Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mary Habila: Abin da muka sani kan mutuwar budurwa a gidan minista Umahi
Ministan Ayyuka na Najeriya, David Umahi, ya yi magana kan mutuwar Mary Habila, wata matashiya da ke cikin tawagar masu kula da lafiyar ministan.
A ranar Alhamis ne ministan ya yi magana kan mutuwar matashiyar a karon farko, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce a faɗin ƙasar.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Umahi ya ce akwai bayanai masu yawa da suka shafi yadda Mary ta rasu.
Ya ce har ma saurayin marigayiyar ya bayyana abin da suka tattauna da Mary kafin rasuwarta.
Ministan ya ce ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan sanadiyyar mutuwar tata (autopsy) domin gano ainihin musabbabin mutuwar.
Tun da farko, mai magana da yawun ministan, Francis Nwaze, ya shaida wa BBC cewa Umahi yana son a gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar Mary, amma iyayenta ba su amince da yin gwajin gawa ba.
"An faɗa min cewa iyalan marigayiyar sun ce yin gwajin gawa ya saɓa wa al'adarsu. Amma wannan lamari ne mai matuƙar muhimmanci, kuma tana da tarihin rashin lafiya. Gwajin gawa ne kaɗai zai iya bayyana ainihin abin da ya jawo mutuwarta," in ji Umahi.
Ya ƙara da cewa Mary Habila ma'aikaciya ce a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tarayya ta David Umahi, kuma ta rasu ne a ranar 27 ga watan Yuni a gidan ministan da ke jihar Ebonyi.
"Mary ta sanar da saurayinta hancinta na zubar da jini kafin ta rasu"
Minista David Umahi ya ce kafin Mary Habila ta rasu, ta sanar da saurayinta cewa jini na zuba daga hancinta.
Da yake magana a wani taron manema labarai ranar Alhamis, Umahi ya ce bayan Mary ta shaida wa saurayin nata halin da take ciki, ya ba ta shawarar ta sanar da shugabanta a wurin aiki, amma daga baya ta ce jinin ya tsaya.
"Ta yi magana da saurayinta kafin ta rasu, inda ta ce hancinta na zubar da jini. Duk da haka sai saurayin ya ce mata dole ta sanar da halin da take ciki," in ji Umahi.
"Sai saurayin ya ce mata, 'Ba zan ci gaba da magana da ke ba tun da kina zubar da jini, hakan na iya ƙara miki matsala.' Amma Mary ta roƙe shi kada ya katse wayar. Duk da haka, saurayin ya katse kiran. Bayan minti uku ya sake kiranta, amma ba ta ɗauki wayar ba."
Umahi ya ce washegarin rasuwarta ne abokan aikinta suka ga gawarta bayan sun kasa tuntubar ta.
A cewarsa, ƙofar ɗakin da take ciki a kulle take, lamarin da ya sa aka karya ƙofar kafin aka tarar da ita kwance babu rai, yayin da famfon ruwa ke ci gaba da zuba.
"Ta kulle ƙofar ɗakinta. Da safe da aka kasa samun ta, sai aka balle ƙofar, aka tarar da famfon ruwa na ta zuba. Abin da ke ba ni mamaki a wannan ƙasa shi ne yadda ake siyasantar da komai."
Ministan ya kuma yi kira ga jama'a da kada su mayar da mutuwar Mary zuwa batun siyasa.
"Kun san me? Ni David Umahi ne. Ban taɓa jin tsoron faɗa ba. Dole mu yi taka-tsantsan sosai. Wannan yana da matuƙar muhimmanci."
Ba na son a binciki mutuwar ƴata - Mahaifin Mary
Duk da cewa ƴan'uwan Mary sun bayyana cewa ba sa son a yi binciken gawa domin gano musabbabin mutuwarta, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce za ta ci gaba da gudanar da binciken.
A cikin wata takarda da mahaifinta, Tanko Habila Wisdom, ya gabatar a Babbar Kotun jihar Ebonyi, ya bayyana cewa ba su amince da buƙatar yin binciken gawa da ministan ko wata tawagar likitoci suka buƙata ba.
Mahaifin marigayiyar ya ce duk da cewa suna maraba da duk wani yunƙuri na gano abin da ya kashe ƴarsa, ba su son a taɓa gawarta ko wani sashe na jikinta.
"Muna maraba da duk wani mataki na gano abin da ya yi sanadin mutuwar ƴata, amma ni da iyalina ba za mu amince a yi binciken gawa ba. Muna roƙon a bar gawarta yadda take."
Ya kuma buƙaci hukumar ƴansanda da ta dakatar da duk wani bincike, tare da roƙon ƴansanda su ba su gawar domin su yi mata jana'iza.
Haka kuma ya ce ba za su amsa gayyatar ƴansanda ko kotu kan lamarin ba, saboda a cewarsa ba su zargin cewa "an aikata wani laifi" a mutuwar Mary.
Ya ƙara da cewa wannan ce matsayar gaba ɗaya ahalinsu, ba tare da wani ya tilasta musu ba.
Za mu gudanar da bincike - Ƴansanda
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da cewa za ta gudanar da binciken gawa domin gano ainihin musabbabin mutuwar Mary.
Mai magana da yawun rundunar, Joshua Ukandu, ya ce Mary na cikin tawagar ma'aikatan lafiya da aka tura tare da Ministan Ayyuka, David Umahi, zuwa garinsu na Uburu, inda aka samu gawarta daga cikin ɗakunan gidan.
Ya ce bayan samun rahoto kan faruwar lamarin, jami'an ƴansanda na Ohaozara sun isa wurin, sannan Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tarayya ta David Umahi da ke Uburu ta tabbatar da cewa Mary ta rasu a ranar 27 ga Yuni.
Ukandu ya ƙara da cewa an miƙa binciken ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), kuma rundunar na jiran zuwan ƴan'uwanta ko wakilansu domin a gudanar da binciken gawar a hukumance.
Abin da muka sani kan mutuwar Mary Habila
A ƙarshen watan Yuni ne aka fara yaɗa labarin mutuwar Mary Habila, wata ma'aikaciyar jinya mai shekara 26, wadda ma'aikatan Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tarayya ta David Umahi da ke jihar Ebonyi suka tabbatar cewa ta mutu bayan an garzaya da ita.
Mary, wadda ƴar asalin jihar Kaduna ce, ta rasu ne a ranar 27 ga watan Yuni a harabar gidan Ministan Ayyuka na Najeriya, David Umahi, bayan ta yi tafiya zuwa jihar Ebonyi tare da tawagar masu kula lafiya na ministan.
Bayan hoton gawarta ya bazu a kafafen sada zumunta, jama'a da dama sun yi ta kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya jawo mutuwarta.
Daga cikin masu yin wannan kira har da ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, waɗanda suka buƙaci a kafa kwamitin bincike na musamman kan mutuwar Mary Habila.
Sai dai mai magana da yawun Minista David Umahi, Francis Nwaze, ya shaida wa BBC cewa ba a cikin gidan ministan Mary ta rasu ba.
Ya ce ta rasu ne a ɗaya daga cikin ɗakunan ma'aikata da ke cikin harabar gidan.
"Ginin ba ba ya cikin gidan da ministan ke zama. Gidajen ma'aikata ne da ke cikin harabar gidan. Ba a nan take zama ba, tana zuwa ne kawai idan akwai aikin da za su yi," in ji shi.
Hoton da aka yaɗa ma an ɗauke shi ne a ɗaya daga cikin gidajen ma'aikatan Asibitin Koyarwa na David Umahi, ba gidansa ba."
Mahaifin Mary ma ya tabbatar a cikin takardar rantsuwar da ya gabatar a kotu cewa ƴarsa ma'aikaciya ce a Jami'ar Lafiya ta David Umahi, kuma tana aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya ta musamman ga Ministan Ayyuka da kuma wasu daga cikin na kusa da shi.
Takardar ta kuma nuna cewa Mary tana zama ne a masaukin baƙi na ministan da ke Abuja, yayin da idan tana jihar Ebonyi take sauka a gidajen ma'aikatan da ke cikin harabar gidan.