Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 5 da suka fito game da binciken ma'aikatar bogi
Yayin da kwamitin majalisar wakilan Najeriya ke ci gaba da gudanar da bincike kan wata ma'aikatar gwamnati da ake zargin ta bogi ce, bayanai da dama sun fara fitowa daga hukumomi da cibiyoyin gwamnati da aka gayyata domin bayar da shaida.
A makon da ya gabata ne majalisar ta kafa kwamitin bincike, ƙarƙashin jagorancin Hon. Yusuf Gadgi, wanda ya riƙa gayyatar hukukomin gwamnati daban-daban da suka jiɓanci kafuwar ma'aikatar domin daga gare su.
Daga cikin bayanan da suka ja hankali akwai iƙirarin da Ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ya yi na cewa ma'aikatar ta gabatar masa da takardun ɗaukar aiki na bogi, yayin da wasu hukumomi da suka haɗa da Ofishin Akanta Janar da Babban Bankin Najeriya suka bayyana abin da suka sani game da lamarin.
A cikin wannan muƙala mun tattara bahasin hukumomi biyar da suka bayyana a gaban kwamitin binciken.
Babban Bankin Najeriya (CBN)
Babban bankin Ƙasar (CBN) ya ce ya buɗe wa ma'aikatar asusun banki na kuɗin ƙasashen waje har guda biyu a CBN, bayan samun takardar umarnin hakan daga ofishin babban akanta na ƙasa.
Daraktan Sashen Ayyuakn Banki na CBN, Hamisu Ibrahim, wanda ya wakilci bankin a zaman kwamitin sauraron bahasin ya ce asusun biyu da CBN ya buɗe wa ma'aikar na 'Dolar Account' ne da na 'Pounds sterling'', kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
"A ranar 30, ga watan Yulin 2025, muka samu takardar umarni daga ofisn babban akanta na ƙasa, wanda ya buƙaci mu buɗe wa ma'aikatar asusun guda biyu''.
Ya yi bayanin cewa dama irin wannan aiki na buƙaytar amincewar ofishin babban akanta na ƙasa, don haka ne da suka ga wasiƙar suka aiwatar da matakin.
Sai dai ya ce tun bayan buɗe asusun guda biyu, babu wanda ya je CBN da nufin ya yi sa hannu domin fara aiki da su.
''Saboda hakan ne ma har yanzu babu ko sisi a cikinsu', in ji shi.
Ofishin babban akanta na ƙasa
A nasa Babban Akanta Janar na ƙasar ya ce wasiƙar bogi daga fadar shugaban ƙasa ce ta sa da yawa hukumomin gwamnati ciki har da ofishinsa suka amince da hukumar, har suka ba ta gudunmowa.
Yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilan ƙasar a ranar Litinin, babban akanta janar na ƙasar, Shamseldeen Ogunjimi ya ce ofishinsa ya amince da dokokin hukumar bayan samun wata wasiƙa daga fadar shugaban ƙasar, wadda daga baya bincike ya gano ta bogi ce.
Ya ce bisa tsarin aiki ofishinsa ya amince da buƙatar fadar shugaban ƙasa wajen samar da hukumar dokoki tare da amincewa da ita, kamar yadda dokar aiki da tanada, inda aka aike wa ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasa kofin takardar amincewar.
Mista Ogunjimi ya ce bayan haka ne sai ofishinsa ya sake samun wasu buƙatun, ciki har da ɗaukar ma'aikata da buɗe asusun ajiya a banki.
Sai dai ya ce duk da haka ba a tura wa hukumar kuɗi ba.
''Duk da cewa hukumar ta buƙaci a ba ta naira biliyan 27.4, hakan bai samu ba saboda kasafin kuɗu bai tanadi hakan ba'', in ji shi.
Ofishin shugaban ma'aikata na ƙasa
Ofishin shugaban ma'aikata na ƙasa wanda ke da alhakin bayar da ofishi ga hukumar ya amince da yin kuskure wajen bai wa hukumar ofishin.
Yayin da ta bayyana a gaba kwamitin, Shugabar ma'aikata ta ƙasa, Mrs. Esther Didi Walson-Jack ta ce ofishinta ta amince cewa ofishinta ya gaza gudanar da binciken da ya dace kafin bai wa hukumar ofishi a sakatariyar gwamnatin tarayya.
Mrs. Walson-Jack ta ce ofishinta nata ya dogara ne da takardun da aka gabatar masa - waɗanda daga baya aka gano na bogi ne - wajen bayar da ofishin da ba ta damar ɗaukar ma'aikata.
"Yanzu, bayan da muka ga dukkan hujjojin da kuma nazarin dukkan takardun da aka gabatar, mun amince cewa da ya kamata mu ƙara yin cikakken bincike da tantance bayanai kafin mu aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ofishinmu na bayar da amincewar kafa ma'aikatar da kuma sahalewar ɗaukar ma'aikata ga PEAC/PFIPC," in ji.
Ofishin kasafin kuɗi
Babban Daraktan Ofishin Kasafin Kuɗi na ƙasa, Tanimu Yakubu, ya ce ofishinsa ya ƙi amincewa da buƙatar hukumar na neman naira biliyan 3.8 domin biyan albashin ma'aikata.
Yayin da ya bayyana a gabana kwamitin binciken, Tanimu Yakubu ya ce a maimakon haka Ofishin Kasafin Kuɗin ne da kansa ya ƙididdige kuɗin zuwa naira miliyan 802.98, bisa yawan ma'aikatan hukumar da kuma jadawalin albashin aikin gwamnati da ake amfani da shi.
Darakta Janar ɗin ya bayyana cewa duk da cewa an ware wa hukumar jimillar kuɗi kusan naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kuɗin 2026, ba a fitar da ko sisin kwabo daga cikin kuɗaɗen ba, kuma ba a kashe komai ba, domin ba ta cika sharuddan doka da ake buƙata kafin samun damar amfani da kuɗaɗen gwamnati ba.
Mr Yakubu ya kuma ce kafuwar hukumar ta samo asali ne tun ranar 9 ga Oktoban 2019, lokacin da tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ita domin samar wa gwamnatinsa shawarwari kan manufofin tattalin arziki.
A cewarsa, tun kafin Ofishin Kasafin Kuɗi ya karɓi buƙatar a ware mata kuɗi a cikin kasafin kuɗi, Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya riga ya ba ta damar gudanar da kasafi.
Rundunar Ƴansanda
A ranar Litinin ne kwamitin binciken ya buƙaci babban sifeton ƴansandan ƙasar ya gabatar mata da shugaban hukumar a gabanta domin jin bahasi daga gare shi.
Dama dai shugaban hukumar na hannun rundunar ƴansandan bisa umarnin kotu, yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken.
To sai dai rundunar ta ce ba za ta iya gabatar da shi, har sai da umarnin kotu da ya buƙaci hakan.
Yayin da ya bayyana a gaban kwmaitin, babban mataimakin sifeton ƴansanda na ƙasa mai lura da cibiyar binciken manyan laifuka ta rundunar, Olufemi Akinol, wanda kuma ya wakilci babban sifeton ƴansandan ya ce, a ƙa'idar aiki rundunar yansanda ba ta gabatar da wanda take tsare da shi bisa umarnin kotu ba, har sai da izinin kotun.
A cewarsa rundunar ƴansanda za ta gabatar mata da Mista Adeyemi ne kawai idan kotu ta bayar da umarnin hakan.