INEC na aikinta yadda ya kamata babu son kai - Tinubu

Asalin hoton, Fadar Shugaban kasa
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa hukumar zaɓen ƙasar, INEC ba ta nuna son kai a yadda take gudanar da ayyukanta.
A baya-bayan nan INEC na fuskantar zarge-zargen nuna son kai a ayyukanta, musamman wasu matakai da take ɗauka, inda har wasu ke kiraye-kirayen shugaban hukumar ya sauka daga muƙaminsa.
Jam'iyyun adawar ƙasar sun sha zargin INEC da mara wa jam'iyyar APC mai mulki baya a matakan da take ɗauka.
To sai dai da yake jawabi yayin da yake karɓar jagororin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Archbishop Matthew Ndagoso, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Talata, Tinubu ya ce INEC na gudanar da ayyukanta bisa doron doka.
" INEC ba ta nuna son kai, ba ta taɓa tsoratar da kowa ba, idan ƴan adawa na ƙorafin, watakila suna zargin kansu ne da kuma rashin shrin da suka yi'', in ji shi.

















