Zanga-zangar matasa da ta tilasta wa ministan ilimi murabus a Indiya

Asalin hoton, Getty
- Marubuci, Abhik Deb
- Aiko rahoto daga, Delhi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A shekaru 12 da Narendra Modi ya shafe yana mulkin Indiya, minista ɗaya kacal ne a gwamnatinsa ya taɓa yin murabus, kuma hakan ya biyo bayan zargin cin zarafin mata da aka masa.
Abin da ya sa murabus ɗin ministan ilimi Dharmendra Pradhan a ranar Asabar, bayan shafe fiye da mako guda ana zanga-zanga mai zafi a titunan ƙasar, ya zama wani muhimmin al'amari a siyasar India. Matasa da dama sun ɗauki lamarin a matsayin wata nasara da ba kasafai ake samu ba.
Sakhi, wata matashiya mai shekara 22 da ke cikin jagororin masu zanga-zangar a birnin Delhi ta ce: "A karon farko na ji cewa za mu iya kawo sauyi ta hanyar zanga-zanga."
Jim kaɗan bayan Pradhan ya yi murabus, masu amfani da kafafen sada zumunta suka fara yaɗa wani tsohon bidiyo na wani babban minista a gwamnatin Modi yana cewa: "ba a yin murabus a gwamnatinmu."
Ga masu zanga-zangar, wannan ya ƙara musu kwarin gwiwa, domin suna ganin ya nuna irin nasarar da gangamin matasan da ya bazu a faɗin ƙasar ya samu.
A shafinta na Instagram, Sakhi ta riƙa wallafa hotuna da bidiyoyin yadda ƴan sanda suka ci zarafin masu zanga-zanga tare da kama wasu daga cikinsu. Haka kuma ta wallafa wasu gajerun bidiyoyi da ke tsokanar jami'an tsaro da ke tsaye a wuraren zanga-zangar.
Miliyoyin mutane ne suka kalli wasu daga cikin waɗannan bidiyoyi.
A cewarta, gwamnati ta kasa fahimtar irin ƙarfin da wannan gangami ya samu saboda ba ta fahimci yaren da matasa ke amfani da shi da kuma dandalin da suke amfani da shi wajen yaɗa saƙonninsu ba.
"Gwamnati tana da tasiri a kafafen sada zumunta irinsu Facebook da WhatsApp. Amma ta mance da tasirin Instagram."

Asalin hoton, Sakhi
Yadda zanga-zangar ta fara a Indiya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sabuwar zanga-zangar da ta maida hankali kan batun ilimi a Indiaa ta ɓarke ne a watan Mayu, bayan soke jarabawar shiga makarantun likitanci ta NEET, wadda ita ce babbar jarabawar shiga fannin likitanci a ƙasar, sakamakon fallasa zargin fitar da takardar jarabawa.
Sakamakon haka, an tilasta wa kusan ɗalibai miliyan biyu sake rubuta jarabawar.
Fiye da ɗalibai 20 ne suka mutu ta hanyar kashe kansu, inda iyalansu suka danganta mutuwar da abin kunyar da ya biyo bayan badaƙalar jarabawar.
Daga nan ne ƙungiyar yaƙin neman sauyi ta yanar gizo mai suna Cockroach Janta Party (CJP) ta fara magana kan lamarin, inda ta shirya wani babban gangami. An kafa CJP ne bayan da babban alkalin India ya kwatanta matasan da ba su da aikin yi saboda suna da "takardun karatu" da kyankyasai.
Jagororin ƙungiyar sun gudanar da zaman dirshan a birnin Delhi, suna neman ministan ilimi Dharmendra Pradhan ya yi murabus, tare da buƙatar a yi gyare-gyare a tsarin ilimi da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Da farko, zanga-zangar ba ta samu kulawa sosai ba.
Sai dai lamarin ya sauya a ranar 18 ga Yuli, lokacin da ƴan sandan Delhi suka yi amfani da ƙarfi wajen kan wani malami Sonam Wangchuk da ke yajin cin abinci, wanda daga baya aka garzaya da shi asibiti.
Bayan kwana biyu, dubban mutane suka yi tattaki zuwa majalisar dokokin ƙasar.
Bidiyoyin da suka yaɗu a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ƴan sanda suka yi amfani da sanduna, hayaƙi mai sa hawaye da kuma harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Maimakon su dakile gangamin, waɗannan hotuna da bidiyoyi sun ƙara fusata jama'a tare da jawo ƙarin mutane shiga zanga-zangar.
Ɓacin ran matasan Indiya ne ya bazu zuwa sauran sassan ƙasar

Asalin hoton, Somaya Korde
Ɓacin ran da matasan India ke ciki da kuma ƙarfin halin bayyana matsalolinsu a kan titunan ƙasar ne ya bazu zuwa wasu sassan ƙasar.
Somaya Korde tana daga cikin waɗanda aka tsare a gidanta bayan ta yi kira a kafafen sada zumunta ga mutane su shiga zanga-zangar da aka shirya a birnin Mumbai a ranar 20 ga watan Yuli. Sai dai daga baya ta amu halartar wasu zanga-zanga da dama a wasu kwanakin.
Ta ce murabus ɗin ministan ilimi Dharmendra Pradhan "ba hi ne ƙarshen gwagwarmayar ba, yanzu ma aka fara".
"A wannan zamani namu, wannan shi ne karo na farko da da yawa daga cikinmu muka fito zanga-zanga. Amma akwai manyan matsaloli da ya kamata mu tattauna a kansu, kuma za mu ci gaba da magana a kansu," in ji Korde.
Korde, mai shekara 26, ita ce mace ta farko a gidansu da ta kammala karatun shari'a, kuma ta taɓa tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomi.
Ta fito ne daga al'ummar da gwamnatin India ta ware a matsayin masu "rauni" saboda matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da suka daɗe suna fuskanta.
Kamar sauran matasa da dama a India, Korde ta ɗauki ilimi a matsayin hanyar samun ingantacciyar rayuwa, amma ta ce badaƙalar fitar da takardar jarabawar NEET ta karya mata ƙwarin gwiwa kan cewa duk wanda ya yi aiki tuƙuru zai ga sakamako.
"Ana mayar da makarantu da jami'o'i hannun ƴan kasuwa, amsar takardun jarabawa na fita, kuma ko da ka kammala karatu, babu isassun ayyukan yi. A tsarin dimokuraɗiyya, duk wannan na ɗiga ayar tambaya kan adalcin gwamnati," in ji ta.

Asalin hoton, Harshvardhan Kadam
Fushin Korde na nuna babbar matsalar da matasan ƙasar ke fuskanta.
India ce ƙasar da ke da mafi yawan matasa a duniya, amma alƙaluman gwamnati sun nuna cewa rashin aikin yi tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa 29 ya ƙaru daga kashi 13.8 a shekarar da ta gabata zuwa 16.2 a watan Yunin wannan shekara.
Hatta waɗanda suka kammala jami'a na fuskantar matsala wajen samun aiki. Wani bincike da Jami'ar Azim Premji ta gudanar a shekarar 2026 ya gano cewa ƙasa da kashi bakwai na masu neman aiki ne suka samu aikin dindindin mai albashi cikin shekara guda, yayin da ƙasa da kashi huɗu suka samu manan ayyukan ofis masu gwaɓi.
Zanga-zangar ta zama wata kafa da bai wa matasa damar cire tsoro tare da bayyana damuwarsu a fili.
Daga cikin su akwai matasa irinsu Harshvardhan Kadam, ɗan shekara 18, wanda ya fara aikin wucin gadi na sayar da kwamfutoci bayan kammala makaranta domin taimaka wa mahaifiyarsa bayan rasuwar mahaifinsa a bara.
A ranar 23 ga Yuli, wani bidiyon da Harshvardhan ya ɗauka yayin tattakin zanga-zanga a Mumbai ya yaɗu sosai a soshiyal midiya.
Wani bidiyo da ya wallafa a Instagram, ya samu makallata miliyan 10, inda aka ga wani ɗan sanda yana yi masa barazanar ƙulla masa laifin safarar miyagun ƙwayoyi yayin da yake tsare da shi a cikin motar 'yan sanda.
Daga baya an dakatar da ɗan sandan.
"Ban so a dakatar da shi ba. Abin da nake so shi ne kawai in nuna yadda ƴan sanda suka yi mu'amala da ni9 saboda na shiga zanga-zangar lumana," Kadam ya shaida wa BBC.
Yayin da yake magana kan murabus ɗin ministan ilimi, ya ce: "Wannan somin taɓi ne kawai. Wannan ya nuna cewa a gaba gwamnati za ta ji tsoronmu idan muka ɗaga murya."
Zargin takaita ƴancin gwagwarmaya a mulkin Modi

Asalin hoton, Varuni Poorva
Swaraj Priyo, marubucin fina-finai mai shekara 29 daga birnin Guwahati, ya ce yawan zanga-zangar da aka yi a lokacin mulkin gwamnatin Narendra Modi sun sa ya rasa ƙwarin gwiwa saboda rashin ganin sauyi mai ma'ana. Sai dai ya ce wannan sabon gangamin ya dawo masa da fatansa.
Sai dai duk da wannan ƙarfin gwiwar da masu zanga-zangar ke nunawa, akwai kuma fargaba a tsakanin wasu daga cikinsu.
Varuni Poorva, mai shekara 30 daga Patna wadda ke fatan zama malamar jami'a kuma ta kwashe kusan shekaru goma tana harkokin gwagwarmayar ɗalibai, ta ce murabus ɗin Pradhan ya nuna cewa za a iya tilasta wa gwamnatin Modi yin biyayya.
Sai dai ta ce tana fargabar yiwuwar gwamnati ta fara ɗaukar wani mataki na musguna wa masu zanga-zangar, duk da alƙawarin da ta yi cewa ba za ta ɗauki mataki a kan waɗanda suka shirya ko suka shiga gangamin ba.
Ƴan sanda sun tuhumi sama da mutum 100 daga cikin masu zanga-zangar da laifuka da suka haɗa da yunƙurin kisan kai, yayin da aka kama fiye da mutum 40.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta ce a lokacin mulkin Narendra Modi, hukumomin India suna "yawan gurfanar da masu fafutuka, ƴan jarida da masu zanga-zangar lumana bisa wasu dokokin yaƙi da ta'addanci da kuma kalaman ƙiyayya da ake zargin an ƙirƙira musu."
Duk da fargabar yiwuwar gwamnati ta fara murkushe masu zanga-zangar, wadda iyayen ɗalibai da dama ke nunawa, Varuni Poorva ta ce wannan gangamin ya bai wa matasa sabon ƙarfin gwiwa.
Ta ce muddin ba a magance manyan matsalolin da suka jawo fushin matasan ba, zai yi wuya gwamnati ta koma ci gaba da harkokinta kamar yadda ta saba.
A wani wurin zanga-zanga a birnin Delhi, rubutun da aka yi a bango ya bayyana yanayin da masu gangamin ke ciki: "Ba mu da ayyukan yi. Idan kuka goge wannan, za mu dawo gobe."











