Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool da Chealsea na zawarcin Camara, Barcelona ta fasa ɗauko van Dijk da Fernandes
Liverpool ce kan gaba wajen son ɗauko ɗan wasan Monaco Lamine Camara, sai dai Chelsea ba ta kai ga fitar da rai ba a zawarcin sa ba. (Caught Offside)
Hansi Flick na Barcelona ya yi watsi da shirinsuna ɗauko ɗan wasan Liverpool Virgil van Dijk, da takwaransa na Manchester United Bruno Fernandes, saboda shekarunsu. (El Nacional - in Catalan)
Chelsea na harin Jules Kounde da ke son barin Barcelona a watan Janairu, bayan da ɗan wasa ya buga wasannin uku a kawai a gasar La Liga a wannan kaka. (Football Insider)
Declan Rice, ya amicen da tsawaita kwantaraginsa zamansa a Arsenal ta fatar baki. (Sky Sports)
Rice zai kasance ɗan wasan da ya fi kowa ɗaukar kuɗi a Arsenal inda albashinsa ya ƙaru da fam miliyan dubu ɗari uku a wata.(Guardian)
Manchester United da Barcelona ne kan gaba a zawarcin ɗan wasan Valerenga Gabriel Rajkovic. (Teamtalk)
Tsohon dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, na atisaye da ƙungiyarsa tun bayan da kwantaraginsa da Galatasaray ta ƙare a kakar wasannin da , inda ake tunanin zai iya komawa ƙungiyar ta Eagles. (Talksport)
Sunderland na harin tsohon ɗan wasan Bournemouth da Newcastle loyd Kelly, yayin da ya ke kokawar shiga cikin ƴan sha ɗayan farkon da ke bugawa Juventus.(Chronicle)
Mai horar da ƴan wasan Arjantina Lionel Scaloni ya bayyana cewar Lionel Messi zai iya komawa ƙungiyar a matsayin daya daga cikin tawagar masu horar da ƴan wasan, bayan da yayi ritaya da bugawa ƙasarsa wasa. (TNT Sports)
Makomar Michael Keane na cikin rashin tabbas a Everton a dai dai lokacin da kwnataraginsa da ƙungiyar ta ƙare a wannan kakar, inda kuma bai jima da fara buga wasa a gasar ta frimiya a wannan kaka.(Liverpool Echo)
Newcastle United da Sunderland za su fuskanci ƙalubale wajen ɗauko ɗan wasan Sheffield United Sydie Peck a watan Janairu, yayin da Blades ɗin ba sa son siyar da dan wasan a wannan kaka. (Football Insider)
Jurgen Klopp ya bayyana cewar yayi yunƙurin ɗauko mai tsaron raga Jamus Marc-Andre ter Stegen, a lokacin da ya ke Liverpool, sai dai ya zaɓi ci gaba da zama a Barcelona maimakonAnfield. (Goal)
Sunderland na harin Franck Zambo Anguissa daga Napoli a watanJanairu, ind aa baya dan wasan ya taɓa taka leda a Fulham. (Sport Witness)
Ɗan wasan QPR Leon Scarlett, na ɗaukar hankulan Eintracht Frankfurt da AC Milan bayan da ya bar ƙungiyarsa ta farko a wannan kaka.(Standard)
PSV Eindhoven ta taya Kevin de Bruyne kan fam miliyan 1.5 daga Napoli. (De Telegraaf - in Dutch)