BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Me ya haifar da rikicin shugabancin majalisar dattawa mai zuwa tun yanzu?
Matakin ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin sanatoci, inda wasu ke kallonsa a matsayin yunƙurin tabbatar da ci gaba da kwanciyar hankali, yayin da wasu kuma ke ganin kamar an fara raba mukamai tun kafin zaɓe.
KAI TSAYE, Atiku, Obi da Duke na dab da cimma yarjejeniyar tsayar da ɗan takara guda – G100
Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 21/10/2026
Yadda aka rataye mutanen da suka aikata assha' a masallaci a Makka
A ranar 14 ga Oktoba ne kafafen yaɗa labaran gwamnatin Saudiyya suka ruwaito cewa an aiwatar da hukuncin kisa kan wasu 'yan Bangladesh biyu, mace da namiji, bayan an zarge su da aikata "ayyuka na rashin ɗa'a" a cikin wani masallaci.
Dars Hausa: BBC za ta ƙaddamar da shirin ilmantar da yaran da ba sa zuwa makaranta
BBC World Service ta faɗaɗa shirin ilmantarwa na "Dars" da ya samu lambar yabo zuwa harshen Hausa domin yara a Yammacin Afrika.
Hukumar binciken kuɗi na duba bayanan lissafin kuɗin Man City
Hukumar kula da binciken kuɗi ta Birtaniya ta tabbatar tana jagorantar bincike kan wasu matsalolin da suka shafi bayanan lissafin kuɗin Manchester City.
Me cutar Ebola ke yi wa jikin wanda ta kama?
Ebola na daga cikin cututtuka masu haɗari da ke haddasa zazzaɓi mai tsanani kuma tana iya kai wa ga lalacewar wasu muhimman gaɓoɓin jiki.
Gwamnoni 7 da za su iya fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa a Najeriya, hankalin 'yan siyasa da masu zaɓe na karkata zuwa kan wasu gwamnoni da ake ganin za su sha baƙar wuya ko ma su rasa mulki a zaɓen 2027 da ke tafe.
Me ya hana Iran wallafa wasiyyar Ayatollah Ali Khamenei?
Jinkirin bayyana wasiyyar Ayatollah Ali Khamenei ya zo ne tare da irin wannan jinkirin wajen fitar da sautin murya ko bidiyon wanda ya gaje shi.
Matsayar ƴan takarar shugabancin Najeriya kan tallafin man fetur
Muhawarar ko za a dawo da tallafin mai ko a'a ta mamaye tattaunawar siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya.
Shiga manhajar BBC Hausa
Mahnajar BBC World News za ta ba ku damar samun labaran duniya da na cikin gida da ɗumi-ɗumi.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 22 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 21 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 21 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 21 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Champions League: Ana 1-1 tsakanin Bayern Munich da Arsenal
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 19 zuwa 25 ga watan Oktoban 2026.
Me zai faru tsakanin Bayern da Arsenal, Real da Leipzig?
Wasa 9 za a buga a gasar Champions League ranar Laraba daga ciki a kwai manyan fafatawa tsakanin Bayern Munich da Arsenal da na Real Madrid da RB Leipzig.
Real Madrid na son Calafiori, Man United ta dage kan Hall
Real Madrid na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar Riccardo Calafiori, Manchester United na zawarcin Lewis Hall, yayin da Liverpool da Arsenal duk suke neman Xavi Espart.
Ronaldo ya ci amanar Manchester United - Ten Hag
Erik ten Hag ya zargi Cristiano Ronaldo da ci wa Manchester United da shi kansa amana. Ga jerin nasarorinsa a Old Trafford, ƙalubalen da ya fuskanta, da kuma dalilan da suka sa aka kore shi daga aikin horar da ƙungiyar
Champions League: Ko Barca za ta iya doke PSG?
Za a buga wasa tara a zagaye na uku-uku a cikin rukuni a Champions League da za a kara har da wasan hamayya tsakanin Paris St Germain da Barcelona ranar Talata.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Shawarwari uku ga masu tafiya a jirgi don kauce wa ɗaukar kayan laifi
A lokuta da dama dai aka samu matsalar saka wa matafiya kayan laifi cikin jakankunansu ba tare da saninsa.
Ƙasurguman Kachalloli biyu da suka mutu a faɗan ƴanbindiga a Zamfara
Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na cewa wani mummunan faɗa da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ƴanbinga ya yi sanadin kashe wasu daga cikin manyan jagororinsu.
Ana jimamin faston da ya mutu a coci bayan kuros ya faɗo masa a kai
A wani ɓangare na wa'azin nasa, ya ce: "Ƴan'uwa, wata rana dukkanmu da muke a nan za mu mutu."
Jihohi 7 da Tinubu zai fi fuskantar ƙalubale a zaɓen 2027
Wani rahoto na Cibiyar Nazarin Zaɓe ta IRI ya bayyana cewa matsin tattalin arziki, rashin tsaro da rashin amincewar jama'a ga 'yan siyasa na daga cikin manyan abubuwan da za su iya tantance yadda zaɓen 2027 zai kasance.
Matsaloli 5 da bashin da gwamnatin Najeriya ke karɓa zai yi wa ƙasar
A sabon rahotonsa na Nigeria Development Update (NDU), Bankin Duniya ya nuna damuwa kan yadda kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen biyan basussuka ya zarce yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati a rabin farkon shekarar 2026, inda ya ƙiyasta adadin da kashi 124 cikin 100.
Akalla mutum 15 sun mutu bayan motar sojoji ta taka nakiya a Borno
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026
'Ban ga amfanin ci gaba da zama da nono a jikina ba'
'Yan watanni da suka gabata, Dr. Fatima Guéunoune ta gano cewa tana ɗauke da wani ƙari mai ɗauke da cutar daji, biyo bayan gwajin da ta yi wa kanta.
Wane tasiri takarar Makinde za ta yi ga Tinubu a kudu maso yamma?
A baya-bayan nan, babban abin da Seyi Makinde ya fi sukar gwamnatin Bola Tinubu a kai shi ne halin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa, yana zargin gwamnatin da kasa sauƙaƙa wa 'yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta.
Me ke yawan gwara kan Kwankwaso da Atiku?
Musayar yawun da ta ɓarke a baya-bayan nan tsakanin jagoran kwankwasiyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NDC da kuma jam'iyyar ADC na ci gaba da aza ayar tambaya kan fatan haɗewar ƴan hamayya gabanin 2027.
Za a hukunta faston da 'ya jawo mutuwar mutane 191 da yunwa domin haɗuwa da Yesu'
Kotun Kenya za ta yanke hukunci kan shari'ar zargin kisan gillar da ta shafi wani fasto mai wa'azi, Paul Mackenzie.
Ƴaƴan shugabannin Najeriya da suka yi fice
Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi wani matsayi na musamman ga ƴaƴan shugaban ƙasa ba, kasancewarsu kusa da madafun iko ya ba wasu damar nuna iko a zamanin mulkin iyayensu.
Su wane ne ke samar wa ƴansiyasa kuɗin yaƙin neman zaɓe a Najeriya?
A daidai lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓen na zaɓen 2027 a hukumance, hankali ya fara komawa ne kan irin rawar da kowace jam'yya za ta taka wajen jan hankalin masu kada ƙuri'a.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.



























































