Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ainihin abin da ya fara shiga tsakanina da Dikko Radda'
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin siyasa, Kabir Ibrahim Masari, wanda kuma makusanci ne ga shugaban ƙasar ya bayyana abin da ya fara janyo saɓani tsakaninsa da gwamnan Katsina Dikko Umar Radda.
An baya an samu rahotonnin saɓani tsakanin manyan jiga-jigan siyasar biyu, lamarin da ya kai ga kama manyan jami'an tsaron lafiyar gwamnan.
Duka Masari da Gwamna Dikko ƴan jam'iyyar APC mai mulki ne a ƙasar, wani abu da wasu ke ganin saɓanin nasu ka iya janyo wa jam'iyyar koma-baya a jihar.
Mutane da dama dai sun jima suna mamakin abin da ya shiga tsakanin manyan jagororin siyasar jihar.
A hirarsa da BBC, Ibrahim Kabir Masara ya bayyana ainihin abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da gwamnan.
'Matsalar ta fara ne kan shugaba Tinubu'
Ibrahim Masari, wanda makusanci ne ga Shugaba Tinubu ya ce matsala tsakaninsa da Gwamna Dikko ta faro ne daga zargin rashin son tallata Tinubu a jihar.
''Matsalar ta faro ne daga yaran gwamnan da waɗanda ke aiki da shi, waɗanda ke kafa allunan hotunan tallata gwamnan da yaransa ba tare da saka hotunan shugaban ƙasa ba'', in ji shi.
Masara ya ƙara da cewa hakan bai yi masa daɗi ba shi da wasu ƴansiyasar Katsinan da ke aiki a Abuja, inda suka fara ɗaukar matakin magance hakan.
''Hakan ya sa muka zo ni da Minista da Mallam Jabiru Tsauri waɗanda dukkanmu ma'aikatan shugaban ƙasa ne muka haɗa kuɗi muka yi manyan alluna ɗauke da hotunan Tinubu, muka saka'', in ji shi.
Babban hadimin an Shugaba Tinubu ya ce a jikin allunan da suka kafa sun saka hoton Tinubu da Kashim Dikko da na tsoffin gwamnonin Katsina biyu, Aminu Bello Masari da Shehu Shema.
Ya ce sauran sun haɗa da nasa da na Muttaƙa Rabe da Jabiru.
'Yaga hotunan Tinubu'
Ibrahim Masari ya zargi jami'an da ke tsaron lafiyar gwamnan Katsina da jagorantar yaga hotunan Tinubu da ke jikin allunan.
''Sai ya kasance ko da sanin gwamna ko ba saninsa babban dogarinsa da CSO ɗinsa suka jagoranci ƴanbanga da suka yi ta yanke hotunan shugaban ƙasa da ke jikin allunan tallen'', in ji shi.
Masari ya ce bai yarda a ce a jihar Katsina ba za a iya tallata Shugaba Tinubu ba.
''Ba a halicci ɗan'adam ɗin da zai ce ba za a iya tallata Tinubu a jihar Katsina ba'', kamar yadda ya bayyana.
'Ban yi nadamar taimaka wa Dikko ba'
Wasu na ganin saɓanin zai sa Masari ya janye goyon bayansa ga Gwamna Dikko a zaɓen 2027.
Sai dai Ibrahim Masari ya ce ba haka lamarin yake ba, hasalima ba ya nadamar taimaka masa a baya.
''Ban yi nadamar taimaka wa da yake bai wa Dikko Radda ya zama gwamnan jihar Katsina ba'', in ji Ibrahim Masari.
Ibrahim Masara ya ce ba shi da saɓani da gwamnan Katsina.
''Sai dai idan shi gwamnan ne yake da saɓani da ni'', in ji shi.
'Ko maƙiyin Dikko ya san ya yi aiki'
Sai dai makusancin na shugaba Tinubu ya yaba wa ayyukan da ya ce Gwamna Dikko ya yi a jihar Katsina a tsawon mulkinsa.
''Ai ko wanda ba ya ƙaunan Dikko ya san ya yi aiki a jihar Katsina'', in ji shi.