na PDP kuma tsohon ɗan takarar Sanatan Yobe ta Kudu, Halilu Mazagane, ya bayyana cewa mutum 500 sun fito daga APC, 1,300 daga ADC, yayin da 225 suka fito daga NDC.

    Mazagane ya yi kira ga sabbin mambobin da sauran magoya bayan jam’iyyar da su kasance masu haƙuri tare da mara wa PDP baya a zaɓe mai zuwa, yana mai cewa jam’iyyar za ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da ƙarfafa mata idan aka zaɓe ta.

    Ya kuma buƙace su da su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana tare da zaɓen shugabannin da suke ganin za su kawo ci gaba ga yankunansu.

  15. Adadin waɗanda suka mutu a ambaliyar Nepal ya haura 900, 4,247 sun ɓace

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Nepal ya haura 900 sun mutu, yayin da waɗanda suka ɓace ya kai 4,247.

    Hukumomi sun ce aƙalla mutum 903 ne aka tabbatar sun mutu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman dubban mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.

    Hukumomin kula da bala'o'i na Nepal sun ce adadin waɗanda suka ɓace ya karu sosai daga 2,502 da aka sanar a ranar Lahadi.

    Daga cikin mutanen da ake nema akwai 'yan ƙasar Nepal 3,655 da kuma baƙi 592.

    Ambaliyar ta yi ɓarna mai yawa a yankunan da ke kusa da iyakar Nepal da China, inda ta lalata gidaje, hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.

  16. Wani jirgin dakon mai ya kama da wuta bayan taka nakiyoyin ruwa a Hormuz - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce wani babban jirgin dakon mai ya kama da wuta tare da tsaya wa cak bayan ya taka nakiyoyin ruwa biyu a kudancin mashigar Hormuz.

    A cewar rundunar, jirgin na ƙoƙarin bi ta wata hanya da ta bayyana a matsayin haramtacciya.

    A wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa, IRGC ta ce duk wani jirgin ruwa da ya karya dokokin tsaro da ta kafa a mashigar Hormuz zai iya fuskantar irin wannan sakamako.

    Har yanzu ba a bayyana sunan jirgin dakon man ba ko ƙasar da yake ɗauke da rajista.

    IRGC ta kuma jaddada cewa dukkan jiragen ruwa masu bi ta mashigar Hormuz wajibi ne su bi ƙa’idojin zirga-zirga da rundunar ruwanta ta gindaya.

    Ta kuma gargaɗi masu jiragen da kada su bari Amurka ta rinjaye su wajen amfani da wasu hanyoyi dabam, tana mai cewa hakan na iya jefa jiragen da ma’aikatansu cikin haɗari.

  17. Shugaban Iran ya isa Kyrgyzstan yayin da ake shirin ganawarsa da Putin

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya isa birnin Bishkek na Kyrgyzstan domin halartar taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Shanghai, yayin da ake sa ran zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a gefen taron.

    Pezeshkian ya isa Kyrgyzstan tare da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, inda mataimakin firaministan ƙasar ya tarbe su a babban birnin Bishkek.

    Ana sa ran shugabannin ƙasashe 21 za su halarci taron, ciki har da na China, Rasha, Kazakhstan, Indiya da Iran.

    Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ce ganawar da ake sa ran za ta gudana tsakanin Pezeshkian da Putin ita ce ta shida tsakanin shugabannin biyu.

  18. Iran ta ce ta kai hari kan sojojin Amurka a Jordan

    Iran ta ce ta harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka biyu da ke Jordan, bayan Amurka ta kai hari kan wasu wuraren harba makamai na Iran a tsibirin Larak.

    Iran ta ce harin na Amurka ya kashe tare da jikkata sojoji da fararen hula, kuma ta yi alƙawarin ramuwar gayya.

    Jordan ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami takwas da suka shiga sararin samaniyarta da sanyin safiyar Litinin.

    A halin da ake ciki, farashin ɗanyen mai ya ƙaru da sama da kashi 2%, inda farashin Brent ya haura dala 90 kan kowace ganga.

  19. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.