Shin Saudiyya na son rage yawan dogaro da Amurka ta fuskar tsaro?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, احمد عمر
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بیبیسی عربی
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Batun raba ƙafa kan ƙawancen tsaro ga Saudiyya na ɗaukar wani sabon salo.
A ranar 5 ga watan Oktoba, Saudiyya da Turkiyya da Pakistan suka sanar da fara aiwatar da alƙawurran tsaro na bai ɗaya cikin gaggawa a ƙarƙashin tsarin abin da suka kira "Ƙawancen Makka".
Ƙasashen sun sanar da ɗaukar matakan samar da dakaru da kayan aikin soja da aka amince da su, da kuma tura su cikin hanzari zuwa Saudiyya.
Hakan na zuwa ne bayan da mayaƙan Houthi na Ansarullah daga Yemen suka ci gaba da kai wa ƙasar hare-hare.
An ɗauki wannan mataki ne a wani taron gaggawa na Kwamitin Siyasa da Tsaro na Ƙawancen Makka domin nazarin "barazanar tsaro da kuma sauye-sauyen da ke fuskantar Saudiyya".
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da yaƙin Yemen ya sake tsananta, kuma Saudiyya ke fuskantar hare-hare daga mayaƙan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.
Tun da farko, rahotannin kafofin watsa labarai sun bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da buƙatun da Saudiyya ta sha yi na neman taimakon soja kai-tsaye domin yaƙi da Houthi.
Bisa waɗannan rahotanni, Washington ba ta amince da shiga kai-tsaye a hare-haren sojin Amurka kan Houthis tare da Saudiyya ba, sai dai ta bai wa Riyadh tallafin bayanan sirri da bayanan leƙen asiri domin taimakawa a hare-haren da ake kai wa ƙungiyar.
Shin waɗannan sauye-sauye za su sa Saudiyya ta rage dogaro da Amurka a fannin tsaro?
Sannan ko "Ƙawancen Makka" zai iya samar wa ƙasar wasu daga cikin tabbacin tsaron da ta saba samu daga Washington a baya?
Amurka na taimaka wa tsaron kan iyaka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Fiye da shekara huɗu na zaman lafiya bayan tsagaita wutar yaƙi da Majalisar Ɗinkin Duniya ta mara wa baya a shekarar 2022, rikicin Yemen ya sake shiga wani sabon mataki na tashin hankali.
Sauyin ya zo ne a watan Yuli, lokacin da dakarun gwamnatin Yemen masu samun goyon bayan Saudiyya suka kai hari kan filin jirgin saman Sana'a da ke ƙarƙashin ikon Houthis, suna cewa manufar harin shi ne hana wani jirgin saman Iran sauka a babban birnin ƙasar.
Sa'o'i kaɗan bayan haka, mayaƙan Houthi suka harba makamai masu linzami zuwa kudancin Saudiyya.
Daga nan ne rikicin ya ɗauki wani sabon salo bayan ƙungiyar ta faɗaɗa ikonta a wasu wurare da ke gaɓar tekun yammacin Yemen.
Wannan ya ƙara wa Houthis damar barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Bab al-Mandab, wadda ke kudancin Tekun Maliya kuma ɗaya ce daga cikin manyan hanyoyin kasuwanci da ke haɗa Tekun Indiya da Bahar Rum ta hanyar Tekun Maliya da Mashigar Suez.
A ranar 5 ga watan Oktoba, dakarun gwamnatin Yemen masu samun goyon bayan Saudiyya, tare da taimakon hare-haren sama na Saudiyya, suka ƙaddamar da wani gagarumin farmakin soja domin ƙwato yankunan da Houthis ke iko da su.
Mitchell Plitnick, mai bincike kan harkokin Gabas ta Tsakiya kuma tsohon mataimakin shugaban gidauniyar Middle East Peace Foundation, na ganin cewa abubuwan da suka faru a makonnin baya-bayan nan sun zama wani sabon gwaji ga dangantakar tsaro tsakanin Saudiyya da Amurka.
"Wannan shi ne wurin da Amurka ta gaza cika abin da Saudiyya ke tsammani daga gare ta," in ji Plitnick.
A cewarsa, tun bayan ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu, Saudiyya ta gina dangantakar tsaro da Amurka bisa wata fahimta da ta haɗa tabbatar da daidaiton kasuwannin mai da kwararar makamashi da kuma kariyar tsaro da Amurka da ƙasashen yamma ke samar mata.
Sai dai a cewar Plitnick, gwamnatin Trump ta nuna tun a wa'adinta na farko cewa wannan fahimta ba ta zama cikakkiyar gwaranti ba, musamman idan kare Saudiyya zai ci karo da wasu muradun Amurka.
Ya yi nuni da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin man fetur na Saudiyya a watan Satumban 2019, ciki har da na kamfanin Aramco, waɗanda suka haddasa tsaikon da ya shafi wani babban ɓangare na yawan man da ƙasar ke haƙowa.
Amurka da Saudiyya sun ɗora alhakin hare-haren kan Iran, amma Tehran ta musanta zargin.
Duk da haka, gwamnatin Trump ba ta mayar da martanin soji kai tsaye kan Iran ba.
A cewar Plitnick, wannan lamarin ya nuna cewa goyon bayan tsaro da Amurka ke bai wa Saudiyya yana da iyaka, kuma yana iya kasancewa ƙarƙashin wasu ƙididdiga na siyasa da dabarun ƙasa da ƙasa na Washington.

Asalin hoton, Saudi Press Agency
Ƙawancen Makka: Maye gurbin Amurka ko wani ƙarin zaɓin tsaron?
A cewar El-Yaami, yarjejeniyar da Saudiyya da Turkiyya da Pakistan suka rattaɓa wa hannu a birnin Makka a watan Agusta na daga cikin manyan misalan yadda ƙasashen ke faɗaɗa haɗin gwiwarsu ta fuskar tsaro da siyasa.
Bisa ga yarjejeniyar, duk wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku, a ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar tsaro na bai ɗaya, za a ɗauke shi a matsayin hari kan sauran ƙasashen biyu.
Sai dai tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, an fara tambayar yadda za a aiwatar da ita a aikace, musamman bayan da mayaƙan Houthi suka kai hare-hare kan Saudiyya ba tare da Turkiyya ko Pakistan sun sanar da tsoma bakin soji kai tsaye ba.
Pakistan ta bayyana a watan Satumba cewa ba a tattauna ɗaukar matakin soja cikin gaggawa a ƙarƙashin yarjejeniyar ba domin mayar da martani ga hare-haren Houthi, duk da cewa ta jaddada aniyarta ta ci gaba da bin yarjejeniyar.
Sai dai taron da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba ya kawo sabon ci gaba, inda ƙasashen uku suka sanar da cewa za su shiga matakin aiwatar da alƙawurran tsaron bai ɗaya "nan take", tare da ɗaukar matakan da suka dace domin samar da rundunonin soja da ƙwarewar sojin da aka amince da su, da kuma tura su cikin gaggawa zuwa Saudiyya idan buƙata ta taso.
Miller na ganin cewa wannan ƙawance ba wani tsari ba ne da za a yi watsi da shi cikin sauƙi, domin ya haɗa Saudiyya, wadda ita ce ƙasa ta biyu mafi yawan samar da mai a duniya, da Pakistan mai makamin nukiliya, da kuma Turkiyya, ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke da ƙarfin soja a ƙungiyar NATO.
Sai dai, a ra'ayinsa, hakan ba yana nufin cewa ƙasashen ukun sun shirya shiga wata buɗaɗɗiyar gaba da Iran domin kare Saudiyya ba, ko kuma cewa wannan ƙawance na da ikon samar da irin ƙarfin soja da bayanan leƙen asiri da kariyar sararin samaniya da Amurka ke samarwa a halin yanzu.
Ina makomar ƙawancen tsaron Saudiyya da Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
A cikin ƴan shekarun nan, Riyadh ta fahimci cewa ƙididdigar Washington kan harkokin tsaro na sauyawa bisa canjin gwamnatoci da manufofinsu, lamarin da ya sa ya zama da wuya a ci gaba da dogaro gaba ɗaya kan tabbacin tsaron da Amurka ke bayarwa.
Miller, wanda ya yi aiki a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a ƙarƙashin gwamnatocin Republican da Democrat guda shida, na ganin cewa waɗannan sauye-sauyen na nufin Saudiyya na mu'amala da ƙasa mai muradu masu ɗorewa, amma ƙididdigarta da abubuwan da take bai wa fifiko suna canzawa.
Plitnick ma yana ganin jami'an Saudiyya sun fahimci wannan gaskiya sosai.
Ya ce Saudiyya ta yi aiki tare da gwamnatocin Barack Obama, daga baya Donald Trump, sannan Joe Biden, kafin sake dawowar Trump a karo na biyu, kuma ta san cewa babu wata gwamnatin Amurka da za ta dawwama.
Saboda haka dole ne ta tsara dangantakarta da Washington bisa wannan fahimta.
A cewar Plitnick, waɗannan gogewa sun sa Saudiyya ta ƙware wajen tafiyar da dangantakarta da Amurka da kuma dacewa da salo da manufofi mabambanta na shugabannin ƙasar.
A cewar Freilich, wannan yana daga cikin dalilan da suka sa Saudiyya ke bin manufar faɗaɗa abokan hulɗarta domin rage haɗari, maimakon neman wata ƙasa guda da za ta maye gurbin Amurka.
Ya ce Saudiyya ba za ta iya yin watsi da Washington ba, amma a lokaci guda ba ta son ta kasance cikin yanayin da duk lokacin da rikici ya tashi dole ta jira hukuncin Amurka kaɗai kafin ta iya kare muradunta na tsaro.





























