Ko har yanzu akwai damar yin haɗaka tsakanin ƴan'adawar Najeriya?

Asalin hoton, Multiple/FB
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da siyasar Najeriya ke fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, har yanzu akwai masu kiraye-kirayen haɗakar jam'iyyun adawa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki.
A cikin watannin baya-bayan nan, an ga wasu fitattun ƴan siyasa da ƙungiyoyin matasa na gudanar da tattaunawa kan samar da wata gamayya da za ta haɗa ƙarfi da ƙarfin da ke faɗin ƙasar.
Masana da masu sharhi kan al'amuran siyasa na bayyana ra'ayin cewa rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan adawa na daga cikin abubuwan da suka bai wa APC damar ci gaba da riƙe madafun iko a matakin tarayya.
Sai dai duk da wannan yunƙuri, akwai alamun tambayoyi kan ko shugabannin jam'iyyun za su iya ajiye bambance-bambancen ra'ayi da muradun siyasa domin cimma manufar bai ɗaya.
Tarihin siyasar Najeriya ya nuna cewa irin waɗannan ƙoƙarin haɗaka sun taɓa samar da manyan sauye-sauye, kamar yadda ya faru kafin zaɓen 2015 da ya bai wa APC damar karɓar mulki daga PDP.
To amma yayin da lokaci ke ƙara matsowa, tambayar da masu sa ido ke yi ita ce ko ƴan adawar za su iya samar da haɗakar da za ta ɗore tare da samun goyon bayan masu zaɓe, ko kuwa saɓanin cikin gida zai sake kassara wannan buri kafin a kai ga zaɓen 2027.
Ɓangarorin da suka yi yunƙurin haɗa ƴan'adawar
Zuwa yanzu akwai aƙalla ɓangarori uku da suka yi yunƙurin haɗa kan ƴanhamayyar amma, haƙarsu ba ta iya cimma ruwa ba.
Wasu ƴan ƙasar da dama dai na da burin ganin ƴan hamayyar sun haɗe wuri guda kafin zaɓen na 2027.
Ɓangarorin sun haɗa da ƴanhamayyar da ƴansiyasa da kuma ƙungiyar matasa.
Ƴan hamayyar

Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun da farko jiga-jigan hamayyar da kansu suka yi yunƙurin haɗewar a jam'iyyar ADC, inda a tun a shekarar 2025, wasu daga cikin suka fara tattauanawa domin komawa jam'iyyar da nufin ƙalubalantar Tinubu a 2027.
Zuwa watannin farko an shekarar 2026 kusan duka ƙusoshin hamayyar ƙasar sun kasance a jam'iyyar ADC, inda har wani adadi na ƴanmajalisar dattawa da na tarayya suka shiga jam'iyyar.
To sai ba a jima da hakan ba, sai wani rikici ya kunno kai a jam'iyyar, inda Nafi'u Bala Gombe, wanda ya ayyana kansa a matsayin ''halastaccen'' shugaban jam'iyyar ya ƙalubalanci fitattun ƴansiyasar da suka shiga jam'iyyar a kotu.
Nafi Bala ya zarge su da shiga jam'iyyar ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ya sa har wata kotu a ƙasar ta bayar da umarni ga INEC ta cire sunayen ɓangaren David Mark a matsayin shugabannin jam'iyyar daga shafinta, kodayake daga baya wata kotun ta bayar da umarnin mayar da su.
Wannan matsala ce ta haifar da ficewar biyu daga cikin manyan jiga-jigan Peter Obi da Kwankwaso, inda suka shiga NDC, kamar yadda suka bayyana.
G-100
Bayan ficewar Obi da Kwankwaso daga ADC zuwa NDC, jam'iyyar ta ba su tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimaki, yayin da a nata ɓangare ADC ta bai wa Atiku da Amaechi takarar shugaban ƙasa da mataimaki.
Hakan ya sa wasu ƴan hamayyar suka fara nuna fargabarsu cewa ba lallai ne ƴan hamayyar su kai gaci ba.
Wannan ya sa wasu fitattun ƴan hamayyar kafa wata ƙungiyar siyasa mai suna G-100 da nufin tattaunawa da dukaƴan hamayyar da nufin haɗa kansu don tunkarar Tunkarar Tinubu a 2027.
Ƙungiyar ta yi zama har sa biyu domin ƙoƙarin haɗa kan ƴan hamayyar, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba.
A wata tattaunawa da BBC a kwanakin baya, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Salihu Lukman ya ce ƙungiyar na aiki tuƙuru domin ganin ta cimma burinta.
''Mun zauna da wakilan duka jam'iyyun kuma mun bayyana musu buƙatunmu, waɗanda kuma suka muradunta.
'Tinubu Must Go'

Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB
Wannan ma wata ƙungiya ce da take faftikar ganin ƴan mahayyar sun dunƙule wuri guda da nufin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Tinubu.
Ƙungiya ce da matasa suka kafa, suka kuma assata, tare da ci gaba da tuntuɓar ɓangarorin hayammar.
Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Barista Abba Hikima ya shaida wa BBC cewa tuni ƙungiyar tasu ta zauna da manyan jam'iyyun hamayyar ƙasar domin gabatar musu da buƙatar haɗewar.
''Mun zauna da duka jagororin jam'iyyun hamayyar, mun kuma gabatar musu da buƙatarmu, inda suka ce za su duba su gani'', in ji shi.
Barista Abba Hikima ya ce duka jagororin hamayyar sun tabbatar musu cewa za su duba shawarar haɗewar, kuma za su tuntuɓe su don jin shawarar da suke yanken.
Me jam'iyyar ADC ta ce?

Asalin hoton, Aminu Waziri Tambuwal
BBC ta yi ƙoƙarin tuntunɓar wasu daga cikin manyan jam'iyyun hamayyar domin jim matsayarsu da matakin da suke shirin ɗauka game da batun haɗewar.
Ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC, Faisal Kabir ya shaida wa BBC cewa ƙofar jam'iyyarsu a buɗe take domin yin haɗakar da duk jam'iyyar da ta shirya yin hakan.
''Mun karɓi buƙatun duka ɓangarorin da ke son haɗewar, kuma ƙofarmu a buɗe take, a shirye muke don yin hakan,'' kamar yadda ya bayyana.
Sai dai ya ce dage cewa duk haɗakar da za a yi sai idan ɗantakarar su ne za a saka a gaba.
Mece ce matsayar NDC?

A nata ɓangare jam'iyyar NDC, wadda Peter Obi da Kwankwaso ke yi wa takara, ta ce a shirye take domin wannan haɗaka.
Injiniya Buba Galadima ɗaya ne daga cikin jiga-jigan jam'iyyar, ya kuma shaida wa BBC cewa ƙofar jam'iyyar NDC a buɗe take domin yin haɗakar kafin zuwan lokacin zaɓen.
''Yanzu haka akwai kwamiti da aka kafa mai mutum shida tsakanin jam'iyyarmu ta NDC da ADC da kuma jam'iyar APM, waɗanda kuma suke aiki tuƙuru domin ganin an shirya yadda za a haɗe ɗin''.
Buba Galadima ya ƙara da cewa a shirye NDC take domin yin haɗakar da nufin kawar da Tinubu na APC.
Me ke janyo jinkirin haɗakar?
Tambayar da ƴan Najeriya da dama ke yi ita ce me ya kawo jan ƙafar a yunƙurin haɗewar?
To amma Dr Yakubu Ja'e shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa na Jami'ar Jihar Kaduna ya ce akwai wasu dalilai da ke kawo jan ƙafar wajen haɗewar.
Ɗaya daga cikin dalilan da ya bayyana shi ne shi ne son kai daga wasu ƴan hamayyar.
''Wasu daga cikinsu na fifita muradun kansu ne, sun fi mayar da hankali kan makomarsu, fiye da makomar ƙasar, suna duba abin da za su samu ne ba wai matsalahar ƙasar ba'', in ji shi.
Dr Yakubu Ja'e ya ce wani dalilin ka iya zama dabara ce ta kada a kawo musu matsala.
''Wataƙila da niyya ƴan hamayyar suka ƙi dunƙulewa tun yanzu, don gudan kada a haifar musu wata matsala'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam'iyyun ka iya yin tunanin cewa idan suka haɗe da wuri, to jam'iyya mai mulki ka iya nazarin dabarar tasu domin kawo musu tsaiko.
Akwai yiwuwar haɗewa?
Dr Ja'e ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba don haka har yanzu akwai dama.
''Komai zai iya faruwa, tun kamar yadda jam'iyyun ke cewa ƙofofinsu a buɗe suke, kuma akwai ƙarin kiraye-kirayen da ake yi musu na su haɗe ɗin'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ƙara da cewa idan har ƴan hamayyar na son ƙwace mulki daga hannun Tinubu da APC, to dole ne su ajiye muradunsu na ƙashin kai.





























