Ta yaya Rasha ke cin moriyar yaƙin Iran?

    • Marubuci, Monitoring Section
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Rasha ta samu wasu fa'idodi kai tsaye da kuma na kaikaice daga yaƙin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar a watan Fabrairu kan ƙawarta Iran.

Yayin da Amurka ke ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran, Rasha na cin moriyar ƙarin kuɗaɗen shiga sakamakon tashin farashin mai, da kuma shagaltuwar ƙasashen da take hamayya da su da wasu rikice-rikice. Haka kuma, tana amfani da wannan dama wajen faɗaɗa tasirinta a tattalin arzikin Iran.

A matakin tattalin arziki, waɗannan fa'idodin sun yi kama da waɗanda Rasha ta samu daga rikicin Yemen, inda ta ci moriyar tashin farashin mai da kuma shagaltuwar Amurka da wani rikici daban.

Sai dai a batun Iran, Rasha na kuma faɗaɗa kasancewarta a kasuwannin makamashin ƙasar da rikicin ya raunana, tare da ƙarfafa matsayinta ta hanyar samar da iskar gas ga arewacin Iran, yankin da a wasu lokutan ke fuskantar ƙarancin iskar gas a lokacin hunturu.

An samu gagarumar ƙaruwa a zirga-zirgar jiragen ruwa a tekun Caspian tun tsakiyar shekarar 2026, lokacin da Amurka ta toshe tashoshin jiragen ruwa na kudancin Iran, yayin da hare-haren Ukraine suka kusan dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin Rasha da ke tekun Azov da Bahar Maliya.

Tekun Caspian na samar da wata hanya da Rasha ke bi wajen jigilar kayan aikin soji da kayayyakin gyara zuwa Iran.

Haka kuma, Iran na ƙara sayen hatsi daga Rasha, matakin da ya taimaka wajen rage matsin lambar da masu noman hatsi na Rasha ke fuskanta sakamakon matsalolin jigilar kayayyaki.

Shin Rasha na ƙara faɗaɗa tasirinta a Iran?

"An tilasta wa Tehran ƙara komawa ga Rasha domin neman ƙarin tallafi da faɗaɗa haɗin gwiwa tsakaninsu," in ji Nikita Samagin, wani mai bincike kan al'amuran Iran, a cikin wani sharhi da ya wallafa a ranar 26 ga Oktoba a kafar yaɗa labarai ta Voznesenie Istorii, wadda ke gudun hijira daga ƙasarta.

Ya ƙara da cewa "Saboda haka, ayyukan da Rasha ke gudanarwa a Iran ba su da wani armashi sosai ta fuskar ribar tattalin arziki, amma fadar Kremlin na zuba jari a ƙasar ne domin ƙara faɗaɗa tasirinta na siyasa a yankin."

Samagin ya lura cewa Iran na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ƙasashe ƙalilan kamfanonin Rasha ke gudanar da manyan ayyukan makamashi, ciki har da tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya ta Bushehr.

Sai dai Rasha ta sha fuskantar matsaloli a baya wajen karɓo kuɗaɗen da Iran ke bin ta bashi, ciki har da kuɗaɗen da aka kashe wajen gina tashar nukiliyar ta Bushehr.

Ya ce yayin da matsalolin tattalin arzikin Iran ke ƙara ta'azzara, akwai yiwuwar bashin da ƙasar ke bin wasu ya ƙaru. A sakamakon haka, "ko dai dangantakar ƙasashen biyu za ta ci gaba da faɗaɗa, amma a kan kuɗin Rasha, ko kuma a tilasta watsi da mafi yawan waɗannan ayyuka."

A cewar Samagin, "kusancin dangantakar Rasha da Iran a 'yan shekarun nan ya samo asali ne kusan gaba ɗaya daga ware ƙasashen biyu da aka yi a idon duniya, lamarin da ya tilasta musu ƙara haɗin gwiwa da juna."

A ganinsa, yaƙin, da killacewar da manazarcin ya ce Amurka ce ta jagoranci aiwatarwa, tare da tabarbarewar dangantakar Iran da wasu ƙasashen maƙwabta, ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun ƙara rage zaɓuɓɓukan da Tehran ke da su.

What do Russian officials say?

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ƙasarsa na da kyakkyawar alaƙar haɗin gwiwa da Iran. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, a ranar 27 ga Oktoba, inda ya ce yawan cinikayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya ƙaru da kashi 10.4 cikin 100 tsakanin watan Janairu da Agusta.

A wata ganawa da ya yi a baya da takwaransa na Iran a ranar 1 ga Satumba, Putin ya ce: "Rasha na tare da al'ummar Iran baki ɗaya. Muna yaba wa jarumtaka da juriyarku wajen kare muradun ƙasarku."

Ya ƙara da cewa Rasha na bai wa Iran "goyon bayan da take buƙata", tare da samar mata da "kayayyaki da muhimman abubuwan buƙata".

Mataimakin shugaban kwamitin tsaron ƙasar Rasha, Dmitry Medvedev, shi ma ya bayyana a baya-bayan nan cewa dangantakar Rasha da Iran ta ƙara kusanta fiye da kowane lokaci, kuma yawan cinikayyar da ke tsakaninsu na ci gaba da ƙaruwa.

A cewar jaridar tattalin arziki ta Vedomosti, Medvedev ya ce yawan cinikayyar ƙasashen biyu zai ƙaru da kusan kashi 20 cikin 100 a shekarar 2025, kuma yana ci gaba da haɓaka duk da matsalolin da ake fuskanta.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya bayyana yayin ziyarar da ya kai Tehran a ranar 19 ga Oktoba cewa Rasha ta "samar da agajin jin ƙai ga al'ummar Iran da take ƙawance da ita".

Ya kuma ce Rasha ba ta da niyyar janyewa daga aiwatar da yarjejeniyoyin tattalin arziki da zuba jari da ta ƙulla da Iran.

Lavrov ya ƙara da cewa "A Majalisar Ɗinkin Duniya, mun dakile ƙoƙarin da ake yi na halatta matakan da ba su dace da doka ba, da kuma hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran."

Ya kuma yi kira da a "maido da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa" a mashigar ruwan Hormuz.

Shin Rasha na bai wa Iran tallafin soji?

Wata masaniya mai suna Yulia Roknifred ta rubuta a shafin wata kafar sadarwa da ke wallafa bayanai da harshen Rashanci cewa, sabanin ƙasashen Yamma, Rasha "ba ta ganin buƙatar bayyana wa duniya irin taimakon da take bai wa ƙawayenta, don haka mai yiwuwa ba za mu ji komai game da hakan ba."

A cikin wani rubutu da ta wallafa a ranar 16 ga Oktoba, ta ce "Ni kaina ina ganin akwai yiwuwar Rasha ta raba wa Iran bayanan da ta samu daga ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa na Gran."

Gran wani jirgin yaƙi ne marar matuƙi da Rasha ta ƙera bisa fasahar jirgin Shahed da Iran ta ƙera.

Roknifred ta rubuta cewa "ƙawayen da ke taimakawa a ɓoye" na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da ke ƙarfafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ta ƙara da cewa Rasha da China na kallon wannan a matsayin wata hanya mafi ƙarancin haɗari ta tunkarar Amurka, maimakon yin barazanar amfani da makaman nukiliya.

Shi kuwa Samagin ya ce Rasha na jigilar makamai zuwa Iran ta tekun Caspian, "musamman kayayyakin haɗa jiragen yaƙi marasa matuƙi da makamai masu linzami na Iran."

Sai dai ya ƙara da cewa Rasha za ta iya bayar da "taimako kaɗan ne kawai", saboda ba ta son ɓata dangantakarta da sauran ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya, sannan kuma galibin ƙarfin sojinta na ci gaba da kasancewa cikin yaƙin mamayar da take yi a Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito a ranar 27 ga Oktoba cewa Rasha ta bai wa Iran bayanan sirri da ta samu ta tauraron ɗan Adam tsakanin watan Yuli da Oktoba. Iran kuma ta raba waɗannan bayanai da ƙawayenta, ciki har da ƙungiyoyin mayaƙan da ke Iraq da kuma 'yan Houthi na Yemen, domin taimaka musu wajen kai hare-hare kan wurare a Saudiyya.

Shin Iran za ta iya zama cibiyar jigilar kayayyaki ta Rasha zuwa wasu ƙasashe?

Samagin ya kuma bayyana cewa Rasha na iya amfani da Iran a matsayin cibiyar jigilar kayayyaki zuwa kasuwannin duniya.

A cewarsa, ƙara yawan cinikayya ta hanyar tekun Caspian na iya kasancewa wani ɓangare na dabarar da ake bi wajen aiwatar da shirin hanyar jigilar kayayyaki ta Arewa zuwa Kudu (North-South Transit Corridor). Wannan hanya ta taso ne daga Rasha, ta ratsa tekun Caspian da yankin Kudancin Caucasus, zuwa Iran da kuma tekun Fasha.

Sauran shirye-shiryen sun haɗa da kafa cibiyar rarraba iskar gas, inda za a riƙa jigilar iskar gas daga Rasha ta bututun da ke ratsa Azerbaijan, kafin a aika da ita zuwa wasu ƙasashe daga tashoshin jiragen ruwa na kudancin Iran.

Wata dabarar kuma ita ce kafa cibiyar hatsi, domin sayar da hatsin Rasha ga ƙasashe irin su Iraq, Afghanistan da Pakistan.

Samagin ya ce: "Manufar mayar da Iran cibiyar jigilar kayayyaki ta Rasha ta samo asali ne daga tunanin cewa Tehran ba za ta mayar da martani ga matsin lambar ƙasashen Yamma ba, saboda ta daɗe tana fuskantar takunkumi."

Sai dai, muddin Iran na ci gaba da yaƙi da Amurka da Isra'ila, aiwatar da irin waɗannan tsare-tsare zai ci gaba da kasancewa abu mai wuya.