Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matasan Najeriya ke rububin zama ƴansanda - Mutum nawa ake ɗauka?
Sama da matasan Najeriya miliyan ɗaya ne suka nemi shiga aikin soja da ɗansanda a ɗauka biyu na kowanne da aka yi na baya-bayan nan, lamarin da ya sa ake tambayar me ya sa ake cigaba da sha'awar shiga aikin.
A tarihin Najeriya, da farko-farkon aikin ɗamara ba na kowa ba ne, domin a shekarun baya, matasa da dama kusan tilasta musu aka yi suka shiga aikin ta hanyar ko dai zuwa garuruwansu a ɗauke su ko zuwa makarantu.
Sai dai yanzu lamarin ya sauya matuƙa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da maganganun cewa jami'an tsaron ƙasar na fuskantar ƙalubalen rashin albashi mai kyau da rashin alawus, sannan uwa-uba da rashin kayan aiki masu inganci.
Haka nan kuma jami'an tsaron a yanzu na shiga cikin hadari sosai sanadiyyar ayyukan an bindiga da kuma ungiyoyin masu dauke da makamai waɗanda ke kai musu hare-hare.
Matasa
Rundunar ƴansandan Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake ganin matasa na yawan neman shiga.
A lokacin ɗaukar jami'an na shekarar 2023/2024, Hukumar Kula da Ayyukan Ƴansanda (PSC) ta ce mutum 547,774 ne suka nemi shiga aiki.
Daga cikin waɗanda suka nema, 358,900 ne suka cika sharuddan farko bayan tantancewa, sannan 171,956 aka tantance domin jarabawar kwamfuta (CBT). Daga ƙarshe, an ɗauki mutum 10,000 da aka horar a matsayin ƴansanda.
Waɗannan alƙaluma sun nuna cewa fiye da rabin miliyan ne suka fafata domin samun guraben aikin wanda ke nuna irin rububin da matasan ƙasar ke yi wajen shiga aikin.
Haka kuma a ɗaukar da hukumar ta yi na baya-bayan nan wato na 2025/26, masu neman shiga aikin sun kai 616,873 daga faɗin Najeriya.
Daga cikinsu, 434,604 ne suka cancanci zuwa matakin tantancewa. A cikin waɗanda suka nema, sannan a ƙarshe hukumar ta sanar da ɗaukar matasa 50,000 da za su samu horon zama ɗansanda.
Aikin soja
A ɓangaren aiki soja ma haka abin yake, inda ɗaukar ƙarshe da aka yi na sojin ƙasa wato 91RRI, rahotanni sun nuna cewa aƙalla matasa 38,000 ne suka rubuta jarabawar neman shiga aikin.
Tuni aka fitar da jerin waɗanda suka samu, amma BBC ba ta samu cikakken jerin sunayensu ba.
Sai dai rundunar da fitar da jerin waɗanda ta ɗauka a duk jiha, inda daga jihohin da suka fi samu akwai Kaduna, wadda matasanta guda 3,039 suka samu aiki.
Jihar Kano na da 2,000, babban birnin tarayya Abuja na da 1,708, Abia na da 395, Zamfara na da 2,000 da sauransu.
Yawan masu neman shiga aikin ya nuna cewa aikin soja har yanzu yana da matuƙar jan hankali ga matasa saboda, duk kuwa da matsalolin da ake gani yana tattare da aikin.
A ɓangaren aikin sojin sama kuwa, rundunar ce aƙalla matasa 20,000 ne suka rubuta jarabawar neman shiga aiki a cibiyoyi daban-daban na ƙasar.
Me ya sa ake rububin shiga aikin?
Yawan masu neman aikin shiga aikin ɗamara musamman na ƴansanda da soja na da alaƙa da matsalar rashin aikin yi a Najeriya.
Ga matasa da dama a Najeriya - ƙasar da ake fama da yawaitar marasa aikin yi - shiga aikin tsaro na ba da abin da ke da wahalar samu a wasu ɓangarori da dama, misali tsayayyen albashi da tabbacin aiki da kuma fansho da damar samun ci gaba a rayuwa.
Haka kuma a Najeriya, masu takardar kammala sakandare kaɗai suna wahalar samun aikin gwamnati, wanda hakan ya sa aikin ɗamara ya zama kusan shi ne mafi kusanci ga matasan ƙasar waɗanda ba su samu damar zuwa makarantar gaba da sakandare ba.
Da yake sharhi kan al'amarin, Dr Kabiru Adamu, mai sharhi kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Security and Consulting, ya ce bayan neman tabbacin da matasan ke yi, aikin ɗamara yana ba wasu da dama sha'awa.
Ya ce aikin tsaro yana da matuƙar muhimmanci ga ƙasar, sannan yana samar da matsayi da ɗaukaka ga matasan.
"Na farko dai aikin tsaro aiki ne da ke da muhimmanci kuma yana da sha'awa, sannan yana ba mutum ɗaukaka da fice ga kuma samun biyan buƙata. A taƙaice wannan ya sa matasan suke da sha'awar son shiga," in ji Dr Kabiru.
Shugaban na kamfanin Beacon, ya ƙara da cewa aikin ɗamara ne aikin da ya fi tabbaci.
"Da zarar an ɗauke ka aiki, idan ba wani babban laifi ka yi ba, sai ka yi aikinka har ƙarshe wanda aiki ne na shekara 35, wanda za ka yi ana biyanka ana ɗaukar nauyinka da kai ka horo da sauransu."
Kabiru Adamu ya ƙara da cewa darajar da ke cikin aiki na ƙara jan hankalin mutane, domin "duk inda ka je, za ka ga ana girmama ka sosai ana mutunta ka saboda aikin da kake yi na jami'in tsaro."
Sai dai masanin tsaron ya ce an fara samun matsala wajen neman shiga aikin, inda a cewarsa aka fara samun koma-baya wajen sha'awar shiga aiki daga wasu yankunan ƙasar, musamman "yankin kudu maso gabas," in ji shi.