Shin ko almajiranci ya taimaka wajen bunƙasar Boko Haram?

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja.
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A duk lokacin da aka yi zance Boko Haram, daga fitattun waɗanda ake tunawa akwai tsohon shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau.

Da wahala a iya tantance ranar da Shekau ya yi ban-kwana da iyayensa a ƙauyen Shekau, da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe, domin tafiya Maiduguri neman ilimin addini.

Amma abin da aka tabbatar shi ne tun yana ƙaramin yaro aka tura shi jihar Borno da ke maƙwabtaka da jiharsa ta Yobe domin karatun Alƙur'ani a tsarin almajiranci.

Sai dai yaron da aka yi tunanin zai koyi karatu ya zama malami, a ƙarshe sai ya ɓuge da zama fitaccen mayaƙi da har Amurka da wasu ƙasashen duniya suka kasance suna nema ruwa a jallo.

Tsarin karatun almajiranci tsohuwar hanya ce ta koya da koyar da Alƙur'ani da sauran ilimi na addinin Musulunci mai dogon tarihi.

Tsarin ya ƙyanƙyashe malamai da dama, waɗanda daga baya suka yi shuhura wajen karantarwa da wa'azi da ma alƙalanci a kotunan Musulunci.

Sai dai a yanzu ana yawan ta'allaƙa ta'azzarar rikice-rikicen Boko Haram da almajiranci, inda ake zargin mayaƙan sukan ɗauki mabarata su canja musu tunani su mayar da su mayaƙa.

Daga wa'azi zuwa ɗaukar bindiga

Muhammad Yusuf ne ya jagoranci assasa ƙungiyar a garin Maiduguri na jihar Borno a yankin arewa maso gabas.

Da farko ta kasance ƙungiyar wa'azi da koyar da addini, inda ta fara samun karɓuwa sosai a tsakanin matasan jihar, har ma ta tasirinta ya fara naso zuwa jihohin arewacin Najeriya.

Sai dai abubuwa sun fara canjawa ne tun da jami'an tsaron Najeriya suka kashe Muhammad Yusuf a watan Yulin 2009, lamarin da ya matuƙar jan hankalin ƙasashe duniya.

Sai dai rasuwar tasa ce ta bar da ƙura, inda Shekau ya maye gurbinsa, sannan a ƙarƙashinsa ƙungiyar ta rikiɗe zuwa ƙungiyar ƴanbindiga masu kai hare-hare har ma da kisa.

Da farko kamar yadda sunansu ya nuna, suna kai hare-hare ne a kan jami'an tsaro da kadarorin gwamnati, amma daga baya lamarin ya ɗauki sabon salo, inda suka fara haɗawa da fararen hula.

A wani rahoton ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya UNOCHA, ya ce zuwa shekarar 2024, rikicin Boko Haram ya raba aƙalla mutum miliyan 2.3 a jihohin Borno da Adamawa da Yola.

Daga adadin rahoton ya ƙara da cewa akwai miliyan 1.7 da suke tsere zuwa jihohi maƙwabta, duk da cewa akwai adadi mai yawa da suka fara komawa garuruwansu saboda sauƙi da aka fara samu.

Talauci da rashin adalci

Tun daga wannan lokaci, wata tambaya ta fara yawo a cikin al'umma: Shin akwai alaƙa tsakanin tsarin almajirci da Boko Haram?

Rahoton United Nations Development Programme (UNDP) mai suna Journey to Extremism in Africa ya nuna cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi suna ɗaukar mambobi daga kowane mataki na rayuwa ciki har da almajirai da masu ilimi da ƴan kasuwa da matasa.

Rahoton ya ce abubuwan da ke kan gaba wajen jefa matasa cikin ƙungiyar su ne:

  • Talauci
  • Rashin adalci
  • Raashin aikin yi
  • Cin zarafin jami'an tsaro
  • Wa'azin tsattsauran ra'ayi

Alaƙa tsakanin almajiranci da Boko Haram?

Kabiru Adamu mai bincike ne kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited ya ce an yi bincike da dama kan matsalar a baya.

''Har gwamnatin Najeriya ta ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ta gudanar da bincike kan ko akwai alaƙa tsakanin almajiranci da matsalar tsaro. Sannan kamfanoni masu zaman kansu sun yi bincike," in ji shi.

Masanin harkokin tsaron ya ƙara da cewa dukkan binciken da aka yi sun gano abubuwa da dama.

"Amma ya kamata mu fara da tarihin tsarin. Ya kasance tsari ne don koyar da ilimin addini, amma yanzu abubuwa da yawa sun shiga ciki. Daga cikin abubuwan da suka shiga kamar yadda bincike ya nuna akwai:

Hatsarin shig cikin ƙungiyar: "Da farko shi ne hatsari ko kasada da yake ciki da ma yake jefa yara da suke ciki da al'umma dangane da yadda ƙungiyoyin da suke faɗa da gwamnati ke ɗaukarsu."

Sai Kabiru Adamu ya nanata cewa babu shaida tabbatacce da ke nuna cew suna shiga ƙungiyoyi, "amma dai ana iya ɗaukarsu saboda ababe da yawa da suka shiga tsarin."

Masanin ya ce za a yi amfani da wa'azi a ja hankalinsu "saboda dama karatu suke yi. Idan aka yi rashin dace malaminsu ko na kusa da shi ko wuraren da suke zuwa akwai masu irin tunanin mayaƙan za su iya shiga. Na biyu amfani da kuɗi wajen jan hankalinsu su shiga."

Masanin ya kuma ƙara da cewa tsarin yakan taimaka wajen ta'azzarar aikata laifuka a cikin birane.

"Bincike ya nuna cewa yaran da aka jibge da ba sa samun kula, ƙungiyoyi na amfani da su wajen aikata laifuka musamma sace-sace a birane."

Ya ƙara da cewa tsarin na janyo safarar jama'a ko jefa su cikin hali na tagayyara. "A ƙarƙashin wannan bincike ya nuna cewa ana wahalar da su ta hanyoyi da yawa ciki har da saka su bara wanda ba na kansu ba, wasu sukan yi bara su kai wa na gaba da su, sannan akwai rhotannin cin zarafinsu."

"Akwai kuma cututtuka da suke iya ɗauka a sanadiyar yanayin wurin da suke zama, wanda sukan iya yaɗawa a cikin al'umma."

Rawar kafafen sadarwa

Ganin an daɗe ana zargin tsarin na almajiranci da hannu a ta'azzarar matsalar tsaron, Kabiru Adamu ya yi zargin cewa kafafen sadarwa sun taimaka wajen ganin hakan da ake yi.

"Kafafen sadarwa musamman na kudancin Najeriya sun taimaka. Yawanci ba su fahimci tsarin ba, sai suka yi masa mummumar fahimta kuma suka riƙa watsa labarai a haka, kuma yawancin labaran na ɓatanci."

Kabiru Adamu ya ƙara da cewa tsarin ya yi amfani a baya, musamman a lokacin da yake da ingancinsa, inda a cewarsa ya taimaka wajen koyo da koyar da ilimin addinin Musulunci.

"Amma matalolin da ke tattare da shi a yanzu sun yi tasiri sosai, kuma kafafen watsa labarai sun yi tasri, shi ya sa yanzu ake ɗaura dukkan matsalolin ƙasar a kansu," in ji Kabiru Adamu.

Masanin tsaron ya ba da shawarar hanyoyin da za a bi wajen inganta tsarin, inda ya fara da bayyana buƙatar da ke akwai ta sanya ilimin boko a cikin tsarin karatun na almajiri.

"Sannan a yi amfani da tsarin doka kamar na kare haƙƙin da tsare-tsaren zamantakewa da rayuwa. Gwamnati ta yi aiki da shugabanni al'umma da sarakuna wajen tabbatar da gyara tsarin da inganta shi."