Dalilan da suka sa Portugal ta dakatar da Ronaldo

Portugal za ta gudanar da bincike kan abin da ya faru tsakanin Ronaldo da kocin kasar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar Kwallon Kafa ta Portugal (FPF) ta dakatar da Cristiano Ronaldo na wucin gadi bayan ya bar sansanin tawagar ƙasarsa a watan da ya gabata.

Kyaftin ɗin mai shekaru 41 ya fice daga tawagar Portugal a gasar Nations League bayan da ya zauna a benci ba tare da an saka shi wasa ba a karawar da suka yi da Norway, sannan ya gano cewa ba za a fara wasan Denmark da shi ba.

A cikin wata doguwar sanarwa, tauraron Al-Nassr ya bayyana cewa ya bar tawagar ne saboda koci Jorge Jesus ya "saɓa alkawarinsa" sau biyu, yana mai zarginsa da "cin amana gaba ɗaya".

A wata sanarwa, FPF ta ce an sanya masa "dakatarwa ta wucin gadi" a ranar 9 ga Oktoba, kuma an baiwa lamarin fifiko domin a kammala bincike cikin gaggawa.

Dokokin FPF sun tanadi cewa duk ɗan wasan da ya ƙi halarta ko ya bar aikinsa na ƙasa ba tare da izini ba zai iya fuskantar dakatarwa daga wata ɗaya zuwa shida, tare da tara.

Shugaban FPF, Pedro Proenca, ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Portugal cewa:"Wannan lokaci ne na natsuwa da kwanciyar hankali. Dukkanmu muna zaune tare domin tattaunawa.

"Akwai ƙwarin gwiwar ganin kyaftin ɗinmu ya dawo. Za a bi tsarin ladabtarwa na yau da kullum."

Ronaldo ya amince da ɗukar alhakin abin da ya faru kuma ya nemi afuwa ga abokan wasansa da magoya baya, kafin ya ƙara da cewa ya cancanci hukunci.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar ya kuma tabbatar da cewa ba zai yi ritaya daga buga wa Portugal wasa ba, yayin da yake ci gaba da neman kai wa kwallaye 1,000 a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

Ronaldo ya zura ƙwallaye 146 a wasanni 234 da ya buga wa Portugal, duka biyun suna matsayin tarihi a ƙwallon ƙafar maza, kuma ya taimaka wa ƙasarsa lashe Euro 2016 da kuma Nations League sau biyu.

Ya yi tunanin yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa bayan gasar cin kofin duniya da ta gabata, amma daga baya ya yanke shawarar ci gaba.

A makon da ya gabata, Ronaldo ya koma filin wasa inda ya zura kwallarsa ta 980 a rayuwarsa, a nasarar da Al-Nassr ta samu da ci 3-0 a kan Diriyah Club

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Batun Ronaldo ya daɗe yana jawo muhawara, inda magoya baya da dama suka soki tsohon kocin Portugal, Roberto Martinez, kan dagewarsa wajen fara wasa da Ronaldo a gasar cin kofin duniya ta bana.

Lamarin ya kai kololuwa a ranar 4 ga Oktoba lokacin da Ronaldo ya kasance a benci ba tare da ya taka leda ba a wasan da Portugal ta doke Norway. Daga baya ya bar sansanin tawagar bayan ya gano cewa shi ma ba zai fara wasan Denmark da za su yi a gaba ba.

Daga nan Ronaldo ya wallafa sanarwa mai kusan kalmomi 2,000 a shafinsa na Instagram inda ya yi kakkausar suka ga koci Jorge Jesus.

Ya nemi afuwa ga magoya baya da abokan wasansa, tare da musanta cewa ya buga wasansa na ƙarshe da Portugal.

Ya ce: "Za a samu wasa guda ko fiye na ban kwana, lokacin hakan zai zo."

Koci Jorge Jesus ya bayyana cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ga Ronaldo idan ya yanke shawarar dawowa, amma bai yi tsokaci kan sabon bayaninsa ba.

Ɗan jaridar ƙwallon ƙafan Portugal, Delgado, ya shaida wa BBC Radio 5 Live cewa:

"Ba na ganin akwai hanyar komawa baya. A cikin bayaninsa, Ronaldo ya ce zai dawo tawagar ƙasa, amma a lokaci guda ya kira Jesus maƙaryaci sau uku.

"A ƙuri'un ra'ayi da aka gudanar a Portugal, kashi 15% ne kawai suka goyi bayan Ronaldo. Mutane suna ganin muna binsa bashin godiya mai yawa, amma lokacinsa ya riga ya wuce kuma ya kamata ya fahimci hakan.

"Matsalar ita ce Ronaldo bai fahimta ba. Yana son ci gaba da wasa kamar yana da shekara 24, ba 41 ba.

"Abubuwa ba za su sake zama iri ɗaya ba. Ko da ya sake bugawa Portugal wasa ko aka shirya masa wasan bankwana, abubuwa ba za su koma yadda suke a da ba.

"Abin da Ronaldo ya yi wa ƙwallon ƙafar Portugal na musamman ne kuma abin mamaki ne, kuma dole ne mu gode masa saboda hidimar da ya yi wa ƙasar. Amma yana da shekara 41 yanzu, kuma ba shi da matsayi a cikin mafi kyawun 'yan wasa 11 na Portugal."