Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya Wannan 30/05/2026

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Iran ta ce sake buɗe intanet ga jama'a mataki ne na kare haƙƙoƙinsu

    Mai magana da yawun gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta bayyana cewa matakin da gwamnati ta ɗauka na sake buɗe intanet na duniya ga jama'a ba kawai cire wata takunkumin fasaha ba ne, illa wani mataki ne na tabbatar da haƙƙoƙin al'umma.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, Mohajerani ta ce katse intanet din da aka yi a watannin baya ya samo asali ne daga barazanar tsaro da hare-haren abokan gaba da kuma yanayin da ya biyo bayan hakan.

    Ta ƙara da cewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa babu wani yanayi na musamman da zai zama dindindin.

    Bayan shafe watanni ana fama da katsewar intanet a Iran sakamakon yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila, an fara mayar da wasu ayyukan intanet a ƙasar kwanaki biyu da suka gabata.

    Tun da farko, gwamnatin Shugaba Masoud Pezeshkian ta yi kira sau da dama da a dawo da intanet, tana mai gargadin cewa katsewar na haifar da illa ga harkokin ilimi, tattalin arziki da kuma kasuwanci a ƙasar.

  2. Shugaban Amurka na cikin ƙoshin lafiya - Likitan Trump

    Likitan Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa shugaban na cikin ƙoshin lafiya kuma yana da cikakken ƙarfin da zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugabancin ƙasa.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Fadar White House ta fitar a ranar Juma'a.

    Dokta Sean Barbabella ya ce gwaje-gwajen lafiya da aka yi wa Trump a wannan makon sun nuna cewa har yanzu yana da ɗan kumburi kaɗan a ƙafafunsa da kuma wasu ƙananan tabo a hannuwansa, amma ba su da wata illa ga lafiyarsa.

    A cewar likitan, zuciyar Trump, huhunsa, tsarin jijiyoyinsa da kuma sauran sassan jikinsa suna aiki yadda ya kamata kuma cikin yanayi mai kyau.

    Ya ƙara da cewa shugaban yana da cikakken ƙarfi da lafiya domin ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayin shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Amurka.

    An gudanar da binciken lafiyar Trump na shekara-shekara ne a ranar 26 ga Mayu.

    Trump, wanda zai cika shekaru 80 a watan Yuni, shi ne mutum mafi tsufa da ya taɓa hawa kujerar shugaban ƙasar Amurka.

  3. Shugaban WHO ya kai ziyara yankin da cutar Ebola ta fi ƙamari a DR Congo

    Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, na ziyarar aiki a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo domin ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na daƙile yaduwar cutar Ebola.

    Bayan ganawa da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa a birnin Kinshasa, ya nufi lardin Ituri da ke gabashin ƙasar, wanda shi ne cibiyar barkewar cutar a halin yanzu.

    A yayin ziyarar, Dr Tedros zai duba halin da ake ciki a yankin tare da tattauna hanyoyin ƙara ƙaimi da daidaita ayyukan yaƙi da cutar tsakanin gwamnatin Kongo da ƙungiyoyin agaji na duniya.

    Ya bayyana cewa akwai ƙalubale da dama wajen shawo kan barkewar cutar, saboda Ebola cuta ce mai wuya, kuma babu rigakafin da aka amince da shi gaba ɗaya domin dakile ta.

    Haka kuma yankin da cutar ta bulla na fama da rikice-rikice da yawan mutanen da ke gudun hijira, lamarin da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar.

    Hukumar WHO ta ce an samu ci gaba wajen gwajin cutar da kuma isar da kayan aikin jinya zuwa yankin.

    Haka kuma ana ci gaba da gina cibiyoyin kula da masu cutar, sai dai hukumar ta ce har yanzu akwai aiki mai yawa da ya rage kafin a samu nasarar shawo kan barkewar Ebola gaba ɗaya.

  4. Cire tallafin mai ya ceci Najeriya daga durƙushewar tattalin arziƙi - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya ceci Najeriya daga fadawa cikin matsananciyar matsalar tattalin arziƙi, tare da shimfiɗa tubalin farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya karɓi bakuncin wasu gwamnoni da suka kai masa ziyarar taya murnar bikin babbar Sallah da kuma cika shekara uku da hawansa mulki.

    Ya ce duk da cewa cire tallafin ya jawo wa 'yan Najeriya ƙalubale da raɗaɗi, matakin ya zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewar kuɗaɗenta da kuma dawo da daidaito a tattalin arziki.

    Tinubu ya ce "tsawon shekaru Najeriya na kashe kuɗaɗe masu yawa wajen biyan tallafin man fetur wanda a cewarsa ya fi amfanar kaɗan daga cikin jama'a, yayin da muhimman fannoni kamar noma da ababen more rayuwa suka rasa jarin da suke buƙata. "

    Ya ƙara da cewa "tattalin arzikin ƙasar na nuna alamun farfaɗowa, inda noma da ayyukan gine-gine ke ci gaba da bunƙasa."

    Shugaban ya kuma yaba wa gwamnonin jihohi bisa haɗin kai da goyon bayan da suka ba gwamnatinsa wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

    Ya ce "a yanzu jihohi ba sa fama da matsalar neman tallafi daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi kamar yadda aka saba a baya."

    A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba wa jajircewar Tinubu wajen tinkarar matsalolin da ke tattare da tallafin mai, yana mai cewa shugaba ya nuna ƙarfin hali wajen ɗaukar matakan gyaran tattalin arzikin ƙasar.

  5. Har yanzu ba a kammala wata yarjejeniya ba da Amurka - Iran

    Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala wata yarjejeniya batsakanin Iran da Amurka ba.

    A wata hira da gidan talabijin na gwamnatin Iran, Baghaei ya ce Iran da Oman ne ke da ikon yanke hukunci kan yadda ake gudanar da harkokin mashigar Hormuz.

    Ya kuma ce a halin yanzu hankalin Iran ya karkata ne wajen kawo ƙarshen yaƙin da ake ciki, kuma babu wata tattaunawa da ake yi kan shirin nukiliyar ƙasar.

    Baghaei, wanda aka naɗa a matsayin mai magana da yawun tawagar masu tattaunawar Iran, ya ce kasashen Yamma ba za su iya yi wa Iran magana da salon umarni ba. Ya ce Iran tana yanke hukunci ne bisa muradun da haƙƙoƙin al'ummarta.

    Kalaman nasa sun zo ne bayan da Amurka ta fitar da wasu sharuɗɗan da ta ce dole Iran ta cika. Waɗannan sun haɗa da tabbatar da cewa Iran ba za ta mallaki makaman nukiliya ba, bude mashigar Hormuz ba tare da karɓar kuɗin wucewa ba da kawar da duk wasu nakiyoyi da ke cikin mashigar, da kuma cire tarin sinadarin uranium da Iran ta wadatar, tare da haɗin gwiwar Amurka da sa ido daga Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

  6. Assalamu alaikum

    Marabanku masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da ta tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta