Ukraine ta yi Allah-wadai bayan Amurka ta sassauta wa Rasha takunkumi

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi Allah-wadai da sanarwar Shugaba Donald Trump ta sassauta wasu takunkuman da aka ƙaƙaba wa Rasha, domin ba ta damar samar wa Amurka da kasuwannin duniya man dizel.
Trump ya ce ya cimma yarjejeniyar ce bayan tattaunawa ta wayar tarho da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Zelensky ya ce sassauta takunkuman ba tare da wata kwakkwarar yarjejeniya ta rage zaman dar-dar ba, alama ce ta rauni, kuma hakan zai bai wa Rasha damar ci gaba da yakin da ta ke da kasarsa na tsawon lokaci.
Ƴan jam'iyyar Democrat a kwamitin harkokin wajen Majalisar Dattawan Amurka, sun bayyana matakin a matsayin cin amanar Ukraine da kawayen Amurka na Turai da kuma tsaron kasar Amurka.
Farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi tun bayan da Amurka ta fara yaki da Iran a watan Fabrairu, lamarin da ke kara matsin lamba kan 'yan jam'iyyar Republican ta Trump gabanin zaben rabin wa'adi.


















