Shari'o'i huɗu da jam'iyyar ADC ke fuskanta gabanin zaɓen 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ake ƙara kusantar babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) na ci gaba da fuskantar shari'o'in da matsalolin cikin gida.

A makon jiya ne dai kotun ɗaukaka ƙara ta yi wani sabon hukuncin, wanda ake ganin zai zama koma-baya ga ɓangaren shugabancin David Mark, wanda shi ne tsagin da Atiku Abubakar ke takara.

Rikicin da ya dabaibaye ADC ya fi karkata ne kan tambayar waye ke da ikon jagorantar jam'iyyar da kuma tsare-tsarenta domin fuskantar babban zaɓen da ke tafe.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, kotuna daban-daban sun fara duba ƙarar da suka shafi sahihancin shugabancin jam'iyyar, da kuma matsayin wasu matakan da aka ɗauka a ADC gabanin zaɓen 2027.

Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu shari'o'in da suka yi wa jam'iyyar dabaibayi a daidai lokacin a take fuskantar lokaci mafi muhimmanci a siyasa.

Shari'ar Nafiu Bala da ADC

Daga cikin manyan ƙalubalen shari'a da ke fuskantar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) gabanin zaɓen 2027, akwai shari'ar da Hon. Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, ya shigar yana ƙalubalantar sahihancin shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.

Shari'ar ta zama ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye ADC.

Nafiu Bala ya kai ƙarar ne a kotun tarayya da ke Abuja, inda ya ƙalubalanci yadda aka kafa shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar da kuma Rauf Aregbesola a matsayin sakataren ƙasa.

A cikin ƙarar, Nafiu Bala ya nemi kotu ta hana David Mark, Aregbesola da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya ci gaba da gabatar da kansu a matsayin halastattun shugabannin ADC.

Bala ya yi iƙirarin cewa bai yi murabus daga matsayinsa na mataimakin shugaban jam'iyyar ba, kuma bisa kundin tsarin mulkin ADC, ya kamata ya samu damar jagorantar jam'iyyar bayan ficewar tsohon shugaban ƙasa na ADC, Ralph Nwosu.

Rikici kan shugabannin jihohi

Babbar shari'ar da ta fi ɗaukar hankali ita ce wadda ta shafi rikicin shugabancin jam'iyyar da kuma jagorantar tsare-tsarenta.

Rikicin ya ɓarke ne bayan ɓullar sabon tsarin shugabanci ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, da wasu manyan ƴan siyasa da suka haɗa kai domin ƙarfafa ADC a matsayin babbar jam'iyyar adawa kafin zaɓen 2027.

Sai dai wasu shugabannin ADC na jihohi sun ƙalubalanci wannan sabon tsarin, suna cewa kwamitin shugabancin ƙasa ba shi da ikon rusa zaɓaɓɓun shugabannin jihohi ko kafa sababbin kwamitoci ba tare da bin kundin tsarin mulkin jam'iyya ba.

Kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci kan batun, inda ta goyi bayan matsayin shugabannin jihohin tare da cewa dole ne a mutunta tsarin da kundin jam'iyya ya tanada.

Ɗaukaka ƙarar shari'ar shugabannin jihohi

Bayan hukuncin Kotun Tarayya, ɓangaren da ke goyon bayan shugabancin David Mark ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Babban abin da kotun ta duba shi ne ko shugabancin ƙasa na ADC yana da ikon kafa kwamitoci na musamman domin gudanar da tarukan jam'iyya a jihohi.

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin baya, inda ta hana hukumar zaɓe ta ƙasa INEC amincewa da tsagin Mark.

Shari'ar neman soke rajistar ADC

Wata babbar ƙarar da ta shafi jam'iyyar ita ce wadda aka shigar domin neman a soke rajistar ADC a matsayin jam'iyyar siyasa mai rijista.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa ADC da wasu jam'iyyu ba su cika wasu sharuddan doka da ake buƙata domin ci gaba da kasancewa cikin jerin jam'iyyun da INEC ta amince da su ba.

Bayan ADC, sauran jam'iyyun da ke fuskantar sokewa su ne: APP da AA da AP da ZLP.

Jam'iyyar ta ƙalubalanci matakin ta hanyar ɗaukaka ƙara domin kare matsayinta na jam'iyya da ta bi matakan da suka dace wajen rajista.

ADC ta zargi APC da kunna wutar rikici a jam'iyyun adawa

A baya dai jama'iyyar hamayya ta ADCn ta sha nananta cewa jam'iyya mai mulki ta APC ce ke haddasa rikice-rikicen a cikin jam'iyyun adawa.

A wata tattaunawa da BBC, Faisal Kabir, jami'i ne a ofishin watsa labarai na jama'iyyar ta ADC bangaren David Mark, ya ce suna zargin akwai sa hannun gwamnati wajen ganin sai an samu cikas a cikin shugabancin jam'iyyar ADC.''

''Tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnati ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba, duba da halin da suka sa Najeriya a ciki. Don haka wannan firgici ne da tsoro ya sa gwamnati ke ƙoƙarin lallai sai shugaba Tinubu ya rasa wanda zai kara da shi a zaɓen 2027.'' In ji Faisal Kabir.