Tarihin Sheikh Ibrahim Inyass da tasirinsa a ɗarikar Tijjaniya

Asalin hoton, Others
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Sheikh Ibrahim Inyass na daga cikin manyan malamai da suka yi tasiri sosai a tarihin Musulunci a Afirka ta Yamma da ma duniya baki ɗaya, musamman a cikin ɗarikar Tijjaniyya, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa koyarwarta da kuma jawo miliyoyin mabiya a ƙasashe da dama.
Masana tarihi sun bayyana cewa tasirin Sheikh Ibrahim Inyass ya zarce iyakokin ƙasarsa ta Senegal, inda koyarwarsa ta bazu zuwa Najeriya, Nijar, Ghana, Sudan da sauran sassan duniya, wanda hakan ya sa ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jagororin Tijjaniyya na ƙarni na 20.
Sai dai, mene ne ainihin tarihin wannan babban malami? Ta yaya ya kai ga zama ɗaya daga cikin jagororin da suka fi tasiri a darikar Tijjaniyya? Kuma wane tasiri koyarwarsa ta yi ga al'ummomin Musulmi musamman a Afirka ta Yamma?
Domin samun ƙarin haske kan waɗannan tambayoyi da ma fahimtar muhimman abubuwan da suka ƙunshi rayuwarsa da gudunmawarsa ga Tijjaniyya, mun tattauna da wani masanin tarihi da ya yi nazari kan rayuwar Sheikh Ibrahim Inyass da tasirinsa a harkokin addini da zamantakewa.
A fagen Tijjaniyya kuwa, Sheikh Ibrahim Inyass ya taka muhimmiyar rawa wajen faɗaɗa ɗarikar, inda koyarwarsa ta "Faidha Tijjaniyya" ta jawo miliyoyin mabiyansa a Afirka da sauran wurare.
BBC ta yi nazari kan tarihinsa da tasowarsa da kuma tasirin karantarwarsa musamman kan matasan mabiya tsarin.
Haihuwa da karatu
Malami a Tsangayar Addini da Shari'ar Musulunci, Dr. Mustafa M. Kassim Kagarko, ya bayyana Sheikh Ibrahim Inyass a matsayin wani fitaccen malami da ya haɗa ilimi, tsoron Allah da kuma da'awa a rayuwarsa.
"Sheikh Ibrahim Inyass na cikin manyan malaman addinin Musulunci a Afirka ta Yamma. Duk da cewa yankin baƙar fata ne, har malamai Larabawa da waɗanda ba Larabawa ba sun amince da iliminsa. Akwai masu ganin cewa daga lokacinsa zuwa yau ba a samu irin bijimin malami kamarsa ba," in ji Dr. Kagarko.
An haifi Sheikh Ibrahim Inyass a ranar 8 ga Nuwamba a shekarar 1900, a garin Taiba Niassene da ke ƙasar Senegal ta yanzu. Ya taso cikin gida mai cike da ilimi da tsoron Allah, inda mahaifinsa, Sheikh Abdullahi Inyass, ya ba da muhimmanci ta musamman ga tarbiyyarsa.
Dr. Kagarko ya ce: "Mahaifinsa ya lura da irin kaifin basira da fahimtar da Allah ya ba shi, saboda haka ya mayar da hankali sosai wajen koyar da shi."
A cewarsa, Sheikh Ibrahim ya haddace Alƙur'ani ne kai-tsaye daga bakin mahaifinsa ba tare da dogaro da rubutu ba.
"Ana karanta masa ne kawai yana haddacewa saboda baiwar da Allah ya yi masa. Saboda muhimmancin Alƙur'ani a wajensa, mahaifinsa ya kasance yana sa shi maimaitawa sosai har ya kai yana sauke Alƙur'ani sau biyu a rana," in ji Dr. Kagarko.
Bayan haka ya ci gaba da karatun fiƙhu, nahawu da sauran fannonin ilimin addini a hannun mahaifinsa.
Ya zama malami tun yana matashi
Dr. Kagarko ya bayyana cewa tun yana da shekara 20, Sheikh Ibrahim ya riga ya zama babban malami kuma marubuci.
"Yana da shekara 20 kacal lokacin da ya rubuta littafinsa na farko mai suna Ruh al-Adab. Daga baya kuma ya rubuta An-Nur al-Basirah."
A shekarar 1922 kuma mahaifinsa ya rasu."Tun bayan rasuwar mahaifinsa bai sake zuwa wajen wani malami karatu ba. Shi kansa ya bayyana a wasu rubuce-rubucensa cewa bai yi karatu a wajen kowa ba face mahaifinsa."
Daga wannan lokaci ya mayar da hankalinsa ga karatu, bincike da koyarwa.
"Saboda yawan karantarwa da da'awa, daga baya ya daina sauke Alƙur'ani sau biyu a rana, har ya koma sau biyu kawai a mako," a cewar Dr. Kagarko.
Zama jigo a Tijjaniyya?
Da yake bayani kan dalilin da ya sa Sheikh Ibrahim ya zama jagora a Tijjaniyya, Dr. Kagarko ya danganta hakan da ikhlasi da tsoron Allah.
"Saboda ikhlasi da tsoron Allah ne. Ya gudanar da addini don Allah, ba domin neman wata duniya ba."
Ya ƙara da cewa: "Ya yi nazari sosai a kan tafarkin Tijjaniyya, ya fahimci manufofinta da muhimmancinta, sannan ya karɓe ta da cikakken yaƙini, sannan ya shiga yaɗa ta," in ji malamin jami'ar.
Ya ƙara da cewa Shehu Ibrahim Inyass bai karɓi tafarkin ba kamar yadda wasu suke yi kawai don sun ga wasu na yi.
Zuwa Najeriya da fara shuhura
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka ƙara wa Sheikh Ibrahim Inyass farin jini shi ne dangantakarsa da Najeriya.
A cewar Dr. Kagarko, Sheikh Ibrahim ya haɗu da Sarkin Kano na lokacin, Alhaji Abdullahi Bayero, yayin aikin Hajji a shekarar 1937.
"Sarkin Kano ya yi mamakin iliminsa da tsoron Allah. Daga nan ne ya gayyace shi zuwa Najeriya."
Sai dai Sheikh Ibrahim bai samu zuwa Najeriya ba sai bayan kusan shekara takwas.
"Da ya isa Kano an yi masa tarba ta musamman, sannan aka tara manyan malaman Kano domin su tattauna da shi."
Masana da dama na ganin cewa Najeriya ce ta zama ƙofar da ta buɗe wa Sheikh Ibrahim Inyass damar isa ga sauran sassan duniya.
"Duk da cewa yana da tasiri a Ghana da wasu ƙasashe, a Najeriya ne ya fara samun gagarumar shuhura wadda daga bisani ta bazu zuwa sauran duniya," in ji Dr. Kagarko.
Yawaitar zuwansa Najeriya ta haifar da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da al'umma da kuma malamai.
Dr. Kagarko ya ce: "Saboda yawaitar zuwansa da kuma matsayin da yake da shi, wasu iyalai sun nemi samun albarkarsa ta hanyar aurar da shi daga gidajensu."
Ya bayyana cewa Sheikh Ibrahim ya yi aure a Kano sannan ya sake yin aure a Kogi.
Faidha da matsayinsa a Tijjaniyya
Wani babban abin da ake danganta Sheikh Ibrahim da shi shi ne batun Faidha Tijjaniyya.
Dr. Kagarko ya ce tushen wannan tafarkin ya samo asali ne tun daga Sheikh Ahmad Tijjani.
"Sheikh Ahmad Tijjani ya yi nuni tun yana raye cewa wata Faidha za ta bayyana a gaba, lokacin da mutane za su yi rauni wajen bin koyarwar addini, sai wani ya zo ya sabunta harkar da'awa."
A cewarsa, mabiyan Tijjaniyya da dama sun yi fatan samun wannan matsayi, amma daga baya aka danganta shi da Sheikh Ibrahim Inyass.
"Ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen da'awa da kiran mutane zuwa ga Allah."
Dr. Kagarko ya kawo misalin yadda aka ruwaito cewa a wata rana kaɗai Sheikh Ibrahim ya jagoranci musuluntar dubban mutane a Ghana.
"Akwai bayanai cewa ya musuluntar da kusan mutum 8,000 a rana guda a Ghana."
Kiransa zuwa haɗin kan Musulmi
Dr. Kagarko ya ce daga cikin muhimman abubuwan da suka bambanta Sheikh Ibrahim shi ne yadda ya fifita Musulunci a kan bambance-bambancen ɗariku.
"Ya kasance yana cewa Musulunci wajibi ne, amma Tijjaniyya mustahabbi ce."
A cewarsa, wannan fahimta ce ta sa ya riƙa kyakkyawar mu'amala da malamai daga ɗariku daban-daban da ma waɗanda ba Tijjaniyya ba.
"Shi ya sa yake da kyakkyawar alaƙa da malaman Saudiyya da sauran manyan malamai a duniya."
Sai dai Dr. Kagarko ya yi gargaɗin cewa ba duk wanda yake kiran kansa ɗan Faidha ba ne yake tafiya a kan koyarwar Sheikh Ibrahim Inyass.
"Akwai masu cewa suna bin Faidha, amma babu abin da suke yi sai saɓa wa koyarwar Sheikh Ibrahim da kuma koyarwar addini."
Ya ƙara da cewa: "Da Sheikh Ibrahim yana raye, shi ne zai fara yaƙi da irin waɗannan fahimtofi."
A cewarsa, ko a zamanin Sheikh Ibrahim an taɓa samun irin wannan matsala a Ghana, lamarin da ya sa ya rubuta wata wasiƙa mai suna Risalat al-Muntaki domin mayar da martani ga wani da ya kauce wa tafarkin addini.



























