Matsayar ƴan takarar shugabancin Najeriya kan tallafin man fetur

Asalin hoton, Bola Tinubu/Atiku Abubakar/Peter Obi/Donald Duke/Facebook
Yayin da ya rage ƙasa da watanni uku kafin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, batun tallafin mai (petrol subsidy) na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za su iya tasiri kan yadda zaɓen zai gudana.
Cire tallafin mai a ranar farko ta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya haifar da ƙarin tsadar kusan komai a ƙasar, daga sufuri zuwa kayan abinci da sauran kayayyakin yau da kullum da talakawa ke amfani da su.
Gwamnati ta ce tallafin mai yana ƙara talauta Najeriya, kuma idan aka cire shi, kuɗaɗen da za a adana za a yi amfani da su wajen aiwatar da wasu ayyukan ci gaban ƙasa da za su amfanar da jama'a fiye da baya.
Sai dai kusan shekaru huɗu bayan haka, mutane da dama na ganin cewa cire tallafin ya ƙara jefa jama'a cikin talauci, duk da cewa gwamnati na ci gaba da jaddada cewa matakin ya ƙara yawan kuɗaɗen shiga tare da ƙarfafa amincewar masu zuba jari a ƙasar.
Da dama daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafe sun bayyana ra'ayoyinsu kan abin da za su yi game da tallafin mai idan suka lashe zaɓen shugaban ƙasa. Ga inda wasu daga cikinsu suka tsaya kan wannan batu:
Tinubu - 'Ba za mu koma Masar ba'

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sha bayyanawa ƙarara cewa ba za ta janye daga matakin cire tallafin mai ba.
Sabon bayanin da Tinubu ya yi kan wannan batu ya kasance ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar City Boy Movement, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke yaƙin neman sake zaɓensa.
Tinubu ya ce dawo da tallafin mai zai zama kamar a nemi Annabi Musa ya koma Masar bayan ya fito daga can.
Ya ce "Na tuna da abin da na koya a littattafan addini, a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma Alƙur'ani mai girma. Lokacin da Annabi Musa ya fito daga Masar, Bahar Maliya ta buɗe hanya gare shi. Ba za ku iya neman Musa ya koma Masar ba. Da ƙarfin gwiwarku da goyon bayanku, ba za mu taɓa komawa Masar ba."
Sai dai gwamnati ta jefa mutane cikin ruɗani a farkon wannan watan lokacin da ta sanar da cewa za ta ƙaddamar da tsarin rangwamen farashin fetur a duk gidajen man gwamnati da ke faɗin ƙasar.
Shugabannin adawa sun mayar da martani suna cewa gwamnati ta dawo da tallafin mai ne ta wata hanya dabam, amma fadar shugaban ƙasa ta dage cewa wannan tsari ba tallafi ba ne. Ta ce rangwamen kawai za a cire shi ne daga ribar da Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC) zai samu daga harkokin sayar da fetur na kamfanin.
An ce wannan tsarin rangwamen farashin fetur zai ci gaba har zuwa ƙarshen watan Oktoba, sannan daga baya gwamnati za ta bayyana matakin da za ta ɗauka na gaba.
Atiku - 'Najeriya na da arziƙin da za ta iya riƙe kanta'

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na Najeriya, Atiku Abubakar, wanda shi ma ke takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana karara cewa zai mayar da tallafin mai ta hanyar da za ta fi mayar da hankali ga waɗanda suka fi buƙata idan ya lashe zaɓen.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai dawo da tallafin ne saboda, a cewarsa, "ba a auna arzikin ƙasa da yawan kuɗin da gwamnati ke tattarawa ba, amma da irin abin da kuɗin da ke aljihun jama'a za su iya saya."
A yayin wani taron jam'iyyar ADC, Atiku ya ce:
"Dangane da batun tallafi, matsayina bai taɓa canzawa ba kuma ba zai canza ba: zan dawo da shi! Ƙasar da Allah Ya albarkace ta kamar tamu ba ta da wani dalilin da zai sa ta bar 'yan ƙasarta cikin wahala. Najeriya tana da isasshen arziki da za ta kula da mutanenta."
Ya ƙara da cewa:
"Idan farashin mai ya tashi, kuɗin sufuri ma zai tashi. Idan kuɗin sufuri ya tashi, farashin abinci ma zai ƙaru. Idan farashin abinci ya ƙaru, iyalai za su shiga cikin wahala."
Peter Obi - 'a kawar da cin hanci da rashawa, a dawo da tallafin mai'

Asalin hoton, Peter Obi/Facebook
Dangane da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce zai dawo da tallafin mai, amma da farko zai kawar da cin hanci da rashawa da ya dabaibaye tsarin tallafin.
Obi ya bayyana wa BBC cewa "Tun daga ranar farko da na fara magana kan batun tallafi, na yi magana ne kan cin hanci da rashawa; cin hanci da rashawa shi ne babban matsalar tallafin."
Ya ƙara da cewa "Zan kawar da cin hanci da rashawar, amma zan ci gaba da ba da tallafin."
Sai dai Obi, wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne da ke kudu maso gabashin Najeriya, ya sha fuskantar suka daga wasu masu sharhi da 'yan siyasa da ke cewa ba shi da tsayayyen matsayi kan batun tallafin mai, saboda a lokuta daban-daban ya bayyana ra'ayoyi mabambanta game da lamarin.
Donald Duke - 'Kamata ya yi a riƙa sayar da litar man fetur 200 a Najeriya'

Asalin hoton, Donald Duke/Facebook
Donald Duke, tsohon gwamnan Jihar Cross River da ke yankin kudu maso kudu na Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), ya ce muhawarar da ake yi yanzu kan tallafin mai tana tafiya ne bisa kuskuren fahimta.
Duke ya nuna rashin amincewarsa da matakin gwamnatin Bola Tinubu na cire tallafin mai, haka kuma bai yarda da ra'ayin Atiku Abubakar da Peter Obi na mayar da tallafin ba.
Ɗan takarar na PRP ya ce fetur dai samfur guda ɗaya ne kacal daga cikin abubuwan da ake samarwa daga ɗanyen mai, don haka gwamnati za ta iya sayar da shi a farashi mai rahusa yayin da take sayar da sauran kayayyakin da ake samu daga ɗanyen mai a farashin kasuwa.
A wata hira da aka yi da shi, Duke ya ce "Za ka iya sayar da fetur a yau kusan naira 200 kan lita, ba wai sama da naira 1,000 kan lita ba. Don haka wannan maganar tallafi, ina ganin ɗaya ce daga cikin manyan yaudare-yaudaren da aka taɓa yi, watakila ma a duniya baki ɗaya."
Ya ci gaba da cewa "Muna ƙona iskar gas fiye da ƙafa biliyan biyu a kullum ba tare da amfani da ita ba. Wannan kuwa daidai yake da lita miliyan 20 na dizal. Don haka kamar a ce akwai ruwa a yalwace amma har yanzu kifaye suna jin ƙishirwa."
Ya ƙara da cewa "Ya kamata ka yi amfani da abin da kake da shi domin samun abin da kake so. Mu ƙasa ce da Allah Ya albarkace mu da albarkatun makamashi. Ya kamata jama'a su ji daɗin waɗannan albarkatu kuma su amfana da su."
Sowore - 'Babu komai a tallafin mai sai damfara'

Asalin hoton, Omoyele Sowore
Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), ya ce bai yi imani da tsarin tallafin mai ba, amma zai dawo da duk wani tsari da zai sa ana sayar da fetur kan naira 400 kowace lita a Najeriya.
Sowore ya kuma ce zai binciki dukkan tsare-tsaren tallafin mai da suka gabata, kuma zai hukunta duk wanda aka samu da hannu a cin hanci da rashawa da sunan tallafin mai.
Ɗan takarar na AAC ya ce ikirarin gwamnatin Tinubu cewa ta cire tallafin mai gaba ɗaya "yaudara ce", domin a cewarsa:
"Tun da farko ma har yanzu suna biyan tallafin. Abin da suka yi kawai shi ne canza sunan abin da suke kira da shi."
Sowore ya zargi gwamnatin da ci gaba da kashe kuɗi wajen rage farashin fetur, duk da cewa ta bayyana wa jama'a cewa an kawo ƙarshen tallafin gaba ɗaya. Ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, zai tabbatar da bayyana gaskiya game da yadda ake tafiyar da harkokin man fetur, tare da ɗaukar matakan hukunci kan duk wanda aka samu da laifin cin hanci ko almundahana a wannan fanni.
Ma zai faru idan aka dawo da tallafin mai

Gwamnatin Bola Tinubu ta ci gaba da jaddada cewa dawo da tallafin mai zai yi wa tattalin arzikin Najeriya illa fiye da yadda yake kafin a cire shi.
Abu na farko shi ne, ba zai kasance mai sauƙi gwamnati ta fito kawai ta ce ta dawo da tallafin ba, domin an cire tallafin ne bisa tanade-tanaden Dokar Masana'antar Man Fetur.
A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a watan Agusta, ta ce:
"Saboda haka dawo da tsohon tsarin zai buƙaci cikakken tsari na doka, kuɗi da gudanarwa, ciki har da bayyana inda za a samo kuɗaɗen da za a kashe da kuma yadda za a aiwatar da manufar a ƙarƙashin tsarin kasuwar man fetur da ake da shi a yanzu."
Har ila yau, Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin fetur na iya haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin Najeriya, har ma ya sa darajar naira ta faɗi zuwa naira 3,000 kan dala ɗaya ta Amurka.
A wani taro da aka gudanar yayin Taron Shekara-shekara na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a Bangkok na ƙasar Thailand, Oyedele ya ce:
"Idan, saboda wani dalili, shugaban ƙasa ya ce ana tunanin dawo da tallafin mai, masu zuba jari za su mayar da martani nan take. Hakan zai jefa naira cikin matsin lamba mai tsanani, inda za ta iya kaiwa tsakanin naira 3,000 zuwa 3,500 ko ma 4,000 kan dala ɗaya. Haka kuma fetur ɗin da mutane ke son a yi wa tallafi zai fi tsada sosai idan aka lissafa shi da naira."
IMF ma ta shawarci gwamnatin Najeriya da kada ta dawo da tallafin mai. A maimakon haka, ta ba da shawarar a samar da manufofin tallafi da za su fi mayar da hankali ga mafi raunana da talakawan al'umma.
Sai dai masanin tattalin arziki Aliyu Ilya ya bayyana cewa tallafi a kansa ba matsala ba ne, domin:
"Babu wata gwamnati da ba ta tallafa wa wasu abubuwa ga 'yan ƙasarta."
Amma ya ce ba lallai ba ne tallafin ya kasance kan fetur. A cewarsa, gwamnati za ta iya tallafa wa fannoni da dama kamar noma, masana'antu da sauran sassa na tattalin arziki.
Duk da haka, ya yi nuni da cewa komawa tsarin tallafin fetur na baya:
"na iya zama aiki mai matuƙar wahala kuma mai ƙalubale."



























