KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 31 ga watan Yulin 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello

  1. Kotu ta ba ƴansanda izinin binciken ɗan shugaban ƙasar

    Brazil

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani alƙalin Kotun Koli ta Brazil ya bayar da izini ga ƴansanda su gudanar da binciken kan Fabio Lula da Silva, babban ɗan Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva, bayan an danganta shi da wata badaƙalar zamba da ta shafi maƙudan kuɗaɗe.

    Ana zargin Fabio, wanda aka fi sani da Lulinha, da taimaka wa wani mai rajin neman tasiri a harkokin gwamnati da ke zaman kurkuku a yanzu, a mu'amalolinsa da Ma'aikatar Lafiya ta Brazil dangane da kasuwancin tabar wiwi da ake amfani da ita wajen magani.

    Mutumin da ake magana a kansa an same shi da laifin damfarar ƴan fansho a wata shari'a ta daban a bara, kuma tuni an taɓa binciken Lulinha dangane da wannan batu.

    Lauyoyin Fabio Lula da Silva sun shaida wa kafafen yaɗa labarai na Brazil cewa ba za su iya yin tsokaci kan sabon binciken ba, domin har yanzu ba su ga cikakkun bayanansa ba.

    Shugaba Lula ya sha alwashin cewa ba za a nuna sani ko sabo ba a kan dan nasa.

  2. Hamas ta amince ta ajiye makami a Gaza bayan tattaunawa da Trump

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayan tattaunawar wata da watanni, ƙungiyar Hamas ta ce ta amince da wani shiri da Hukumar Zaman Lafiya ta Shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar, na ta kwance damarar yaki gaba daya - ta ajiye makamanta a Zirin Gaza.

    Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban abin tarihi, yana mai cewa ta zama wani muhimmin mataki na samar da sabuwar gwamnatin Falasɗinawa a Gaza.

    Wakilin BBC a Gaza, wanda ke birnin Alkahira na Masar, ya ce shirin ya tanadi ƙididdige da adana manyan makaman Hamas da suka rage ƙarƙashin kulawar hukumomin Falasɗinawa.

    Wakiliyar BBC ta ce, zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba. Shugaba Trump dai ya ce dakarun Isra'ila za su fice daga Gaza da zarar an kammala kwance damarar Hamas da sauran ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai.

  3. Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'atu babbar rana.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.