Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
United na son Hall, Madrid na harin Gvardiol
Manchester United na son ɗaukar ɗan wasan Newcastle da Ingila Lewis Hall, da ke son barin ƙungiyar. (Sun)
Haka kuma United ɗinna sa ido kan ɗan wasan Fulham da Amurka Antonee Robinson, a matsayin ɗan wasan da za su ɗauka a kaka mai zuwa. (Sky Sports)
Barcelona ba zata iya siyen ɗan wasan Portugal Bernardo Silva ba, saboda farashin sa da ɗawainiyar ɗan wasan, yayin da Atlentico Madrid da Real Madrid su kuma ke kokawar ɗaukar ɗan wasan idan kwantaraginsa ya ƙare da Manchester City a ƙarshen watan Yunin nan. (Marca in Spanish)
Da alama dai Real Madrid na dab da ɗaukar Silva kasancewar sun shiga mataki na gaba kan tattaunawa kan buƙatun ɗan wasan.(Fabrizio Romano)
Ɗan wasan Manchester City da Croatia Josko Gvardiol, ya shiga cikin jerin ƴan wasan da Jose Mourinho ke son ɗauka domin inganta tsaron bayan Real Madrid. (Teamtalk)
Tsohon mai horar da ƴan wasan Manchester United Ruben Amorim, na ɗaukar hankalin AC Milan, inda suke da ƙarfin yaƙinin cewar zai ƙara azamar ƙungiyar. (Fichajes in Spanish)
Barcelona sun shirya ƙin amincewa da ɗaukar ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford, kan fam miliyan 26, yayin da zamansa a ƙungiyar a matsayin ɗan wasan aro zai ƙare a ranar Litinin. (Daily Mirror)
Manchester United na iya ɗauko ɗan wasan Lens Mamodou Sangare, bayan da aka yi masa tayi, a madadin ɗan wasan NottinghamForest Elliot Anderson. (Teamtalk)
Ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Nico Schlotterbeck, na duba yiwuwar hakura da komawa Real Madrid domin mayar da hankali kan gasar cin cofin duniya.
Trabzonspor na son ganin sun ɗauke mai tsaron ragar Manchester United da Kamaru Andre Onana, a matsayin ɗan wasan din-din-din, a kakar nan. Mirror)
United na duba yiwuwar ɗauko mai tsaron ragar TurkiyaAltay Bayindir, da Czech Radek Vitek, da ke matsayin ɗan wasan aro a Bristol City a kakar bara. (Sky Sports)
Sunderland sun shiga cikin jerin masu son siyen ɗan wasan Bosina Kerim Alajbegovic, daga RB Salzburg. (Teamtalk)
Wloves na iya sake ɗauko ɗan wasan West Ham Pablo, inda sabon mai horar da ƙungiyar Cesar Piexoto, da ke aiki da dan wasan gaban Portugal Gil Vincente. (Football Insider)
Real Madird na duba yiwuwar bayar da ɗan wasan gaban Ajantina Franco Mastantuono, a matsayin ɗan wasan aro ga Juventus. (TuttoSport - in Italian)