Shin Man City tana da hujjar da za ta yi nasara a ɗaukaka ƙarar da ta yi?

A general view of The Etihad Stadium, home of Manchester City
Bayanan hoto, Etihad ce take daukar nauyin Manchester City tun daga Mayun 2009
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Manchester City na fuskantar babban ƙalubale, idan har tana son samun wata damar yin nasara a ɗaukaka ƙarar da ta shigar, bayan an same ta da laifin karya dokokin kuɗi na Gasar Firimiya a cewar wani fitaccen lauya da ya yi magana da BBC Sport.

An samu Manchester City da laifin dukkan tuhume-tuhumen da suka shafi karya dokokin kuɗi na Gasar Firimiya tsakanin kakar 2009-10 zuwa 2017-18, tare da ƙirƙirar "kwangilolin bogi" domin ƙara darajar yarjejeniyoyin tallafi na fam miliyan 830.

Kungiyar ta ce "ba ta da laifi kan zarge-zargen da Gasar Firimiya ta yi mata", kuma tana da "hujjoji da ke nuna tuhumar ta ƙunshi "bayyanan da aka yi kura-kurai kan doka da ƙa'ida da bayyana gaskiyar lamarin", kuma ba abin dogaro ba ne.

A cikin ɗaukaka ƙarar da ta shigar, Manchester City ta yi iƙirarin cewa gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ta biya kuɗin a matsayin mai hannun jari a kamfanonin masu ɗaukar nauyi, sannan kuma akwai saɓani a tuhumar da kwamitin ya yanke.

Saboda haka, City ta ce kuɗin tallafin halal ne, kuma ba masu kungiyar ne suka ƙara musu kuɗi ba.

James Severn, mamba a London Solicitor Litigation Association (LSLA) kuma abokin hulɗa a kamfanin lauyoyin Penningtons Manches Cooper, ya shaida wa BBC Sport cewa ɗaukaka ƙarar "ba wata dama ce kawai ta neman sabon kwamitin domin ya soke hukuncin ba".

"Ya kamata City ta nuna babban kuskure ta fuskar doka da ƙa'ida ko gaskiyar lamari, ko kuma wani rashin adalci a tsarin shari'ar, wadda za ta yi tasiri kai tsaye ga hukuncin da kwamitin ya yanke," in ji Severn.

"Duk da haka, Kwamitin Ɗaukaka Ƙara yana da cikakken iko na amincewa ko watsi da ɗaukaka ƙarar, sauya hukuncin ko kuma yanke duk wani umarni da ya ga ya dace."

Dole City ta tabbatar da cewa an yi kuskuren fassara hujjojin da ake da su

City
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamfanin jiragen sama na Etihad Airways, ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar nauyin Manchester City da ke tsakiyar wannan shari'ar, ya taɓa bayyana cewa gwamnatin Abu Dhabi ba ita ce ta biya kuɗin tallafin da yake bai wa Manchester City ba.

Wannan bayani ya fito ne a cikin takardun kotu a matsayin wani ɓangare na binciken da aka gudanar a New York, Amurka, a shekarar 2015.

City za ta bayar da hujjar cewa wannan bayanin bai zama abin dogara ba, kuma ba hujja ba ce da ke tabbatar da cewa ta ba da bayanai da suka zama saɓani ba.

Kungiyar ta nace cewa takardun gwamnatin suna goyon bayan matsayinta gaba ɗaya. Sai dai, a cewar James Severn, idan an riga an gabatar da waɗannan takardu a gaban kwamitin da ya yanke hukuncin, mai yiwuwa ba za su kasance masu amfani sosai ba a ɗaukaka ƙarar.

"Takardun bayanan banki da bayanan gwamnati da kuma takardun biyan kuɗi da aka samar a lokacin da aka gudanar da ma'amalolin na iya zama hujjoji masu ƙarfi idan sun nuna a sarari cewa kuɗin da ake jayayya a kansu sun fito ne daga gwamnatin Abu Dhabi maimakon masu kungiyar ɗin," in ji Severn.

"Sai dai idan wannan hujja tana gaban kwamitin tun da farko, duk da haka kuma kwamitin ya yanke hukuncin cewa tsarin yarjejeniyoyin ya kasance na bogi, to City za ta fuskanci babban ƙalubale wajen tabbatar da cewa hukuncin ya kasance kuskure mai tasiri."

Kafin a tabbatar da ɗaukaka ƙarar da City ta shigar, Etihad Airways ya fitar da wata sanarwa cewa bai taɓa samun "dama daga Gasar Premier ta samun wakilci, ko ta gabatar da bayanan da suka dace, ko kuma ta tabbatar da sahihanci da adalcin bayanan da aka dogara a kansu ba."

Severn ya ce korafin da Etihad Airways ya yi "shi kaɗai ba ya tabbatar da cewa an samu rashin adalci a tsarin shari'ar."

"Etihad Airways ba shi ne wadda ake ƙara ba, kuma mai yiwuwa bai da wani haƙƙin kai tsaye na shiga cikin shari'ar," in ji Severn.

"Mai yiwuwa kowane ɓangare daga cikin masu shari'ar na da damar samun irin waɗannan hujjoji tare da gabatar da su ga kwamitin.

"Idan Kwamitin Ɗaukaka Ƙara ya amince ya yi la'akari da sabbin hujjojin daga Etihad, to za su fi samun ƙarfi kwarin giwa, idan suna tare da takardun da aka rubuta kuma aka adana a lokacin da abubuwan suka faru."

City za ta iya kafa hujjar cewa an samu 'babban kuskure a gaskiyar lamarin'

City

Wani muhimmin ɓangare na kariyar da Manchester City za ta dogara da shi shi ne cewa Kwamitin Mai Zaman Kansa ya ba da muhimmanci fiye da kima ga saƙonnin imel da aka samo daga takardun Football Leaks.

"Idan City ta iya nuna cewa kwamitin ya fahimci saƙonnin imel ɗin ta hanyar da ba ta dace ba, ya kasa la'akari da cikakken mahallinsu ko kuma ya yanke hukunci da ya saɓa wa wasu takardun da aka rubuta a lokacin da abubuwan suka faru, hakan na iya zama babban kuskure a gaskiyar lamari," in ji James Severn.

"Kalubalen da City ke fuskanta shi ne cewa kwamitin ya saurari shaidu da yawa tare da nazarin ɗimbin takardu, amma duk da haka ya yanke hukunci mai tsauri cewa an yi yarjejeniyoyin bogi da kuma ɓoye kuɗin da masu kungiyar ɗin suka bayar."

Kieran Maguire, farfesa kan harkokin kuɗin ƙwallon ƙafa a Jami'ar Liverpool, ya shaida wa BBC Sport cewa kwamitin ya gano cewa "an tsara takardun ne daga baya domin su dace da abin da ake zargin ya faru".

"Tilas ne kwamitin ya kai ga matsayar cewa hujjojin da kuma amincin shaidun da Manchester City ta gabatar sun kasance marasa ƙarfi," in ji Maguire.

"Duk da haka, daga mahangar doka, wannan wani ɓangare ne da za a mayar da kalamai idan tawagar lauyoyin Manchester City na iya tabbatar da cewa tsarin kwamitin da kansa yana da matsala, ta yadda mambobinsa zabin Gasar Firimiya ne maimakon na Manchester City, don haka an rigaya an fifita wani ɓangare tun daga farko.

"Amma hakan dai yana da wuya sosai."

Severn ya ƙara da cewa tsoffin manyan alƙalai da manyan lauyoyin da suka zauna a kwamitin sun "shafe rayuwarsu ta aiki suna fassara bayanan shari'a masu rikitarwa, sauraron shaidu da kuma tantance irin ƙimar da ya kamata a bai wa hujjoji".

Duk da cewa ya ce "ba zai yiwu a tantance daidai yiwuwar City ta yi nasara a ɗaukaka ƙarar ba", Severn ya ƙara da cewa "ba abu ne mai sauƙi ba".

Sai dai Maguire na ganin cewa, duk da wahalar lamarin, "akwai wata hanya" da City za ta iya bi domin samun nasara.

Maguire ya ce:

"Idan aka yi la'akari da irin lauyoyin da Manchester City ta ɗauka aiki, mai yiwuwa su bi abin da aka bayyana mini a matsayin dabarar haddasa ruɗani da hayaniya.

"Wannan na nufin ƙoƙarin rusa amincin duk abin da ya shafi tsarin aikin kwamitin, maimakon kai hari kai tsaye ga hujjojin da aka gabatar.

"Na ga takardun da Abu Dhabi ta gabatar a shari'ar New York. Ni ba lauya ba ne, amma daga mahangar lissafin kuɗi, ana iya fassara su ta hanyoyi fiye da ɗaya."

Duk da cewa dokokin Gasar Firimiya sun tanadi cewa dole ne a saurari ɗaukaka ƙara cikin makonni 12, ko kafin jajiberin Kirsimeti, Severn ya ƙara da cewa "saboda girma da sarkakiyar wannan shari'a, mai yiwuwa a ɗauki lokaci mai tsawo kafin a san hukuncin da za a yanke ."