Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashe 10 masu ƙarancin mutuwar aure a duniya
- Marubuci, Mamadou Faye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Ƙiyasin yawan mutuwar aure tsakanin ma'aurata a faɗin duniya ya nuna cewa ana samun saki 1.7 zuwa 1.8 a cikin ma'aurata 1,000.
To sai dai akwai ƙasashe da dama waɗanda nasu yawan mutuwar auren bai kai haka ba ko kaɗan, wasu ma ba kasafai ake samun mutuwar auren ba gaba ɗaya, inda ƙasashen Indiya da sri Lanka da Vietnam suke kan gaba-gaba cikin jerin ƙasashen da mutuwar aure ya yi ƙaranci sosai.
Za mu kawo muku ƙasashe 10 da ake da ƙarancin mutuwar aure a cikinsu.
Shafin WorldAtlas mai fitar da alƙaluma kan fannoni daban-daban na duniya ya yi nazari alƙaluma daga Hukumar lura da tattalin arziki da rayuwar al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya da Sashen fitar da alƙaluma na Tarayyar Turai - Eurostat da Hukumar alƙaluma kan iyali ta Indiya da kuma hukumomin fitar da alƙaluma na ƙasashen duniya wajen tattara wannan bayani.
Amma ya kamata a sani cewa ƙarancin mutuwar aure a wata ƙasa ba shi ne ke nufin cewa ma'aurata sun fi zaman lafiya ba.
Shafin WorldAtlas ya ce a mafi yawan lokuta hakan ya dogara ne a kan tanade-tanaden addini ko kuma mutuwar aure a gida ba tare da sanin hukumomi ba.
Ga jerin ƙasashen:
1. Indiya (mutuwar aure 0.01 - 0.1 a mutane 1,000)
Ana kallon Indiya a matsayin ƙasar da aure ya fi ƙarko a duniya. Amma hakan ya danganta ga addinin ma'aurata (Dokokin addinin Hindu na 1955, dokar hukuma kan aure ta 1954, tsarin aure na Musulunci da Kiristoci), duk suna taka rawa kan ƙarkon aure.
Haka nan kuma al'adar auren haɗi, wadda har yanzu matasan Indiyawa da dama suke so, da kuma rawar da iyaye da ƴan'uwa ke takawa a cikin aure na daga cikin abubuwa da suka sa ake da ƙarancin mutuwar aure a ƙasar.
Sai dai ya kamata a sani cewa a mafi yawan lokaci ba sanya Indiya cikin jerin wadanda ake nazari kan mutuwar aure a cikinsu kasancewar ana kallon tsarin rajistar aure na ƙasar bai kammala ba idan aka yi la'akari da abubuwan da ke faruwa a zahiri.
2. Sri Lanka (Mutuwar aure 0.15 a mutane 1,000)
Alƙaluma da aka sanar a hukumance sun nuna cewa Sri Lanka ce ƙasar da aka fi samun ƙarancin mutuwar aure a duniya.
Ƙasar na amfani da tsarin shari'a uku daban-daban, dangane da yankin da mutum ke rayuwa (tsarin dokar zamantakewa, dokoki na al'adar ƙabilar Kandy da kuma dokokin Musulunci), waɗanda dukkansu na da tsaurara dokokin yin saki.
Matakan da kotuna ke bi wajen tabbatar da cancantar yin saki na ɗaukar lokaci kuma suna da tsada. Haka nan kuma akwai matsi daga al'umma na ganin cewa mutum ya yi aure.
3. Vietnam (Mutuwar aure 0.2 a mutane 1,000)
Dokar aure da zamantakewar iyali ta Vietnam, wadda aka samar tun shekarar 2014, ba ta bar wata kafa ta yin saki ba, inda miji da mata suke da ƴanci iri ɗaya. Haka nan kuma wasu al'adu na al'ummar yankunan da kuma al'adar zamantakewar iyali da dangi sun ƙara tsaurara matakan yin saki.
Sai dai yanzu wannan al'ada na raguwa a birane irin su Ho Chi Minh da Hanoi, lamarin na sauyawa sanadiyyar yadda mata suke dogaro da kansu ta fuskar samun kuɗi.
4. Guatemala (Mutuwar aure 0.2 a mutane 1,000)
Guatemala ce ƙasar da ta fi karancin mace-macen aure a yankin nahiyar Amurka. Kuma ana alaƙanta hakan ga wasu abubuwa biyu: riƙo da koyarwa addinin Kirista na mabiya Katolika da kuma yawan amfani da dokokin hukuma musamman yankunan al'ummar Mayan.
5. Tajikistan (Mutuwar aure 0.3 a mutane 1,000)
Tajikistan ƙasa ce wadda kusan dukkanin mutanenta Musulmai ne, wadda take a tsakiyar nahiyar Asia.
Kasancewar al'ummarta na riƙo da tsauraran al'adun riƙe aure da kuma na kare mutuncin iyali, hakan na matuƙar rage yawan neman raba aure musamman daga ɓangaren mata.
6. Bosnia da Herzegovina (Mutuwar aure 0.3 a mutane 1,000)
Bosnia da Herzegovina ƙasa ce da ke a yankin Balkan, wadda ke da kusan mafi ƙarancin mutuwar aure a nahiyar Turai. Hakan ya faru ne sanadiyyar riƙo da addinin Musulunci da kuma bin tanadin ɗarikar Katolika na Kiristanci, sai kuma al'adar aure da ake riƙo da ita sosai musamman a yankunan karkara, wanda hakan ya sanya aure ke matukar ƙarko.
7. Chile (Mutuwar aure 0.7 a mutane 1,000)
Chile na daga cikin ƙasashe na baya-baya da suka halasta yin sakin aure a yankin nahiyar Amurka, a shekara ta 2014.
Kafin wannan lokaci abin da ake amfani da shi, shi ne soke aure, wanda yake da matuƙar tsada.
Har yanzu kundin tsarin mulki ƙasar Chile na bayar da muhimmanci sosai a kan aure a matsayin tushen al'umma haka nan mutane na riƙo da koyarwar addinin Kiristanci.
Sai dai a halin yanzu matsalar mutuwar auren na ƙara yawa daga aurarrakin da aka ɗaura a shekarar 2004.
8. Malta (Mutuwar aure 0.6 a mutum 1,000)
Malta ce ƙasar nahiyar Turai ta ƙarshe da ta halasta saki a cikin aure a hukumance, a watan Oktoban 2011, bayan wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a inda kashi 53% na al'ummar ƙasar suka nuna goyon baya.
Kafin wannan lokacin mutane na iya rabuwa amma ba tare da saki ba, idan akwai dalili mai ƙarfi.
A yanzu dokokin ƙasar Malta na buƙatar a akalla shekara hudu kafin hukumomi su amince da buƙatar rabuwar aure.
Wannan shi ne lokaci mafi tsawo a tsakanin ƙasashen Turai.
9. Peru (Mutuwar aure 0.6 a mutum 1,000)
A ƙasar Peru, bin koyarwar ɗariƙar Katolika da kuma ƙarancin yin rajistar aure a hukumance ya sanya ana da ƙarancin alƙaluma kan mutuwar aure.
Haka lamarin yake a ƙasashe da dama na nahiyar Latin America.
10. Ireland (Mutuwar aure 0.7 a mutum 1,000)
Sai a shekarar 1996 ne aka halasta yin sakin aure a Ireland bayan wata ƙuri'ar jin ra'ayin al'umma, inda masu son a halasta sakin suka samu ƙanƙanin rinjaye da kashi 53.3%.
Wata ƙuri'ar jin ra'ayin al'ummar da aka ƙara yi a 2019 ya rage tsawon lokacin da ake kwashewa ana duba buƙatar rabuwar ma'aurata daga shekara 5 zuwa 4.
Kashi 12% zuwa 15% ne na ma'aurata a Ireland aurensu ke mutuwa, wanda hakan ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da kimanin kashi 35% zuwa 45% a yammacin nahiyar Turai.
Ana alaƙanta lamarin da jan ƙafar hukuma wajen amincewa da rabuwar aure da kuma riƙo da addini.
Me hakan ke nufi?
Akwai abubuwa uku da suka fito fili daga bayanan na WorldAtlas:
- Riƙo da al'ada da addini: Riƙo da tanadin ɗariƙar Katolika a ƙasashen Latin America (Guatemala, Chile, da Peru), da kuma Sri Lanka da Indiya.
- Amincewa a hukumance da saki: A Malta 2011, Chile 2004, Ireand 1996.
- Yanke hukuncin yin tarayya ba tare da aure ba
Ya kamata a sani cewa ƙarancin mutuwar aure a waɗannan ƙasashen ba yana nufin ma'aurata sun fi samun zaman lafiya ba ne, zai iya yiwuwa an samu hakan ne sanadiyyar rashin sanar da hukumomi, cin zarafi a gida ko kuma ma'aurata na ci gaba da zama ne kawai don gudun tsangwama daga al'umma.