Illoli 8 da amfani da maganin mata ke haifarwa

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A kasuwanni da shafukan sada zumunta da kuma wajen masu talla, ana yawan jin kalmomi irin su "maganin mata", "maganin gyaran gida", "ƙara ni'ima" ko "ƙara sha'awa." da sauransu.

Haka kuma ya zama ruwan dare a yanzu yadda ake cewa za a "gyara mace" a lokacin da take shirin aure, duk da cewa suma mazan ba a barinsu a baya, domin wasu sukan yi gyara kafin shiga ɗakin amarya.

Wasu kayayyakin ana sayar da su ne da sunan mafita ga matsalolin aure, inda ake ikirarin cewa suna ƙara wa mace armashi, ko kuma suna taimaka mata wajen gamsar da mijinta.

Saboda irin waɗannan tallace-tallace, wasu mata kan saya saboda shawarar ƙawaye da ƴan'uwa, wasu kuma saboda abin da suke gani a kafafen sada zumunta. Wasu ma kan yi hakan ne saboda matsin lambar al'umma da ke sa su tunanin cewa dole mace ta yi wani "gyara" domin ta zama cikakkiyar mata.

Gargaɗin likitoci

Sai dai masana harkar lafiya suna gargaɗin cewa yawancin waɗannan magunguna ba su tsallake gwaje-gwajen kimiyya da ke tabbatar da ingancin da amincinsu ba kafin a sha.

Ɗaya daga cikin ƙwararrun likitocin mata da haihuwa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, Dr Wasila Umar Darma, ta ce ya kamata mata su yi taka-tsantsan kafin amfani da duk wani abin da ake kira "maganin mata".

Ta bayyana cewa kalmar "maganin mata" tana nufin abubuwa daban-daban kuma tana ƙunsar abubuwa da dama.

A cewarta, wasu magungunan gargajiya ne, wasu na zamani, wasu ana sha ne, wasu ana shafawa, wasu kuma ana saka su a farji.

Kuma mafi yawansu ana tallata su da ikirarin ƙara sha'awa, ƙara ni'ima da matse da sauransu.

A cewar Dr Wasila, babban abin da ke damun ƙwararrun likitoci shi ne cewa yawancin abin da ake kira "maganin mata" ba a san ainihin sinadaran da ke cikinsu ba. Haka kuma, da dama ba su bi matakan binciken kimiyya da hukumomin lafiya ke buƙata kafin a sayar da su. Saboda haka, mace na iya amfani da wani magani tana zaton zai inganta lafiyarta ko rayuwar aurenta, alhali yana iya jefa ta cikin matsalolin lafiya masu tsanani.

Mene ne illolinsa?

Dr Wasila ta ce wasu illolin kan bayyana cikin ɗan gajeren lokaci, yayin da wasu kuma kan ɗauki watanni ko shekaru kafin a gane su. Hakan ya sa ƙwararriyar likiitar ta yi bayanin wasu daga cikin illolin da za a iya fuskanta

  • Matsalolin narkewar abinci

Likitar ta ce wasu daga cikin waɗannan magunguna na iya haifar da ciwon ciki, amai, gudawa ko tashin zuciya. Hakan kan faru ne saboda yadda wasu sinadarai da ke cikinsu ke iya tayar da jijiyoyin hanji ko kuma su zama masu guba ga jiki.

  • Lalacewar hanta da ƙoda

Hanta da ƙoda su ne ke tace abubuwan da mutum ya sha. Idan magani ya ƙunshi sinadarai masu haɗari ko kuma ana amfani da shi na dogon lokaci, hakan na iya lalata aikin waɗannan gabobi, lamarin da zai iya janyo matsalolin lafiya masu tsanani.

  • Rikicewar sinadaran hormones

Wasu daga cikin magungunan na iya sauya daidaiton hormones a jikin mace. Wannan na iya haddasa matsalar al'ada, wahalar ɗaukar ciki ko ma rashin haihuwa.

  • Rage sha'awa ko janyo zafi yayin saduwa

Ko da yake ana tallata wasu daga cikin magungunan da cewa suna ƙara sha'awar jima'i, Dr Wasila ta ce a wasu mata akasin haka kan faru. Wasu kan rasa sha'awa, yayin da wasu kuma kan riƙa jin zafi lokacin saduwa.

  • Matsaloli ga masu juna biyu

A cewarta, idan mace mai juna biyu ta yi amfani da wasu daga cikin waɗannan magunguna, suna iya shafar lafiyar jaririn da ke cikin mahaifa. A wasu lokuta hakan na iya janyo zubewar ciki, haihuwar jariri da wuri ko kuma wasu nakasu da matsalolin lafiya ga jariri.

  • Mu'amala da sauran magunguna

Idan mace tana shan magani saboda wata cuta kamar hawan jini, ciwon sukari ko wata lalura, wasu "magungunan mata" na iya yin mu'amala da waɗannan magunguna. Wannan na iya rage tasirin magungunan ko kuma ya ƙara musu illa.

  • Sinadaran da ba a bayyana ba

Dr Wasila ta ce wasu kayayyakin da ake sayarwa a matsayin magungunan gargajiya kan ƙunshi sinadarai irin na steroids ko wasu magungunan zamani ba tare da an bayyana hakan ga masu amfani ba. Wannan na ƙara haɗarin fuskantar matsalolin lafiya.

  • Ƙara hatsarin kamuwa da wasu nau'o'in cutar daji

A cewarta, wasu daga cikin waɗannan sinadarai na iya ƙara haɗarin kamuwa da wasu nau'o'in cutar daji ko kuma su taimaka wajen habaka cutar idan tana nan. Wannan ya haɗa da cutar dajin mahaifa, bakin mahaifa da wasu cututtukan da suka shafi al'aurar mace.

Shin akwai wani amfani?

Dr Wasila ta ce ba za a iya cewa duk wani abin da ake kira "maganin mata" ba shi da amfani ba ko kaɗan.

Ta ce idan wani magani ya bi matakan binciken kimiyya, aka gwada shi kuma hukumomin lafiya suka tabbatar da ingancinsa da amincinsa, zai iya taimakawa wajen magance wasu matsalolin lafiya da suka shafi lafiyar mata, kamar bushewar farji ko wasu matsalolin da ke da alaƙa da sha'awa.

Haka kuma, idan abin da ake kira "maganin mata" haɗaɗɗen abinci ne daga kayan marmari ko kayan lambu da ake ci a kullum, yana iya amfani ga lafiyar jiki.

Sai dai ta jaddada cewa babu isasshiyar hujjar kimiyya da ta tabbatar da yawancin ikirarin da ake yi game da magungunan gargajiya da ake tallatawa domin matse farji, gyaran gaba ko "wanke mahaifa."

"Ko da wasu mata sun ce sun ga wani sauyi bayan amfani da su, hakan kaɗai ba hujja ba ce da ke tabbatar da cewa maganin yana da tasiri ko kuma yana da aminci," in ji ta.

Me ya fi dacewa ga mata?

A cewar Dr Wasila, ba ta ba da shawarar amfani da magungunan gyaran jiki ko fata domin inganta rayuwar aure.

A maimakon haka, ta ce zai fi kyau ga mata su yi abubuwan da ke tafe:

  • Cin abinci mai gina jiki.
  • Motsa jiki akai-akai.
  • Samun isasshen barci.
  • Rage damuwa.
  • Gujewa shan taba da barasa.

Ta ƙara da cewa abin da ya fi taimaka wa ma'aurata samun gamsuwa shi ne kyakkyawar sadarwa tsakanin ma'aurata, fahimtar buƙatun juna, nuna soyayya da kulawa, da kuma magance duk wata matsalar lafiya idan ta taso.

Shawara ga mata

Dr Wasila ta shawarci mata da kada su yi amfani da magunguna ko haɗaɗɗun kayan gargajiya ba tare da sanin abin da ke cikinsu ba.

Ta kuma bayyana cewa farji yana iya tsaftace kansa, don haka ba ya buƙatar amfani da sinadarai ko ganyaye domin "wankewa."

Idan mace tana fama da bushewar farji, rashin sha'awa, jin zafi yayin saduwa ko wata matsalar lafiya, ƙwararriyar likitar ta ce hanya mafi dacewa ita ce zuwa asibiti domin a gano ainihin musabbabin matsalar sannan a ba ta maganin da ya dace.

Har ila yau, ta yi kira ga mata da kada su canja jikinsu saboda matsin lambar al'umma ko kuma saboda tunanin cewa dole ne su yi wani "gyara" domin faranta ran mazajensu.

A ƙarshe, Dr Wasila ta ce lafiyar mace ita ce mafi muhimmanci fiye da duk wani abin da ake kira "gyaran jiki."

Ta ce idan akwai wata matsalar lafiya ko ta rayuwar aure, hanya mafi aminci ita ce neman shawarar ƙwararrun likitoci domin a yi magani bisa hujjar kimiyya maimakon amfani da magungunan da ba a tabbatar da ingancinsu da amincinsu ba.