Yadda ce-ce-kuce ya ɓarke a PDP bayan Wike ya ce INEC ta karɓi ƴan takararsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam'iyyar PDP, bayan da ɓangaren Wike ya ce hukumar zaben Najeriya INEC, ta karɓi sunayen waɗanda za su yi wa jam'iyyar takara a zaben 2027 .

Wannan matakin dai ya haifar da musayar kalamai tsakanin ɓangaren Wike da Tanimu Turaki, da ke da'awar su ne halattatun shugabannin jam'iyyar bayan wani hukunci da wata babbar kotun ƙasar ta yanke.

Wike dai ya tabbatar da cewa hukumar zaɓen ƙasar ta ba su lambobin shiga rumbunta domin miƙa sunayen waɗanda za su yi musu takara.

To sai dai ɓangaren Tanimu Kabiru Turaki, ya ce da sake wai an ba mai kaza kai, kuma a yanzu haka suna kotun ƙoli domin sauraren hukuncin ƙarshe da zai tabbatar da makomar jam'iyyar, saboda haka matakin amincewa da ƴantakarar ɓangaren Wike, lamari ne mai kama da almara.

Farida Umar ita ce mai magana da yawun ɓangaren Tanimu Turaki, ta shaida wa BBC cewa, su ma sun riga sun kai dukkan abubuwan da INEC ke buƙata akan ƴan Takara, don haka idan har an karɓi na ɓangaren Wike, to suna ɓata lokacinsu ne.

Ta ce,"Magana na kotu yanzu haka, umarnin da kotun ƙoli ta bayar da shi ne kwamitin amintattu ne ke da iko ya naɗa shugaban jam'iyya a PDP, kuma kwamitin ya naɗa shugabannin riƙo, don haka su ne za su kai sunayen ƴan takarar PDP, ba ɓangaren Wike ba."

Su ma a nasu ɓangaren na Wike, sun ce abokan jayayarsa na ɓata lokacinsu wajen yaudarar ƴan takarar da suke marawa baya ta hanyar karɓar kuɗaɗensu na sayen fom alhali ba su ne hukumar ta INEC ta amince da su ba. inda suka ce akan tilas Turaki zai dangana da wannan jayayya domin kuwa hukumar zaɓen ba ta san da zamansa ba.

Muhammed Jangudu Haruna, shi ne mai magana da yawun ɓangaren na Wike, ya shaida wa BBC cewa, zancen cewa ana kotu eh haƙiƙa haka ne don akwai wata shari'a ta daban da suka kai hukumar zaɓe cewa suna wai IINEC, ɗin ta aminta da su.

Wannan dambarwa dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaɓen ta INEC ta fitar da wata sanarwar ƙara wa'adin lokacin da jam'iyyu za su miƙa sunayen ƴan takararsu har ya zuwa ranar 14 ga wannan watan na Yuli na 2026.