Iran ta gargaɗi Birtaniya kan duk wata haɗin gwiwa a harin da za a kai mata
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gargaɗi Birtaniya cewa duk wata haɗin gwiwa ko taimako da za ta bayar wajen kai hari kan Iran ba abu ne da ƙasarsa za ta amince da shi ba.
A wata tattaunawar waya da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, Araqchi ya ce bai halatta a yi amfani da yankin wata ƙasa ko cibiyoyinta wajen kai hari kan wata ƙasa ba, yana mai cewa hakan na iya kasancewa "aikin ta'addanci" a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, kuma ƙasar da aka kai wa hari na da haƙƙin kare kanta.
A cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Miliband ya bayyana cewa Birtaniya ba ta shiga yaƙi da Iran, kuma ta fi goyon bayan amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen rage zaman ɗarɗar a yankin.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Miliband ya ce ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, kan hanyoyin rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya da kuma kare 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz.