Wane saƙo gwamnatin Iran ta aike a Jana'izar Khamenei?

    • Marubuci, بخش مانیتورینگ
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی‌بی‌سی
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Jana'izar Ali Khamenei, tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ita ce babbar jarabawar ƙarfin siyasa ta farko ga gwamnatin ƙasar tun bayan rasuwarsa, kuma dama ce ta nuna tasirin rusuwar tasa ga ƴan gida da ƙasashen waje.

Kafafen yaɗa labaran Iran sun shafe kwanaki suna nuna hotuna da bidiyon dandazon mutanen da suka halarci janaizar a Tehran.

Gidan talabijin ɗin ƙasar ya bayyana jana'izar a matsayin wadda ta ''kafa tarihi'' yayin da jaridu suka ce ''ba a taɓa ganin irin wannan janaiza ba a cikin wannan ƙarni'' sannan mahukunta a ƙasar na ganin yawan mutanen da suka halarci janaizar a matsayin wata manuniya kan goyon baya ga tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Baya ga hotuna da bidiyon masu makoki, janaizar ta zamo wani abu mafi girma da ya ɗauki hankalin kafafen yaɗa labaran duniya a ƴan shekaraun nan.

Daga farkon makokin har zuwa duk wani taro da addu'o'i da aka yi, ya zuwa jana'izar da kuma manyan mutanen da suka halarta, duk wasu abubuwa ne masu kama da tsararren abu mai aikewa da saƙonnin siyasa a lokaci guda.

A halin yanzu, masu adawa da gwamnati da masu sa ido na ƙasashen waje sun bayar da fassarori da nazari daban-daban game da wannan taron.

Ta yaya taron ya nuna ƙarfin Iran?

Rasuwar jagoran addinin Iran a lokacin da ƙasar ke tsakiyar yaƙi ta zamo ƙalubalen siyasa mafi girma da Iran ta taɓa fuskanta a tarihi.

Mahukunta a Iran sun yi amfani da jana'izar wajen bai wa jama'ar ƙasar tabbacin cewa duk da yaƙin da ake ciki, gwamnati na nan daram kuma dukkan ressan ta suna aiki yadda ya kamata a ƙarƙashin sabon jagora.

An riƙa nuna dandazon da mutane suka yi a wajen jana'izar a matsayin sabunta goyon bayan jama'a ga Jamhuriyar Musulumci ta Iran, a madadin taron makoki da bankwana da marigayin.

Mohammad Baqer Qalibaf, kakakin majalisar ƙasar kuma ɗaya daga cikin masu ƙarfin faɗa a ji tun bayan kisan Ali Khamenei, ya bayyana ƙarara cewa gagarumin taron manuniya ce kan biyayyar da jama'a ke yi ga sabon jagoran addinin ƙasar Mojtaba Khamenei, yana mai jaddada saƙon da gwamnatin ƙasar ke yaɗawa cewa za a ci gaba da tafiyar da Iran har bayan waɗanda suka kafa ta.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun yayata wannan matsaya ta hanyar yaɗa duk abubuwan da suka faru a lokacin jana'izar daga Tehran zuwa Qum da kuma Mashhad, aka kuma tsallaka zuwa biranen Najaf da Karbala na Iraqi.

A matakai da dama kafafen sun riƙa bayyana abin a matsayin ƙuri'ar raba-gardama mai jaddada Jamhuriyar Musulumci ta Iran.

Maƙasudin bayar da fifiko wajen fayyace wannan shi ne: Jamhuriyar Musulumci ta Iran ta ci gaba da zama daram duk da yaƙi da takunkumi da kuma kisan jagoranta.

Daga zaman makoki zuwa gangamin nuna ƙarfin siyasa

Idan ci gaba da mulkin ƙasar na cikin saƙonnin da jami'an gwamnatin ke neman aikewa, to akwai kuma ƙoƙarin nuna jajircewa da ƙarfin hali. A madadin nuna alhinin rashin Ali Khamenei sai mahukunta a Iran suka mayar da hankali wajen nuna abin da ya faru a matsayin shahadar da dole a ɗauki fansar ta nan gaba.

Wani saƙo da aka riƙa aikewa a duk tsawon tarukan jana'izar shi ne kiran a ɗauki fansar kisan Khamenei kan Amurka da Isra'ila.

Mafi yawan masu halartar jana'izar suna ɗauke da jajayen tuta ɗauke da rubutun "Ya Latharat al-Hussein," wani abu da mabiya shi'a suka ɗauka a matsayin daɗaɗɗiyar al'ada mai jaddada goyon baya ga jagoransu.

Masu gabatar da shirye-shirye a gidajen talabijin ɗin ƙasar sun ce mutanen da suka halarci jana'izar suna ɗauke ne da ''tutocin neman a ɗauki fansa ba na makoki ba,'' wani abu da ke nuna yadda taron ya rikiɗe zuwa na neman amincewar siyasa a madadin makoki.

Su ma manyan jami'an sun riƙa kambama lamarin. Mohammad Baqer Qalibaf ya ayyana cewa ''za a hukunta'' masu hannu a kisan Ali Khamenei kuma ya bayyana taron a matsayin fito na fito da Amurka da Isra'ila.

Ma'aikatar tattara bayanan sirri na tsaro ta yi amfani da irin kalaman tana cewa "Damuwar da ke cikin zukatan Iraniyawa za ta gushe ne kawai idan aka ɗauki fansar kisan jagoran nasu.''

Dakarun juyin juya-halin ƙasar ma sun bayyana irin wannan saƙo a wajen jana'izar suna shan alwashin yin ramuwa.

Ya aka yi taron jana'iza ya rikiɗe zuwa na diflomasiyya?

Taron jana'izar wata dama ce ga gwamnati ta nuna irin ƙarfin ikon da take da shi har a tsakanin ƙasashen duniya.

Mahukuntan Iran sun ce ƙasashe aƙalla 100 suka aike da wakilai wajen taron, suna jaddada zuwan wakilai daga Rasha da China da Pakistan da kuma ƙasashen yankin Gulf.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayar da rahotan yadda aka ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da tsaro da kuma haɗakar tattalin arziki a yayin taron jana'izar.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a yayin taro da wakilan Hezbollah da Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa ya jaddada shirin Iran na goyon baya da kuma tallafa wa duk wani yunƙuri na turjiya ga Isra'ila.

Shugaba Masoud Pezzekian, a yayin wani taro da jami'an da suka halarci taron jana'izar ya yi kiran a faɗaɗa haɗakar siyasa da bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yankin.

Kafafen yaɗa labarai sun yaɗa rahotannin da ke nuni da ƙarfin ikon da Iran ta nuna saboda yadda suka ce duk da Amurka ta yi barazana ga ƙasashen duniya kan halartar taron jana'izar, an samu da dama da suka halarta.

Jayayya kan yawan mutanen da suka halarci taron jana'izar

Dandazon jama'a a wajen jana'izar Ali Khamenei ta zamo babban abin tattaunawa a kafafen sada zumunta a Iran, inda masu goyon bayan gwamnati ke iƙirarin cewa mutane aƙalla miliyan 24 suka halarci tarukan da aka shafe kwanaki ana yi.

Amma masu suka sun ce an kambama alƙalumman, suna kafa hujja da hotunan da tauraron ɗan'adam ya ɗauka.

Kafar FactName mai binciken ƙwaƙwaf wacce ke gudanar da ayyukan ta ba a cikin Iran ba ta yi ƙiyasin cewa jimillar mutanen da suka halarci ƙololuwar taron jana'izar a babban masallacin Tehan ba su fi 300,000 ba kuma ta ce idan aka haɗa mutanen baki ɗaya ba za su zarce miliyan ɗaya ba.

Mahukunta a Iran na ganin taron jana'izar a matsayin wani abu na haɗin kan ƙasa, yayin da masu adawa da gwamnati a ƙasar ke jayayya da hakan.

Kafafen yaɗa labaran gwamnati sun ce yawan mutanen alama ce ta goyon bayan jama'a da gwamnati ke da shi.

Amma ƴan adawa na ɗora ayar tambaya a kai. Sun ce mutane sun halarci jana'izar ne saboda dalilan su daban-daban, ciki har da aƙidar addini da ƙabilanci da kuma fatan shiga cikin jama'a domin a shaida wani abin tarihi a tare da su.

Kamar dai yadda aka saba a manyan jana'iza da gwamnatoci ke jagoranta, hotunan mutanen da aka yaɗa ba za su iya zama tabbacin goyon baya ga tsarin siyasa ko gwamnatin ƙasa ba.

Amma a jana'izar Ali Khamenei, an ga sauyi a wannan matsaya domin kuwa ta zamo hanyar aikewa da muhimmnin saƙo wanda zai iya sauya tunani game da makomar Jamhuriyar Musulumci ta Iran.