Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Mahdi, yaushe zai bayyana kuma a ina?
- Marubuci, Usman MINJIBIR
- Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 10
Kusan ilahirin al'ummar Musulmin duniya sun yi imani cewa a ƙarshen zamani za a yi wani mutum bawan Allah mai suna Mahdi wanda zai yaƙi zalunci sannan ya tabbatar da adalci.
Sai dai kuma fahimtar wane ne Mahdi da kuma haihuwarsa sun kasance wasu abubuwa masu taƙaddama a tsakanin mazhabobi da ɗariƙu daban-daban.
Wannan ya sa a tarihi aka samu wasu mutane a baya da suka ayyana kansu a matsayin Mahdi to amma idan tafiya ta yi tafiya sai jama'a su fahimci al'amarin ba haka yake ba - duk da cewa dai rasuwar mai iƙrarin kasancewa Mahdi ba ta sauya wa wasu ra'ayi.
Wataƙila hakan ne ma ya sa wasu da suka haɗa da malami da waɗanda suka yi imani da zahiri ke da fahimtar cewa babu wani Mahdi da zai zo a ƙarshen zamani.
Domin sanin haƙiƙanin yadda al'amarin yake, BBC ta tattauna da malamai daga fahimta daban-daban ta addinin Musulunci domin sanin abin da kowane ɓangare ya yi imani da shi dangane da Mahdi.
A mazhabar Shi'a, Imam Mahdi kamar yadda mabiya mazhabar ke kiran sa, shi ne Imami na 12 a jerin Imaman da mabiya mazhabar suka yi amannar cewa su ne wakilan annabi Muhammad SAW a bayansa.
Yarda da Imamai shi ne ginshiƙin imani na huɗu a tsakanin mabiya mazhabar ta Shi'a, bayan Imani da Allah (Tauhid), Imani da adalcin Allah (Adl), Imani da annabta (Nubuwwa) da kuma imani da ranar lahira (Ma'ad).
Muhammad al-Mahdi kamar yadda sunansa yake ɗa ne ga Hassan al-Askari wato Imami na 11 da mabiya Shi'a suka yarda da su sannan sunan mahaifiyarsa Narjis Khatoon, wadda ƴa ce ga Sarkin daular Roma a lokacin.
An haifi Mahdi a shekaru 255 bayan Hijra wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Yulin shekarar 869 bayan annabi Isa.
"Abin da ya inganta a tarihi a duniyar Shi'a shi ne an haife shi a ranar 15 ga watan Sha'aban shekara ta 255 hijrar manzo SAWW," in ji Dakta Shu'aibu Muhammad Abdullahi, shugaban cibiyar nazarin kimiyyar addinin Musulunci ta Khatamul Anbiya Institute of Islamic Sciences da ke Kano.
To sai dai kasancewar akwai kashe-kashe tsakanin mabiya mazhabar ta Shi'a, inda ake da Shi'a Imamiyya (Ja'afariyya) da Zaidiyya da kuma Isma'iliyya, za mu duba irin fahimtar da kowane ɓangare ke da ita dangane da Mahdi.
Shi'a Imamiyya
Shi'a Imamiyya Ithna Ashariyya ko kuma wadda aka fi sani da Ja'afariyya ita ce fahimtar da ta ɗoru a kan makarantar Ja'afar al-Sadiq wanda shi ne Imami na shida a jerin Imamai 12 da suka yi imani da su.
Sun ƙudurce cewa dukkan Imamai 12 ciki har da Mahdi ma'sumai ne wato ba sa aikata saɓo sannan kuma zaɓaɓɓu ne da annabi SAW ya yi wasiyyarsu da sunayensu.
Mabiya wannan fahimta sun ƙudurce cewa yarda da Mahadi ginshiƙin imani ne. Sannan sun amince cewar an haifi Mahdi a zamanin shugabancin Al-Mu'tamid na daular Abbasiyya, a garin Samarra da ke ƙasar Iraq.
To sai dai sakamakon azabtarwar da basaraken ya yi wa mahaifinsa har ta kai ga kisa, sai shi Mahdi ya ɓace ko kuma ya ɓuya abin da ake kira da 'Gaybah' a lokacin yana ɗan shekara biyar.
- Ƙaramar ɓacewa (Gaybah al-Sughra): Ɓacewar da Mahdi ya yi a shekarar 250 bayan Hijra inda ya kwashe shekaru 69 ba tare da jama'a na ganin sa ba illa dai kawai ya bai wa wasu manyan mataimakansa guda huɗu saƙo su faɗa wa mabiya.
- Babbar ɓacewa (Gaybah al-Kubra): A shekarar 329 bayan Hijra ne Mahdi ya shiga babbar ɓacewa bayan rasuwar ɗaya daga cikin mabiyan nasa mai suna Ali ibn Muhammad al-Samari. Kafin rasuwarsa, al-Samari ya sanar da cewa wakilci ya ƙare kuma ba za a sake ganin Mahdi ba har sai lokacin bayyanarsa a gaba.
A ina Mahadi yake a yanzu haka?
Dangane da wurin da Mahdi yake, Dakta Shu'aibu ya ce:
"Za mu ce Allah ne ya bar wa kansa sanin wurin da yake. Ba duk abin da kenan ne ya zama dole mu san inda yake ba. Kowa ya san annabi Isa yana nan da rasa...Ƙur'ani ya ce Allah ne ya ɗauke shi zuwa gare shi. A ina yake a zaune? A wane wuri aka ajiye shi? Allah ne kawai ya bar wa kansa sani."
Sannan akwai ruwayoyi da ke nuna cewa wasu daga cikin waliyyan Allah suna nan da rai har ma suna halartar aikin hajji, irin su Kidr da Zhul Qarnain da sauransu. Za ka ga ruwayoyi sun kawo cewa suna nan da ransu amma a ina suke? Allah shi ya san a ina suke...to shi ma Imam Mahdi yana cikin waɗanda muke da yaƙinin yana cikin su," in ji Dakta Shu'aibu.
Wurin bayyanar Mahadi:
Mabiya wannan mazhabin na jingina ga manyan malamansu da ake kira da (Marja') ko kuma Maraji'ai domin samun shiriya har zuwa tsawon lokacin da Mahdin zai bayyana.
A yanzu haka dai mabiya mazhabar Shi'a Imamiyya suna zaman jiran bayyanar Mahdi a kowane lokaci, kuma sun yi amannar cewa Mahdi zai bayyana ne a birnin Makka kafin daga bisani annabi Isa ya bayyana.
"Akwai maganganu da dama kan wajen bayyanarsa amma abin da ya fi rinjaye shi ne wurin bayyanarsa zai kasance Makka mai daraja kuma a Ka'aba, inda zai tsaya tsakanin Maqami Ibrahim da Hajr al-Aswad... inda zai yi sallah raka'a huɗu..", in ji Dakta Shu'aibu Muhammad.
Yaushe zai bayyana?
"Babu lokacin tsayayye na bayyanar Imam Mahdi. A duk lokacin da Allah ya so zai bayyanar da shi, kamar yadda zai bayyar da annabi AS a lokacin da ya so. Ruwayoyin Musulmi Shi'a da Sunnah, ba su faɗi lokacin bayyanar Mahdi ba. Babu rana babu wata kuma babu shekara. Amma dai ruwaya ta nuna cewa zai bayyana ne a lokacin da zalunci ya kai ƙololuwa a duniya"
"Idan muka duba ruwayoyin da aka samu daga manzo (saww) a kan shi Imamul Mahdi za ka ji suna cewa Allah zai tayar da...to cewar za a tayar ya nuna samamme ne..ko kuma zai fito. Cewar zai fito shi ma ya nuna samamme ne. Da ba a haife shi cewa za a yi za a haife shi," in ji Dakta Shu'aibu Muhammad.
Salsalar Mahdi a Shi'a Imamiyya
- Muhammad bn Hassan (Imam al-Mahdi)
- Hassan ibn Ali al-Askari
- Ali ibn Muhammad al-hadi
- Muhammad ibn al-jawad
- Ali ibn Musa al-Ridha
- Musa ibn Ja'afar al-Kazim
- Ja'afar ibn Muhammad al-Sadiq
- Muhammad ibn Ali al-Baqir
- Ali ibn al-Husayn Zaynul al-Abideen
- Hussain bn Ali
- Ali ibn Abi Ɗalib (mijin Faɗima ƴar annabi Muhammad SAW)
Shi'a Zaidiyya
Mabiya wannan fahimta sun ɗoru ne a kan ginshiƙin imani da Imamai guda biyar maimakon 12 da ƴan Shi'a Imamiyya suka ƙudurce.
Zaidiyya ba su yarda cewa akwai wani bawan Allah da ke ɓoye da zai bayyana a ƙarshen duniya mai suna Mahdi ba. Kuma ba su yarda da ma'sumancin kowane Imami ba sannan kuma ba zaɓaɓɓu ba ne ba kamar yadda Imamiyya suka ƙudurce.
A fahimtarsu, Mahdi laƙabi ne ga duk wani jagora mai tsoron Allah daga jinin annabi SAW wanda ya jagoranci sauyi domin tabbatar da adalci a ban ƙasa.
Shi'a Isma'iliyya
Su ma mabiya Shi'a Isma'iliyya ba su amince da cewa Mahdi yana ɓoye ba. A wurinsu Mahdi na nufin duk wani Imami da ya zo a ƙarshen lokacinsa ya kuma samar da mafita ga addini.
Sun ƙudurce da imani da Imamai guda bakwai ba kamar Shi'a Imamiyya da Zaidiyya ba.
Shi'a Isma'iliyya su ne magoya bayan Isma'il bn Ja'afar wato ɗa ga Imami na 6 da Shi'a Imamiyya suka ƙudurce.
To sai dai maimakon yadda da Musal Kazeem wato Imami na 7 a wurin ƴan Shi'a Imamiyya, sai suka yi muba'a ga ɗan uwansa Isma'il bn Ja'afar.
Mahdi kamar dai yadda yake a Mazhabar Shi'a, su ma mabiya mazhabar Sunna sun yi imani da shi sai dai al'amarin ya sha bamban da na ƴan uwansu mabiya Shi'a.
Babban saɓanin fahimtar tsakanin Sunnah da Shi'a, shi ne haihuwar Mahdi, inda su mabiya Sunna suka tafi a kan cewa ba a haifi Mahdi ba amma za a haife shi ne a nan gaba.
"Tabbas Mahdi a Musulunce a wajen Ahlussunnah Wal Jama'a, suna ne na wani bawan Allah da manzon Allah SAWW ya yi busharar bayyanarsa wanda a cikin hadisai wasu a cikin ingantattun litattafai wasu kuma a cikin littafan da ba a nassanta ingancinsu ba amma hadisan sun inganta...idan aka tattara hadisan sun zo ta hanyar sahabbai daban-daban da tabbatar da batun..." in ji Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale, malamin addinin Musulunci a Kano.
To sai dai ita ma mazhabar Ahlussunnah Wal jama'a na da manyan rassa guda biyu wato na Salafiyya ko kuma Ahlussunnah da kuma Sufaye, inda ɓangarorin biyu suke da ƴar saɓanin fahimta dangane da haƙiƙanin wane ne Mahdi.
Mahdi a mahangar Salafiyya
Ahlussuna ko kuma Salafiyya wani ɓangare ne na fahimta a addinin Musulunci da baya ga bambancin fahimta da suke da shi da mabiya Shi'a a wasu rukunan addini, sun gina wakilcin annabi a kan halifanci inda suka ƙudure cewa bayan wafatin annabi halifanci ya koma hannun Sayyadina Abubakar sai Sayyadina Umar zuwa Sayyidina Usman sannan sai Sayyidina Aliyu.
Saɓanin mabiya mazhabar Shi'a da suka ce Mahdi zai kasance jinin jikan annabi Al-Hussaini, su kuma Ahlussunnah sun ce zai kasance jinin Al-Hassan ne.
"Sunansa Muhammdu ɗan Abdullahi ɗan wane....har sai an tiƙe da ɗan Hassan ɗan Aliyu ɗan Abu Ɗalib kenan tsatsaon Nana Faɗima Alaihassalam.
"Manzon Allah SAWW ya ce a ƙarshen zamani wani bawan Allah zai bayyana sunansa zai dace da sunana sunan mahaifinsa zai dace da sunan mahaifina. Zai cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta kafin nan da zalunci," in ji Sheikh Abubakar Abdussalam.
- Ina Mahdi yake?
Bisa fahimtar Ahlussunah, Mahdi ba wani mutum ne da aka taskace ba kuma ba a haife shi ba sannan bai ma san shi ne Mahdi ba da farko.
"A cikin wani hadisi na annabi SAW ya ce a cikin dare daya Allah zai shiryar da shi ya kuma kimtsa shi dama sunansa Mahdi wato wanda aka kimtsa aka shirya ya samu shiriya," in ji Sheikh Abdussalam.
- A ina zai bayyana?
"A wani hadisi, manzon Allah SAW ya bayyana cewa zai fito ta ɓangaren gabashin duniya kamar yankin Kurasan kenan sannan sai kuma ya tafi Madina daga nan kuma sai ya gudu daga Madina saboda tsoron ka da a kashe shi. Sai kuma ya dawo Makka. Daga nan kuma a ƙarshen bayyanarsa dai za a ji shi a Baitil Maqdis a daidai lokacin da Dujjal ya mamaye kusan mafi yawan yankunan Musulmai kuma yake barazanar kashe duk wanda bai yi imani da shi Dujjal ɗin ba."
"A lokacin ne kuma annabi Isa zai sauko daga wata farar hasumiyya da ake cewa a Dimashq wato Damascus ta Syria a yanzu daga nan zai tafi Baitil Maqdis inda zai tarar da Mahdi sun tayar da sallar Juma'a sai a ƙwanƙwasa musu ƙofa a ce wa Mahdi ga annabi Isa. Sai Mahdi ya ce da annabi Isa ya ja sallar sai annabi Isa ya ce a'a ai kai aka tayarwa da sallar saboda haka a bayanka zan yi sallah," in ji Sheikh Abubakar Abdussalam.
- Me zai faru idan Mahadi ya bayyana?
"Manzon Allah ya yi bayani cewa zai bayyana mabiyansa da tutoci baƙaƙe. Sannan annabi ya ce zai cika duniya da adalci. Sannan manzon Allah ya ce zai bayyana a cikin zuriyarsa ma'ana jikokin Nana Faɗima. Kuma a wasu hadisan da dukka malaman Ahlussunnah sun yarda da ingancinsu zai bayyana ne ta tsatson ɗan Nana ɗan Nana Faɗima Alhassan."
"Dalilai na hadisai ba su bayyana cewa zai zalunci kowa ba. Ba su bayyanawa cewa zai zubar da jini ba. Amma sun bayyana cewa zai cika duniya da adalci. Har mutane su fi son bauta wa Allah," in ji Sheikh Abubakar Abdussalam.
Mahdi a mahangar Sufaye
BBC ta tuntuɓi Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna, wanda kuma ya ce ra'ayoyin Sufaye sun kasu gida biyu.
"Wasu sun fahimci cewa an riga an haifi Imam Mahadi tun ranar 15 ga watan Sha'aban a shekarar 255 bayan hijra musamman masu bin mazhabar Shi'a. Amma waɗanda suke bin tafarkin Sunna sun tafi a kan fahimtar cewa nan gaba ne za a haifi Mahdi," in ji Sheikh Maraya.
Sai dai kuma Sheikh Maraya ya ce dukkannin Sufaye sun amince cewa shi Imamul Mahdi waliyyin Allah ne kuma walittaka za ta tuƙe ga Mahdi.
"Sufaye sun tafi a kan cewa sunansa zai zama sunan Manzon Allah ne SAW sannan sunan mahaifinsa Abdullahi,"
Sheikh Maraya ya ƙara da cewa a wurin mabiya Tijjaniyya, Imamul Mahdi ɗaya ne daga cikin ƴan ɗarikar ta Tijjaniyya
"Idan kuma ka ɗauko ɗarikar Tijjaniya wadda nake yi kuma ɗaya daga cikin ɗarikar Sufaye, Shehu Tijjani Radhiyallah Ta'ala Anhu ya faɗi cewa Al-Imamul Mahdi wato zai karɓi ɗarikar Tijjaniyya idan ya zo. Shehu Tijjani ya faɗi wannan a littafin Kashful Ijab na Sheikh Ahmad Sukhairin da kuma littafin Rimahu na Shehu Umarul Gadusi."
A ina Mahdi zai bayyana?
Sheikh Maraya ya ce wasu malamai sun ce zai bayyana a Madina ne.
"Amma za a yi masa mubaya'a a Ka'abah a masalalcin Makka tsakanin Rukunul Yamani da Maqami Ibrahim, a lokacin da zalunci ya bayyana a duniya. Sai ya zama shugaban duniya domin wanzar da adalci," in ji Sheikh Maraya.