Me ya sa ƴan bindiga suka fara kai wa alƙalai hari a Najeriya?

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A cikin ƙasa da mako guda, ƴan bindiga sun kai wa alƙalai biyu hari a arewacin Najeriya. Ɗaya an yi garkuwa da shi, yayin da ɗayan ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu masu ɗauke da makamai suka kutsa cikin kotun da ya ke shari'a.

A ranar 26 ga watan Yuli, wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Faruku Hassan, a ƙaramar hukumar Bunza. Rahotanni sun ce masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 200.

Bayan 'yan kwanaki kaɗan, wasu ƴan bindiga ne suka mamaye kotun Shari'a da ke ƙauyen Gwarjo a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina, inda suka riƙa harbe-harbe tare da tambayar "ina Alƙali Mohammed Muktar yake".

Sai dai ya tsalleke rijiya da baya, inda aka ce ya samu ya tsere wa maharan bayan ya hango maharan tun suna tahowa daga nesa, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga

Wani ganau ya ce bayan maharan sun gano cewa alƙalin ya tsere, sun fusata tare da yin barazanar "kashe shi idan ya sake dawowa gudanar da shari'a" a wannan kotun.

Waɗannan hare-hare na ɗiga ayar tambaya kan ko alƙalai sun zama sabon abin da ƴan bindiga ke kai wa hari. To amma me hakan ke nufi ga tsarin shari'a da tsaron masu gudanar da ita?

Me ya sa ƴan bindiga ke kai wa alƙalai hari?

Masana harkokin tsaro na ganin hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa alƙalai ba wai don neman kuɗin fansa kaɗai ake yi ba.

A cewarsu, irin waɗannan hare-hare na iya kasancewa wata dabara ta razana masu gudanar da shari'a, tare da isar musu da saƙon tsoro domin su kasa gudanar da aikinsu cikin 'yanci.

Masanin harkokin tsaro, Dakta Kabiru Adamu, ya ce akwai yiwuwar ƴan bindiga na ƙoƙarin hana alƙalai gudanar da shari'o'in da suka shafe su ko kuma gurfanar da mambobinsu idan jami'an tsaro suka kama su.

"Akwai yiwuwar ƴan bindiga na ƙoƙarin isar da saƙo ga alƙalai domin su ji tsoro. Kai hari kan alƙalai na iya kasancewa wata hanya ta ɗaukar fansa kan hukunce-hukuncen shari'a.," in Kabiru Adamu

Dakta Kabiru ya ce sace-sacen alƙalai da sauran ma'aikatan shari'a a arewacin Najeriya na da dalilai masu yawa, amma ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne fahimtar cewa hakan na nuna irin yadda matsalar tsaro ta ƙara tsananta a wasu jihohin yankin.

Ko akwai abin da suke nema?

Ya ce neman kuɗin fansa na daga cikin manyan dalilan da ke sa masu garkuwa da mutane su kai hari kan manyan mutane, ciki har da alƙalai.

Alal misali, sace Mai Shari'a Faruku Hassan a jihar Kebbi, inda aka ruwaito cewa masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa har naira miliyan 200.

Sai dai ya ce ba kuɗin fansa kaɗai ke jawo irin waɗannan hare-hare ba. A cewarsa, rashin isasshen tsaro a gidajen alƙalai da kuma kotuna, musamman a yankunan karkara, na ƙara ba masu aikata laifuka damar kai hare-hare cikin sauƙi.

Ya kuma bayyana cewa rashin cafke masu laifi ko hukunta su yadda ya kamata a lokuta da dama na ƙara musu ƙarfin guiwa, har su ci gaba da kai hare-hare ba tare da tsoron sakamakon abin da suke aikatawa ba.

Masanin ya ƙara da cewa yawaitar makamai a hannun masu aikata laifuka, da kwararowar ƙungiyoyin 'yan ta'adda da sauran masu laifi zuwa wasu jihohin arewacin Najeriya, na daga cikin abubuwan da suka ƙara ta'azzara matsalar.

A cewarsa, wani abin damuwa kuma shi ne gibin da ke tsakanin al'umma da jami'an tsaro, musamman 'yan sanda. Ya ce hakan na sa masu aikata laifuka su gudanar da ayyukansu cikin sauƙi saboda ba sa fuskantar saurin gano su ko samun bayanan sirri da za su taimaka wajen cafke su.

Me ya kamata yi domin dakile hare-hare kan alƙalai?

A cewar Dakta Kabiru Adamu, daƙile hare-haren da ake kai wa alƙalai da sauran manyan jami'an gwamnati na buƙatar ɗaukar matakai a fannoni da dama, ba wai ta fuskar amfani da jami'an tsaro kaɗai ba.

Ya ce mataki na farko shi ne ƙarfafa tsaro a matakin ƙauyuka da al'umma, musamman a yankunan karkara da hare-haren 'yan bindiga suka fi ƙamari. A ganinsa, ƙarin jami'an tsaro a irin waɗannan yankuna zai taimaka wajen hana masu aikata laifuka samun damar kai hare-hare cikin sauƙi.

Ya kuma ce akwai buƙatar a ƙara tsaurara tsaron gidajen alƙalai da harabar kotuna ta hanyar samar da isassun jami'an tsaro da kuma amfani da na'urorin sa ido kamar kyamarori, domin rage haɗarin kai musu farmaki.

Masanin ya ce inganta tattara bayanan sirri na daga cikin muhimman matakan da za su bai wa hukumomin tsaro damar gano shirye-shiryen 'yan bindiga tun kafin su kai hari.

"Idan aka samu ingantattun bayanan sirri, za a iya dakile hare-hare tun kafin su faru."

Ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen dakile yawaitar makamai marasa lasisi ta hanyar toshe hanyoyin da ake shigar da su cikin ƙasar, domin a cewarsa waɗannan makamai ne ke ƙara bai wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka ƙarfin kai hare-hare.

Har ila yau, Dakta Kabiru ya ce hukunta masu aikata laifuka cikin gaggawa na da matuƙar muhimmanci, domin hakan zai rage musu ƙarfin guiwar ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin al'umma da hukumomin tsaro.

"Ba jami'an tsaro kaɗai za su iya magance wannan matsala ba. Dole ne al'umma su kasance abokan hulɗa wajen samar da bayanai da kare yankunansu."

Masanin ya ce baya ga matakan tsaro, akwai buƙatar gwamnati ta inganta tattalin arziki a yankunan da matsalar ta fi ƙamari, musamman ta hanyar samar wa matasa ayyukan yi da hanyoyin samun abin dogaro, domin rage yawan masu shiga cikin ayyukan ta'addanci da sauran laifuka sakamakon rashin aikin yi.