Hukumar binciken kuɗi na duba bayanan lissafin kuɗin Man City

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar kula da binciken kuɗi ta Birtaniya ta tabbatar da cewa tana jagorantar bincike kan wasu matsalolin da suka shafi bayanan lissafin kuɗin Manchester City.

Financial Reporting Council (FRC) ta tabbatar a cikin wata wasiƙa da ta aikewa kwamitin kasuwanci na Majalisar Dokokin Birtaniya cewa ta karɓi ragamar "nazarin tsarin sa ido" daga Institute of Chartered Accountants in England and Wales (ICAEW) a ranar 30 ga Satumba.

Har yanzu ba a ƙaddamar da cikakken bincike a hukumance ba, amma FRC na ci gaba da gudanar da bincike da tattara bayanai kan lamarin.

Wannan na zuwa ne bayan wani kwamiti mai zaman kanya ta sami Manchester City da laifin dukkan tuhume-tuhumen da suka shafi karya dokokin kuɗi na Premier League tsakanin kakar wasan 2009-10 zuwa 2017-18, ciki har da zargin ƙara wa kungiyar kuɗi ta hanyar da ba ta dace ba da fiye da fam miliyan 900. City na ƙalubalantar tuhumar ta hanyar ɗaukaka ƙara.

FRC tana da dama da kuma ƙarin iko wajen ɗaukar matakan hukunci idan har ta samu hujjojin da ke nuna an karya ƙa'idoji. A kullum hukumar na sa ido kan ka'idojin lissafin kuɗi a manyan cibiyoyi kamar kamfanonin da ke kasuwar hannayen jari, amma ba ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ba.

Hukumar za ta iya binciken yadda kamfanin BDO, wanda shi ne mai binciken kuɗin Manchester City kan yadda ya gudanar da aikinsa domin tantance ko binciken ya kasance daidai da dokoki da ƙa'idojin da ake bi.

Haka kuma, tana da ikon ɗaukar matakan hukunci kan daidaikun mutane kamar daraktoci ko ma'aikatan kungiyar ta Etihad, idan har suna cikin tawagar ta masu lissafin kuɗi.

BDO ita ce ta biyar a jerin manyan kamfanonin lissafin kuɗi a Birtaniya, amma tana ikirarin cewa ita ce ke jagora a fannin ƙwallon ƙafa, inda take ba wa ƙungiyoyin Premier League da Championship shawara fiye da kowane kamfani.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kwamitin mai zaman kansa da ya binciki Manchester City ya gano cewa kungiyar ta bayar da rahoton kuɗinta ta wani abu da ta kira "bayanan yaudara" game da tsarin da aka yi amfani da shi wajen ɓoye asalin kuɗin masu hannun jari da aka saka a zuba, yayin da masu binciken kuɗin ba su da masaniya kan wannan tsari.

Manchester City ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kwamitin ya yanke, tana mai cewa hukuncin ya ƙunshi "manyan kura-kurai na doka da karya ƙa'ida da kuma rashin sanar da gaskiyar lamarin", don haka ba za a iya dogaro da shi ba.

Shugaban Kwamitin Kasuwanci na Majalisar Dokokin Birtaniya, Liam Byrne, ya yi kira da a bai wa Financial Reporting Council (FRC) ƙarin iko domin binciken irin waɗannan lamurra a nan gaba.

Ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Wasiƙar da mai sa ido kan harkokin kuɗi ya aike ta bayyana gibin da ke cikin ikonsa na tilasta kungiyoyin bayar da hujjoji ko kuma ɗaukar mataki kan daraktocin da ba sa ƙarƙashin dokokin ladabtarwarsa.

"Wannan na haifar da manyan tambayoyi game da ikon da ake da shi wajen hukunta kamfanoni da daraktocinsu.

"Gwamnati na da alhakin bayyana dalilin da ya sa aka yi watsi da sauye-sauyen da za su rufe waɗannan gibin da kuma abin da za a yi yanzu domin ƙarfafa tsarin ɗaukar alhaki."

Kamfanin BDO ya ƙi yin tsokaci kan lamarin.