Real Madrid ta kusan kammala cinikin Silva, Bayern Munich na son Rashford

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ana sa ran Real Madrid za ta kammala cinikin siyan dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, bayan wa'adin kwantaraginsa ya zo karshe a Manchester City a karshen watan da mu ke ciki yayin da Jose Mourinho zai koma aiki a matsayin kocin kungiyar.(Mail - subscription required), external

Bayern Munich nada kwarin gwiwar cewa za ta iya siyan dan wasan Manchester United da Ingila, Marcus Rashord, mai shekara 28, bayan tattaunawa mai kyau da wakilansa.(Teamtalk), external

Manchester United na da kwarin gwiwar daukar dan wasan Portugal da West Ham Mateus Fernandes, mai shekara 21, bayan ta sha gaban Arsenal wajan zawarcinsa. (Times -subscription required), external

Newcastle ta sake farfado da zawarcin da ta ke yi wa golan Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekara 23, a daidai lokacin da ta ke ci gaba da kokarin karfafa bangaren tsaron ragarta.(Athletic - subscription required), external

Arsenal na nazari kan dan wasan Real Sociedad da Sfaniya Ander Barrenetxea, wanda Tottenham ke son ta dauka. (Sun), external

Leeds da Liverpool dukkansu suna zawarcin dan wasan Midtjylland da Koriya ta Kudu Lee Han-beom, mai shekara 23, inda Napoli, da Monaco da kuma Lyon suna cikin kungiyoyin da suka sa ido kan dan wasan.(Teamtalk), external

Brighton da Hove Albion sun yi wa dan wasan Croatia da Tottenham, Luka Vuskovic, mai shekara 19, tayin fam miliyan 30 (Athletic - subscription required), external

Besiktas ta fara tattaunawa da dan wasan Arsenal Leandro Trossard, mai shekara 31, wanda ta ke son ta saya a kan fam miliyan 20. (Caught Offside, external)

Galatasaray na sha'awar dan wasan Aston Villa Emiliano Buendia, mai shekara 29, kuma ana ganin kungiyar za ta maye gurbinsa da Crysencio Summerville, mai shekara 24 na kungiyar West Ham. (Football Insider, external)

Barcelona za ta sayar da mai tsaron ragarta Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 34, ga Ajax. (Fichajes - in Spanish, external)