Dubban baƙin-haure sun tsallaka Spain ta Morocco
Dubban ƙarin baƙin haure sun taru a kan bakin iyakar Ceuta, yankin Sifaniya da ke Arewacin Afirka, bayan da yankin ya fuskanci gagarumar kwararar masu shiga ƙasar a jiya Alhamis, karo na farko cikin shekara biyar.
Gwamnatin Sifaniya ta tura karin sojoji domin taimakawa wajen shawo kan lamarin, yayin da ake sa ran Firaminista Pedro Sánchez zai kai ziyara yankin na Ceuta a yau Juma'a.
Rahotanni sun ce hukumomin Maroko sun fara ɗaukar tsauraran matakai kan bakin hauren, inda a daren da ya gabata suka rika fesa wa bakin ruwa domin tarwatsa su.
Sifaniya ta ce ta cimma yarjejeniya da Maroko domin mayar da bakin hauren zuwa ƙasarsu cikin gaggawa.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin Maroko a kan batun. Jami'ai a Ceuta sun ce aƙalla mutum 15 sun mutu bayan da suka nutse a teku yayin da suke ƙoƙarin isa yankin na Sifaniya.