Amurka na neman yaƙi ya ƙazance - Iran
Iran ta soki lamirin Amurka kan hare-haren da ta kai tare da haɗin gwiwar Saudiyya a ƙasar Iraqi, inda Iran din ta ce wani mataki ne na faɗaɗa rikicin da ake fama da shi a yankin.
Iran ta yi wannan suka ne bayan wata ƙungiya mai goyon bayan Iran da ke samun mafaka a Iraqi ta ce an kashe mambobinta aƙalla 20 sanadiyyar hare-haren da Amurka da Saudiyya suka kai a cikin dare.
Hare-haren da aka kai wa ƙungiyar na zuwa ne bayan Iran ta ce ta kai hari da makamai masu linzami kan wani sansanin sojin Amurka da ke Jordan.
Amurka ta ce ta kakkaɓo makaman.