Su wane ne Larabawan Mahamid da aka kora daga Jamhuriyar Nijar?

Nijar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Jamhuriyar Nijar ta sake ɗaukar mataki mai tsauri kan wata al'umma da ta shafe shekaru tana rayuwa a yankin Diffa, bayan gwamnatin sojin ƙasar ta ba Larabawan Mahamid ɗin wa'adin ficewa daga ƙasar.

Hukumomi a ƙasar dai na zargin Larabawan ne da hannu wajen tallafa wa ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da ISWAP, waɗanda suka zama ɗoriya kan zargin da aka daɗe ana musu na tayar da zaune tsaye a wasu yankunan ƙasar.

Wannan mataki ya tayar da muhawara mai zafi a Nijar da ma ƙasashen yankin Tafkin Chadi, musamman saboda Mahamid sun daɗe suna kallon kansu a matsayin wani ɓangare na al'ummar Nijar.

Wannan ya sa ake tafka muhawara kan asalin Larabawan da zuwansu Nijar da ma inda za su koma idan har korar ta tabbata.

Hakan ya sa BBC ta yi nazari kan su wane ne Larabawan Mahamid? Ta yaya suka isa Nijar? Kuma me ya sa ake ambatarsu a rikicin da ya shafi tsaro, muhalli da kuma muhawara kan kasancewarsu ƴan ƙasa?

Su wane ne Mahamid?

Mahamid wata ƙabila ce daga cikin Larabawan da suka samo asali daga yankin gabashin Chadi, musamman a kusa da birnin Abéché. Yawancinsu makiyaya ne masu kiwon raƙuma, shanu da sauran dabbobi, suna rayuwa ne ta hanyar yawo daga wuri zuwa wuri domin neman makiyaya da ruwa.

A al'adance, Mahamid na daga cikin manyan al'ummomin Larabawan hamadar Sahel da Sahara, inda suke da daɗaɗɗen tarihin kasuwanci da kiwo a ƙasashen Chadi, Sudan, Nijar da wasu sassan Afirka ta Tsakiya.

Hukumomin ƙasar sun kuma bayyana damuwa kan cewa dubban mutane daga cikin al'ummar na zaune a Nijar ba tare da cikakkun takardun zama na doka ba.

Sai dai ce-ce-ku-cen da suka shafi ƙasar da Mahamid suka fito da kuma matsayinsu na doka ba sabon abu ba ne. Iyalan Mahamid sun shafe shekaru da dama suna rayuwa a Nijar, amma tambayoyi kan kasancewarsu ƴan ƙasar Nijar da kuma sahihancin takardun shaidar zamansu sun sha jefa su cikin rikici da hukumomin ƙasar.

Zuwan su Nijar

Farkon zuwan Mahamid Nijar ya samo asali ne daga wata mummunar fari da ta afka wa Chadi a shekarun 1970, inda dubban mutane suka tsallaka zuwa yankin Diffa domin neman ruwa da wuraren kiwo.

A shekarun 1980 kuma, wasu ƙungiyoyin Mahamid sun sake shiga Nijar yayin da yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen siyasa suka ƙaure a Chadi.

Da yawa daga cikinsu sun zauna a Diffa, inda wasu suka samu takardun zama ƴan ƙasa, suka samu damar shiga harkokin kasuwanci, aikin gwamnati da ma rundunonin tsaro.

A tsawon shekaru, Mahamid sun gina matsugunai da makarantun yara tare da zama na dindindin a yankin.

Rikici tsakaninsu da al'ummomin 'asali'

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da adadin Mahamid ke ƙaruwa, matsin lamba kan albarkatun ƙasa ya ƙaru.

Mazauna yankin Diffa sun riƙa zargin Larabawan da:

  • Mamaye wuraren kiwo.
  • Yawaita amfani da rijiyoyin ruwa.
  • Lalata muhalli saboda yawan raƙuma.
  • Mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Waɗannan zarge-zarge sun haifar da rikice-rikice masu jawo asarar rayuka tsakanin Mahamid da sauran al'ummomin yankin.

Ko da yake an cimma yarjejeniyoyin zaman lafiya a wasu lokuta, tashin hankali bai taɓa gushewa gaba ɗaya ba.

A cikin shekarun baya-bayan nan, gwamnatin sojin Nijar ta ƙara tsananta matakai kan Mahamid.

Mahukunta sun ce bayanan sirri da makaman da aka kama daga 2023 zuwa 2026 sun nuna yiwuwar wasu daga cikin Mahamid suna samar wa mayaƙan Boko Haram da ISWAP makamai, alburusai da kayan aiki.

Wannan zargi ne mai matuƙar nauyi saboda yankin Diffa ya shafe fiye da shekara goma na fama da hare-haren Boko Haram da ISWAP.

Sai dai Mahamid ba su amince da wannan zargi ba, kuma babu wata hujja da aka bayyana a bainar jama'a da ke nuna cewa gaba ɗayan al'ummar Mahamid suna da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci.

Korarsu a 2006 da 2007

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin Nijar ta yi ƙoƙari tare da yunƙurin korar Mahamid ba.

A shekarar 2006 gwamnatin Nijar ta ba su umarnin ficewa daga ƙasar, tana zarginsu da laifuffuka ciki har da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba, sata da kuma haddasa rashin tsaro.

A lokacin, dubban Mahamid sun yi ikirarin cewa su ƴan asalin Nijar ne ko kuma sun shafe shekaru da dama a ƙasar har ba su da wata ƙasa da za su koma.

Matsin lamba daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da kuma damuwar da Chadi ta nuna ya sa gwamnatin Nijar ta dakatar da shirin korar su a shekarar 2007, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a Diffa daga al'ummomin yankin.

Matsayar Chadi a yanzu

A sabon rikicin da ake ciki, gwamnatin Chadi ta bayyana cewa ba za ta karɓi duk wanda Nijar ta kora kai tsaye ba.

N'Djamena ta ce wajibi ne a tabbatar da asalin kowane mutum daban-daban kafin a ɗauke shi a matsayin ɗan ƙasar Chadi.

Hukumomin Nijar ba su bayyana inda suke son al'ummar Mahamid su koma ba. Amma Ma'aikatar Harkokin Wajen Chadi ta shaida wa BBC cewa bai kamata a ɗauki mambobin wannan al'umma a matsayin ƴan ƙasar Chadi kai tsaye ba saboda asalinsu na ƙabilar Larabawa.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce: "Larabawan da ake magana a kansu ƴan Nijar ne. An haife su a Nijar, sun rayu dukkan rayuwarsu a can kuma suna da tushe a ƙasar. Kasancewarsu mambobin wata al'umma ko ƙabila ba hujja ba ce da ke tabbatar da cewa su ƴan ƙasar Chadi ne."

Sanarwar ta ƙara da cewa ya kamata Nijar ta bi hanyoyin shari'arta wajen hukunta duk wanda ake zargi da haddasa matsalolin tsaro.

"Dole ne Nijar ta ɗauki alhakin wannan batu. Idan akwai mutanen da ake zargi da yunƙurin tayar da zaune tsaye ko kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasar, ya kamata su fuskanci shari'a a gaban kotunan Nijar. Laifin mutum laifinsa ne shi kaɗai, kuma hakan ba zai zama hujjar raba ko tilasta wa ɗaukacin wata al'umma yin hijira ba."

A yau, makomar dubban iyalan Mahamid na ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas, yayin da Nijar ke matsa lamba kan ficewarsu, Chadi kuma ke nuna cewa sai an tabbatar da asalinsu kafin ta karɓe su. Wannan ya sanya rikicin ya zama ba wai na tsaro kaɗai ba, har ma na ƙasa, ainihi da kuma makomar dubban mutane a yankin Sahel.