Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 9 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku
  • Sanata BARAU da Hon Abba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. An rufe makarantu biyu a jihar Binuwai saboda tilastawa iyaye sayen littafan karatu

    Ɗaliban makaranta

    Hukumar Tabbatar da Ingancin Ilimi da Shirya Jarabawa ta Jihar Binuwai a Najeriya, ta rufe makarantu biyu, wato Orenda Schools da Opal Schools, bisa zargin cin zarafin ɗalibai da kuma karya manufofin gwamnati kan amfani da litattafan karatu.

    Matakin ya biyo bayan wani rahoto da ke cewa mamallakin makarantun ya kai hari ga jami’an hukumar yayin da suke gudanar da aikinsu.

    Sakataren zartarwa na Hukumar, Dr. Terna Francis, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, yayin da yake bayanin dalilan da ya sa aka rufe makarantun.

    Ya zargi mamallakiyar makarantun, Onyinye Okoye, tare da wasu ma’aikatan makarantar da cin mutuncin tawagarsa ta baki da kuma lalata wata motar hukuma bayan an miƙa musu umarnin kotu da ya ba da damar rufe harabar makarantun.

    Dakta Francis ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafen iyaye kan makarantun suna tilasta musu sayen sabbin litattafan karatu kai tsaye daga makarantar.

    Ya bayyana cewa wannan ya saɓa wa manufar gwamnatin Jihar Binuwai, wadda ta amince ɗalibai su ci gaba da amfani da tsofaffin litattafansu da kuma ba iyaye damar sayen littattafai daga shagunan sayar da littattafai na waje idan sun ga dama.

    Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da take jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa dukkan makarantu a jihar suna bin dokoki da manufofin ilimi da gwamnati ta gindaya.

  2. Atiku ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027

    Atki

    Jam'iyyar ADC mai hamayya a Najeriya ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasar.

    Yayin ƙaddamar da kwamitin a birnin Abuja, ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar ya ce waɗanda aka naɗa ba wai kawai ‘yan siyasa ba ne, illa masu kishin ƙasa kuma gogaggun mutane a tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya.

    Senator Augustine Okwudiri Akobundu ne zai jagoranci kwamitin da taimakon sauran jiga-jigan jam'iyyar ciki har da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, wanda yanzu haka ke tsare a hannun hukukomin ƙasar bisa zargin laifuka

    A cewarsa, kwamitin na ɗauke da babban nauyi na taimaka wa jamiyyar ADC a ƙoƙarinta na tabbatar wa ƴan Najeriya cewa tana da mafita ga matsalolin ƴan kasar.

    ADC na daga cikin jam'iyyun da ake ganin za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027 da ke tafe.

  3. An fara neman aƙwatin naɗar bayanan jirgin sojin Najeriya da ya yi hatsari

    Jirgin sojin Najeriya
    Bayanan hoto, Jirgin sojin saman Najeriya ya yi hatsari, inda dukkan wadanda ke ciki suka rasu

    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce ta fara ƙoƙarin gano na’urorin bayanan muryoyin matukan jirgi da abin da ya faru gabannin hatsarin shi a yankin Igbokoda, da ke ƙaramar hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.

    Babban jami’in kula da ƙa’idoji da tantancewa na rundunar sojin, Air Vice Marshal Ebimobo Ebiowe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wurin da hatsarin ya faru a ranar Juma’a.

    Jirgin, wanda ke gudanar da aiki na yau da kullum daga Birnin Benin na Jihar Edo zuwa Legas, ya fado cikin wata fadama kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda a ranar Litinin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar duka mutane 25 da ke cikinsa.

    Jami’ai sun bayyana cewa jirgin ya faɗo tare da rabewa gida biyu, inda babban sashensa ya nutse gaba ɗaya cikin fadamar.

    Sun ƙara da cewa jirgin ya nutse zuwa zurfin kusan mita 30 a cikin ruwan fadamar, abin da ke sa aikin ceto da gano muhimman na’urorin jirgin ya kasance mai matukar wuya.

  4. Ghana ta dakatar da dokar hana wa'azi a motocin haya

    Ghana
    Bayanan hoto, Shugaba Jihn Dramani Mahama

    Gwamnatin Ghana ta dakatar da aiwatar da dokar hana wa’azi a cikin motocin haya a faɗin ƙasar. Sabuwar dokar zirga-zirga ta haramta yin wa’azi da kuma talla a cikin motocin haya ko na jama’a yayin da suke tafiya, inda masu karya dokar za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin watanni takwas a kurkuku ko tara da ta haura dala 52.

    Wani rahoton BBC da aka yi kwanan nan game da dokar ya tayar da muhawara a Ghana, musamman kan yadda dokar za ta shafi ƴancin addinai.

    Mai magana da yawun gwamnatin Ghana, Felix Kwakye Ofosu, ya shaida wa BBC a ranar Juma’a cewa akwai buƙatar sake nazari kan dokar bayan damuwar da shugabannin addinai suka nuna.

    Ya ce an samu ƙorafe-ƙorafe daga wasu shugabannin addinai da masu ibada, saboda haka an dakatar da aiwatar da dokar na ɗan lokaci domin a ci gaba da tattaunawa da tuntuɓa, tare da neman amincewarsu kafin a fara aiwatar da ita.

    Ghana ƙasa ce da yawancin al’ummarta Kiristoci ne, kuma yin wa’azi a cikin motocin haya, musamman bas-bas, abu ne da aka saba gani. Sai dai sabuwar dokar ta bayyana wannan aiki a matsayin abin da ke kawo cikas ko damuwa ga jama’a, ba tare da la’akari da addinin mutum ba.

    Ra’ayoyin al.umar ƙasar sun kasu kashi biyu, aƙwai masu adawa da wa’azin a cikin motocin haya suna ganin cewa hakan na damun fasinjoji kuma yana iya jefa lafiyarsu cikin haɗari.

    Amma masu goyon bayan wa’azin suna cewa aikin bishara wani muhimmin nauyi ne na addinin Kirista, kuma kundin tsarin mulkin Ghana ya ba mutane ƴancin bayyana addininsu.

  5. Jirage sun dakatar da jigila zuwa Saudiyya bayan harin Houthi

    Jirgin sama

    Kamfanonin jiragen sama na Jamus, Lufthansa, da na Indiya, Air India, sun sanar da dakatar da jigilarsu zuwa Riyadh, babban birnin Saudiyya, bayan hare-haren da ƙungiyar Houthi ta Yemen ta kai kan filin jirgin saman Riyadh.

    Dakatar da jiragen na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren Houthi ke ƙaruwa kan filayen jiragen sama da kuma cibiyoyin samar da man fetur na Saudiyya.

    A ranar Alhamis, mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun tsananta hare-harensu kan Saudiyya, inda suka harba makamai masu linzami zuwa sararin samaniyar ƙasar da kuma wasu cibiyoyin samar da mai.

    Hare-haren da mayaƙan suka kai yau kan filin jirgin saman Riyadh sun yi sanadin mutuwar mutum uku tare da lalata wani jirgin sama matuƙa.

    Ƙungiyar ta kuma gargaɗin ma'aikata su nisanci wuraren samar da makamashi da take shirin kai wa hari.

    Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin fasinja na kamfanin jiragen sama na Saudiyya ya lalace sakamakon hare-haren da aka kai a Filin Jiragen samana na Sarki Khalid da ke Riyadh.

  6. Gwaji ya nuna mutumin da ake zargin na ɗauke da Ebola ba shi da ita

    Kenya
    Bayanan hoto, Jami'an lafiya sanye da rigar kariya daga cutar Ebola

    Ƙwamishinan yankin Wajir Ahmed Abdullahi, ya bayyana cewa sakamakon gwajin da aka yi wa wani mutum a garin Wajir a arewa masu gabashin Kenya, ya nuna baya ɗauke da cutar Ebola.

    A jiya Talata ne hukumomin yankin suka sanar da samun mutum na farko ɗauke da cutar Ebola, wani dan ƙasar da ya dawo daga Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Congo da kuma ya rasu a wani asibiti a nirnin Nairobi.

    Wannan ya ɗarsa fargabar a zukatan hukumomi, kan wani maras lafiya da ke ƙwance asibitin Wajir ka iya ɗauke da cutar.

    Maras lafiyar mai shekaru 20, ya koma ƙasar daga Congo inda ya fara yada zango a Uganda kafin isa Kenya kamar dai maras lafiya na farko cutar ta yi ajali.

  7. Hukumar NDLEA ta yi wa mutum 53,843 magani kan shan ƙwaya

    NDLEA
    Bayanan hoto, Jami'an hukumar NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce cikin shekaru biyar ta yi wa masu fama da shan muggan ƙwayoyi 53,843 magani a cibiyoyin hukumar da ke jihohin kasar 31.

    Hukumar ta bayyana hakan ne a gangamin da ta ke yi na wayar da kai da yaƙi da shan muggan kwayoyi.

    Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar. Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya shaidawa mataimakin shugaban Hukumar Ƙwastam Archie-Abia Ibinabo, shirin hukumarsa na ganin bayan sha da fataucin muggan ƙwayoyi a fadin Najeriya.

    Marwa, ya ƙara da ce wa halin da masu tu'ammali da muggan ƙwayoyi ke ciki ya munana lamarin da ya ke kai su ga rasa lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, kuma matasa lamarin ya fi shafa.

    NDLEA dai na yawan kama muggan ƙwayoyi da hodar iblis da tabar wiwi da sauran kayan maye a filayen jiragen sama na ƙasar da tasoshin mota da sauransu.

  8. Amurka za ta ƙwace kusan dala biliya ɗaya na crypto da ake alaƙantawa da Iran

    Kuɗin Kirifto

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Besant, ya shaida wa tashar talabijin ta Newsmax cewa akwai yiwuwar Washington ta ƙwace kadarorin kuɗaɗen cryptocurrency da darajarsu ta kai kusan dala biliyan ɗaya, waɗanda ake alaƙanta su da Iran, kafin ƙarshen wannan makon.

    Ya ƙara da cewa, ba tare da yin ƙarin bayani ba, jami'an gwamnatin Amurka sun san inda waɗannan kadarori suke.

    Tare da haɓakar kasuwar kuɗaɗen intanet a cikin 'yan shekarun nan, an fara amfani da dandamalin musayar irin waɗannan kuɗaɗe wajen hallaka hanyoyin gano sahihan ma'amaloli na kuɗi ko kuma kauce wa takunkumai da ƙuntatawar tattalin arziki.

    A ƴan shekarun da suka gabata, Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta yi gargaɗin cewa cinikin kuɗaɗen intanet na iya rage tasirin takunkuman da Amurka ke ƙaƙaba wa ƙasashe ko ƙungiyoyi.

  9. An kashe matuƙin jirgin saman Saudiyya a harin filin jirgin ƙasar

    Jirgi

    Kamfanin jiragen saman Saudiyya, Saudiya, ya tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin matuƙansa bayan wani hari da ya faru a ranar Alhamis a Filin Jiragen Sama na Sarki Khalid da ke Riyadh.

    Kamfanin ya bayyana sunan matuƙin a matsayin Hamoud Ali Al-Kulthami.

    Tun da farko kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa wani jirgin fasinja na kamfanin Saudi Arabian Airlines da ke ajiye a ɗaya daga cikin tashoshin filin jirgin saman Riyadh ya yi mummunar lalacewa sakamakon gobara.

    A wani ɓangaren kuma, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya ta ce mutum uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a hare-haren da aka kai ranar Alhamis kan Filin Jiragen Sama na Sarki Khalid da ke Riyadh.

    Hukumar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin jiragen saman da ke filin ya lalace sakamakon harin.

  10. Habasha ta yi wa Eritrea kakkausan gargaɗi

    Sojojin Habasha
    Bayanan hoto, Dakarun sojin Habasha sun karɓe ikon babbar birnin yankin Tigray wato Mekelle a makon da ya wuce daga hannun ƴantawaye.

    Ƙasar Habasha ta zargi makofciyarta Eritrea da gaddamar da cikakkiyar mamaya arewacin yankin Tigray, da gargaɗin za ta ɗauki duk matakin da ya dace domin kare kan ta.

    Wannan na zuwa ne ƙwanaki kaɗan bayan mazauna yankin sun shaidawa BBC dakarun Eritrea sun tsallako iyakar ƙasashen biyu.

    A wasiƙar da ministan harkokin wajen Habasha ya aikewa ƙwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya kira matakin Eritrea da tsagwaron keta haddin ƙasarsa kuma su na da dama kare kan su ta kowacce hanya, sakamakon yadda dakarun ƙasar suka kai hare-haren makamai masu linzami a yankin Tigray.

    A martanin da ministan yaɗa labaran Eritrea Yemane Gebremeskel, ya ce Habasha na son tada zaune tsaye da neman dalilin kai wa ƙasarsa hari.

    Tashin hankali ya ɓarke tsakanin gwamnatin Habasha da jam'iyyar TPLF da iko da yankin Tigray, makonni biyu da suka gabata.

    Dukkan ɓangarorin biyu sun zargi juna da take yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin basasar da suka shiga a shekara 2020 zuwa 2022, kuma Habasha ta zargi Eritrea da taimakawa TPLF, zargin da ta musanta.

  11. Yadda gwamnan Kano ya jagorancin sulhun Barau da Abba Bichi

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  12. Ɓarayi sun sace ƙwalaben barasa 30,000 a Italiya

    Barasa
    Bayanan hoto, Barasa

    Wasu ɓarayi sun sace ƙwalaben barasa 30,000 da darajarsu ta kai yuro miliyan 5 daga wani katafaren kantin saida giya a ƙasar Italiya.

    Kanfanin Marchesi Antinori,na ɗaya daga cikin fitattun kantinan saida barasa da wasu iyalai attajirai suka mallaka a ƙasar, bayanai sun ce ɓarayin sun shiga wurin ajiyar barasar a yankin Tuscany daidai lokacin da kamfanin ke ƙoƙarin da haɗa kayan da za su aikawa abokan hulɗarsu da ke ƙasashen waje.

    An yi amanna ɓarayin su 7 da suka rufe fuskokinsu sun kashe kararrawar ankararwa da wurin, da katse kyamarar CCTV sun kuma yi amfani da motar ɗaukar kayan kamfanin wajen loda barasar da suka sace.

    Shugaban kamfanin barasar Renzo Cotarella, ya shaidawa jaridar Corriere della Sera cewa wannan ce sata mafi girma da aka taɓa yi wa wani kantin saida barasa a ƙasar Italiya.

  13. Jihohin Najeriya da jam'iyyun hamayya ke da ƙarfi gabanin 2027

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  14. Zazzabin lassa ya kashe mutum 263 yayin da 1,115 suka kamu a Najeriya — NCDC

    Hukumar Yaƙi da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutum 263 sun mutu, yayin da aka tabbatar da mutum 1,115 sun kamu da zazzabin Lassa tsakanin watan Janairu zuwa 20 ga Satumban 2026.

    A taƙaice, hukumar ta ce yawan mace-macen ya kai kashi 23.6 cikin 100, wanda ya fi na makamancin lokacin a shekarar 2025 da ya kasance kashi 18.5 cikin 100.

    Jihohin Ondo, Bauchi, Taraba, Edo da Benue ne suka fi yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda suka ƙunshi kusan kashi 87 cikin 100 na dukkan cututtukan da aka tabbatar.

    NCDC ta danganta karuwar mace-macen da jinkirin kai marasa lafiya asibiti, tare da kalubale irin su tsadar jinya, rashin tsaftar muhalli da ƙarancin wayar da kai a wasu al'ummomi.

    Hukumar ta buƙaci jama'a da ma'aikatan lafiya su ci gaba da ɗaukar matakan kariya da kuma hanzarta gano masu cutar domin rage yaduwarta.

  15. An kashe ƴan Saudiyya uku a harin filin jirgin Riyadh

    jirgi

    Ƴan Saudiyya sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-hare biyu da aka kai kan filin jiragen saman Sarki Khalid da ke Riyadh a ranar Alhamis, kamar yadda Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta sanar a ranar Juma'a.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ambato hukumar na cewa harin farko ya yi wa wasu sassa na filin jirgin saman illa, yayin da na biyu ya auka wa wani jirgin sama na kamfanin Saudia.

    A cikin wata sanarwa, GACA ta ce tawagogin kai ɗaukin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa sun yi gaggawar mayar da martani ga hare-haren biyu bisa tanade-tanaden da aka shimfiɗa na gaggawa da kuma tsare-tsaren ko-ta-kwana.

    Hukumar ta ce hare-haren sun jikkata wasu ƴan ƙasar da mazauna ƙasar na ƙabilu daban-daban.

    Tuni ƙungiyar ƴantawaywen Houthi ta ɗauki alhakin kai harin

    GACA ta ce tana ci gaba da tantance irin asarar da aka yi tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki, tare da ɗaukar duk matakan da suka dace domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da ma'aikatan filin jirgin sama, da kuma kare tsarin sufurin jiragen sama na farar hula na Saudiyya.

    Hukumar ta ce tuni aka koma zirga-zirga a filin jirgin.

  16. TUC ta umarci mambobinta a Abuja su yi watsi da yajin aikin NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta TUC reshen Babban Birnin Tarayya Abuja ta umarci dukkan mambobinta da su ci gaba da zuwa wuraren aikinsu, tana mai bayyana cewa ba ta goyi bayan yajin aikin sai baba-ta-gani da ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ayyana ba.

    TUC ta ce ba ta halarci taron da aka yanke shawarar fara yajin aikin ba, kuma ba ta amince da matakin ba.

    Saboda haka, ta buƙaci mambobinta da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

    Ƙungiyar ta kuma gargaɗi mambobinta da kada su bari a tilasta musu shiga yajin aikin, tana mai kira da a warware rikicin da ya shafi malamai ta hanyar tattaunawa domin kauce wa katsalandan ga harkokin ilimin yara.

  17. Jami'in shige da fice na Amurka ya harbi wani mutum a New York

    ...

    Wani jami'in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE) ya harbi wani mutum a yankin New York yayin wani samame da aka ce an kai domin cafke wani ɗan baƙin haure da ke zaune a yankin ba bisa ƙa'ida ba

    Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ce mutumin bai mutu ba, kuma an kwantar da shi a wani asibiti domin kula da lafiyarsa

    Rahotanni sun ce lokacin da lamarin ya faru, mutumin yana cikin mota tare da wani yaro ɗan shekara biyar, wanda bai samu rauni ba.

    Magajin Garin New York, Zahran Mamdani, ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yayin da Gwamni Kathy Hochul ta ce ta tattauna da Shugaba Donald Trump kan harbin tare da nuna damuwarta kan abin da ya faru.

    Jami'ai sun ce mutumin ɗan asalin Jamhuriyar Dominika ne kuma yana da tarihin aikata laifi.

  18. Tsohuwar babbar jami’ar MDD Navi Pillay ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel

    ....

    Tsohuwar babbar jami’ar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da kare haƙƙin ɗan Adam, Navanethem “Navi” Pillay, ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2026.

    Kwamitin Nobel na Norway ya ce an ba ta kyautar ne saboda gudunmawar da ta bayar wajen bunƙasa zaman lafiya da kuma ƙarfafa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da jajircewarta wajen tabbatar da hukunta masu laifukan yaƙi, cin zarafin bil adama da kuma kisan kiyashi.

    Navi Pillay, mai shekaru 85 ‘yar asalin Durban ta Afirka ta Kudu, ta shafe shekaru da dama tana aiki a fannonin shari’a da kare haƙƙin ɗan Adam.

    Ta riƙe muƙamai da suka haɗa da alƙaliya a kotunan ƙasa da ƙasa da kuma Babbar Kwamishiniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Haƙƙin Ɗan Adam tsakanin 2008 da 2014.

  19. Pakistan ta aike da manyan dakarunta zuwa Saudiyya domin tsaro

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta sanar cewa ƙasar ta tura ɗimbin sojoji da kayayyakin aikinta na soji zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin tsaro.

    Mai magana da yawun ma'aikatar, Sajjad Haider Khan, ya ce a halin yanzu Pakistan na da yawan sojoji da kayan aiki da aka jibge a Riyadh.

    Sai dai ya jaddada cewa sojojin Pakistan da ke Saudiyyar ba za su tsallaka iyaka domin kai hari kan Mayaƙan Houthi a Yemen ba, illa kawai za su taimaka wajen kare yankin da tsaron ƙasar Saudiyya.

    Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankin Gabas ta Tsakiya

  20. Atiku da NDC sun soki ragin farashin fetur na kwanaki 30 da gwamnati ta sanar

    ...

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, da jam'iyyar NDC sun soki shirin gwamnatin tarayya na rage farashin fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen mai na NNPCL.

    Atiku ya ce matakin ba zai magance matsalolin tsadar rayuwa na dogon lokaci ba, yana mai tambayar abin da zai faru bayan wa'adin rangwamen ya ƙare.

    Ya ce rage farashin na ɗan lokaci ba zai saukar da kuɗin sufuri da farashin kayan abinci yadda ya kamata ba.

    A nata ɓangaren, jam'iyyar NDC ta bayyana shirin a matsayin yaudara da matakin da bai isa ya rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ba.

    Jam'iyyar ta kuma nuna damuwa kan yadda gidajen mai na NNPC kaɗai za su iya biyan buƙatun jama'a, tana mai cewa wannan ba mafita ba ce ga matsalar da 'yan Najeriya ke fuskanta sakamakon tsadar fetur da hauhawar farashin kayayyaki.