Dabarun da Arsenal za ta iya amfani da su wajen lashe Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 11

Arsenal da koci Mikel Arteta na fatan ƙara ɗaukar kofi mai suna Champions League a karon farko, bayan lashe Premier League, inda za ta kara da Paris St Germain a wasan karshe ranar Asabar.

Arsenal ta yi fice a wasannin Turai ta hanyar mallakar ƙwallo da bani in baka da kuma rage damar bai wa abokan hamayya sararin cin ƙwallo. Hakan ya taimaka mata wajen yin wasa ba tare da ƙwallo ta shiga ragarta ba, mafi yawa a gasar kenan.

A gefe guda, PSG ta fi kowace kungiya cin ƙwallaye a wannan kakar a Champions League, inda ta zura 44 a raga, yayin da Arsenal ke da 29.

Sai dai PSG ta yi karawa biyar ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba, wanda ke nuna bambanci tsakanin masu tsare baya da raga tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Wannan ya sa wasan za a yi ne tsakanin masu cin kwallo da kuma masu hana cin cin kwallo.

Duk da haka, koci Mikel Arteta na fatan Arsenal za ta taka wasa mai ƙyau a gaba, tana matsawa PSG zuwa kusurwar filinsu, kamar yadda suka yi a wasu lokuta a zagayen daf da kusa da na karshe a kakar da ta gabata, duk da cewa sun yi rashin nasara a wancan matakin da PSG ta kai wasan karshe ta lashe Champions League a karon farko a tarihi.

Lamba 9 da ba a saba gani ba

Dabarar da Arsenal ta yi amfani da ita a kakar da ta gabata a wasan da ta yi da Paris Saint-Germain, duk da cewa ta yi rashin nasara, ta yi amfani da Mikel Merino a matsayin ɗan gaba wato lamba tara.

Paris Saint-Germain, wacce ta shahara wajen matsin lamba da tsarin bin mutum (man-to-man pressing), takan matsa gaba sosai yayin da Arsenal ke ƙoƙarin fara gina wasa daga baya.

Muhimmin ka'ida a tsarin wasan shi ne a samu wasu ƴan wasa da ba a tare su. Amma idan abokan hamayya suna yin man-to-man, samun wannan ɗan wasan da ba kowa a tare da shi ya kan zama da wahala sosai.

Lokacin da Merino ya sauko cikin tsakiyar fili, sai mai tsaron bayan PSG, Willian Pacho bai bi shi kai tsaye ba, domin hakan zai bar giɓi a bayan. Wannan ya sa PSG ta kara samun mai tsaron baya.

Sai dai hakan ya sa Arsenal ta samu fa'ida, domin ba tare da ɗan gaba ba wato lamba tara, yanzu tana da ƙarin ɗan wasan tsakiyar fili.

PSG kuma tana ƙoƙarin amfana da yanayin ta hanyar motsa ƴan wasanta na tsakiya tare da Merino, amma duk lokacin da suka yi hakan, wani ɗan wasan Arsenal zai kasance ya samu sarari, wanda ke taimaka musu wajen wucewa gaba da sauri kuma cikin sauƙi.

Duk da cewa ɗan wasan Sweden Viktor Gyökeres ya kammala kakar wasan bana cikin kykkyawan yanayi, Merino — wanda ya dawo daga jinya — da kuma Kai Havertz su ne ƴan wasan da suka fi dacewa da irin wannan dabara da salon.

A wasa da ƙungiyoyin da ke matsin lamba ta hanyar bin mutum (high man-to-man pressing), buga doguwar ƙwallo a sama ta wuce ƴan wasan gaba da na tsakiya na abokin hamayya ita ce dabara mai matuƙar amfani.

Arsenal na iya amfani da Mikel Merino da Kai Havertz wajen amfani da dogayen ƙwallaye da David Raya ke aikawa daga baya.

Bayan haka, ƴan wasan tsakiyar Arsenal sukan cushe tsakiyar fili wajen karɓar ƙwallo, wanda hakan ke ba su damar ci gaba da kai hari cikin sauri. Wannan wata dabara ce da za a dinga amfani da ita sosai a wasanninta.

Haka kuma, Viktor Gyökeres zai iya amfani da dogayen ƙwallaye ta hanyar fafatawa da ƴan bayan abokan hamayya a gefen fili, inda zai rika gudu a kan layukan gefe, domin ƙoƙarin haifar da barazana kai tsaye ga kariya.

Jarumtar riƙe ƙwallo da wasa a kankanin wuri

A kakar da ta gabata, Arsenal ta sha wahala wajen zura kwallo a ragar Paris Saint-Germain, saboda jarumtar mai tsaron raga Gianluigi Donnarumma.

Paris Saint-Germain ba ta yawan barin ƙwallo ta shiga raga a wannan kakar, amma ƙungiyoyi kamar Chelsea, RC Lens da Bayern Munich sun nuna cewa za a iya samun hanya idan aka kai hari mai kyau.

Dabarar da waɗannan ƙungiyoyi ke amfani da su shi ne salon ƴan wasa kusa da juna a tsakiyar fili. Wannan yana jawo Paris Saint-Germain da ƴan wasanta masu bin mutum su matsa gaba su kuma cunkushe tsakiyar fili.

Sakamakon haka, wasu sassan filin suna kasancewa a buɗe. Lokacin da aka fitar da ƙwallo daga irin wannan wurin mai cunkoso zuwa inda ba ƴan wasa sosai, hakan na taimakawa wajen karya tsaron bayan PSG, musamman a kai hari ta tsakiyar fili.

Arsenal a dabi'arta tana gujewa yin wasa mai hatsari a tsakiyar fili, ta fi son kai hari ta gefe da kuma yin jefa kwalli masu nisa, domin rasa ƙwallo a tsakiyar fili na iya jawo a je a zura mata ƙwallo cikin sauki.

Amma wannan wasan na iya zama abin da za su yi ƙarfin hali su gwada a wannan karon, saboda suna da ƴan wasa kamar Leandro Trossard, Kai Havertz, Bukayo Saka, Martin Zubimendi da Eberechi Eze da ke iya taka leda a kusa da juna a cikin matsin lamba.

Haka kuma, suna da ƴan wasan da za su iya hare-hare daga tsakiyar fili idan an samu damar buɗe masu tsare bayan PSG.

Dakatar da kai hare-haren PSG masu hadari

Khvicha Kvaratskhelia, wanda ɗan wasa ne mai ƙarfi da sauri kuma yana buga gefen hagu da kuma amfani da ƙafar dama, yana daga cikin ƴan wasan da suka fi hatsari a ƙwallon ƙafa, kuma Arsenal za ta bukaci ta dakile shi sosai.

Paris Saint-Germain a karkashin koci, Luis Enrique ƙungiya ce mai yawan sauya salo da motsi a fafatawa, amma tana bin wasu tsare-tsare na wasa da aka bayyana a nazarin dabara tun daga gurbin baya.

Suna da wasu wurare a filin wasa da suke ƙoƙarin mamayewa a kowane lokaci, ciki har da wuraren tsaron baya lamba biyar da shida, gefuna biyu na fili, da kuma matsayin ɗan gaba.

Sai dai ba wai muhimmin abu ba ne wanda ɗan wasa ke cike wannan wuri a kowane lokaci, domin suna yawan musayar gurabe tsakanin ƴan wasa daban-daban.

Wannan yawan sauyawa da jujjuyawa tsakanin ƴan wasa yana taimaka wa PSG karya lagon abokan hamayya, wanda ke haifar da gibi da kuma buɗe sarari don kai hari cikin sauƙi.

Khvicha Kvaratskhelia yawanci yana samun kansa a gefen hagu, inda yake motsowa ba tare da ƙwallo ba, kenan dole ake lura da shi sosai.

A wasan farko tsakanin Paris Saint-Germain da Bayern Munich, Desire Doue ya sauko daga layin gaba zuwa tsakiyar fili, wannan motsin ya kamata Arsenal ta kula da shi, idan ba haka ba sai a yi mata illa.

Saboda ɗan bayan Bayern Dayot Upamecano bai rufe shi sosai ba, Doue ya samu lokaci da sarari lailaya da ƙwallo a ƙafarsa.

A gefe guda, Kvaratskhelia ya fara yin motsi mai haɗari: wani lokacin sai ya nuna kamar zai yi gudu zuwa wajen masu tsaron baya, sannan ya tsaya ya dawo ƙasa, ya sake nuna kamar zai yi gudu, ya sake dawowa, kafin daga ƙarshe ya yi gudu zuwa gidan abokan hamayya.

Wadannan motsi sun rikitar da ɗan bayan gefen na Bayern Munich da ya sa ta kasa samun natsuwa.

Sakamakon haka, Doue ya aika wata ƙwallo zuwa masu tsaron bayan ƙungiyar Jamus, inda abokin wasansu ya yi gudu ya samu ƙwallon, sannan ya ci gaba da kai hari da ta kai ya zura ƙwallo a raga.

Idan Arsenal na son dakile Paris Saint-Germain, dole ne ta yanke shawara mai ƙarfi kan dabarar da za ta bi a irin wannan yanayi.

Za ta iya zaɓar ko dai ta tsaya kusa sosai da ƴan wasan da ke saukowa ƙasa domin ba su damar tsara wasan, ko kuma ta ja baya kaɗan, ta bar su da ƙwallo a wasu wurare amma ta rage tazara da ke bayanta domin hana su gudu zuwa gaba.

Bayan Arsenal ta fara cin ƙwallo 1-0 a wasan farko a kakar da ta gabata, koci Mikel Arteta ya gyara tsarin kare ƙwallon da suka ci. Daga baya ya bayyana cewa sun warware wata matsala cikin mintuna 15 zuwa 20, wanda ya canza yadda wasan ya gudana.

A wannan gyaran, ƙwazon Martin Odegaard ya karu a fafatawar, wanda ya sa PSG ta sha wahala wajen sarrafa tsakiyar fili kamar yadda ta saba.

Babban canji kuma shi ne yadda William Saliba ya ƙara matsa wa Ousmane Dembele, har ya rika bin sa kai tsaye (man-to-man) ko da Dembele ya sauka sosai zuwa bayan gidansu.

Wannan ya yi kama da abin da tsohon kocin Chelsea Enzo Maresca ya fada bayan nasararsu 3-0 kan PSG a FIFA Club World Cup, inda ya ce:

"Dole ne ka matsa musu sosai. Idan ka ba su lokaci ko sarari, za ka sha wahala. Man-to-man pressing shi ne mafita."

Wannan yana nuna cewa dakile PSG ba abu ne mai sauƙi ba, amma ana bukatar cikakken tsari, matsin lamba mai ƙarfi, da kuma yanke shawara mai sauri da ɗaukar matakan da suka dace a filin wasa.

Fenariti, bugun kusurwa da tazara ka iya sa a lashe kofin

Ba za ka iya rubuta game da yiwuwar Arsenal ta doke abokiyar hamayya kai tsaye ba tare da ambaton ɗaya daga cikin manyan hanyoyinta na cin ƙwallo a wannan kakar ba — wato set-pieces.

Paris Saint-Germain a kakar nan a zura mata ƙwallo 29 kacal a gasar lig, amma guda shida daga ciki sun fito ne daga set-pieces babu fenariti. Wannan ya nuna cewa akwai wani bangare da ke nuna rauni a tsarinsu, musamman idan aka zo batun ƙwarin tsaro baya a ƙwallon sama zuwa ragar PSG.

Thomas Frank da ƙungiyarsa Tottenham sun riga sun nuna cewa ana iya cutar da PSG ta wannan hanya. Duk da cewa PSG ta doke Spurs a Champions League a baya a kakar, Spurs sun ci ƙwallaye uku a wasan, ɗaya daga ciki daga bugun kusurwa. Har ila yau, sun kuma sun tashi 2-2 a UEFA Super Cup kafin daga bisani PSG ta yi nasara a bugun fenareti.

A karkashin Thomas Frank, Spurs sun yi amfani da wasu dabaru da suka yi kama da na Mikel Arteta, musamman wajen mai da set-pieces hanya mai ƙarfi ta kai hari.

A cikin dukkan kwallayen set-piece guda uku da suka ci, Spurs sun fi mayar da hankali zuwa gefen baya na raga, inda suke kai kwallon kai ta koma cikin da'irar PSG, ko abokin wasa zai samu damar zuwa ƙwallo kai tsaye a raga.

Arsenal ma ta fi ƙwarewa a wannan fanni, don haka idan ta samu damar shiga yankin PSG, ta tilasta musu bugun kusurwa ko na tazara, hakan zai iya zama babbar dama ta zura ƙwallo.

Duk da cewa babu wata dabara da za ta hana sa hazaka ko ƙwarewa ga ɗan wasa, akwai alamun cewa Arsenal na da hanyoyi masu ƙyau da za ta iya cutar da mai rike da Champions League mai fatan lashe kofin a bana.

Za mu kawo muku sharhi da bayanan wasan karshe a Champions League tsakanin Arsenal a Paris St German a kan shafin BBC Hausa tare da Mohammed Abdu.