KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 22/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 22/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Ministan ilimin Koriya ta Kudu ya yi murabus saboda maguɗin jarabawa

    Ministan ilimi na Koriya ta Kudu ya yi murabus saboda badaƙalar magudin jarrabawa. Choi Kyo-jin ya ce ya ɗauki cikakken alhakin ruɗanin da aka samu sakamakon sabbin matakan daƙile magudi ta hanyar amfani da fasahar AI da aka ɗauka a jarrabawar shiga jami'a.

    Mako guda da ya gabata, wanda ya fi kowa samun maki a jarrabawar akawun haraji na Koriya ta Kudu ya amince da amfani da wata ƙaramar kyamara da wayar salula.

    Wannan ikirarin ya sa hukumomi suka sanar da matakan gano na'urori da aka boye, da suka hada da aika sanarwar gaggawa zuwa wayoyin hannu.

    Jarabawar shiga jami'a ta shekara-shekara a Koriya ta Kudu baban lamari da ke shafar miliyoyin dalibai a kasar.

  2. Falasɗinawa biyu sun mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza

    Gaza

    Majiyoyin kiwon lafiya a Gaza sun tabbatar da mutuwar Falasɗinawa biyu da suka jikkata sakamakon wani hari na Isra'ila a kudancin Gaza.

    A cewar Asibitin Nasser Medical Complex, mutum biyu sun samu raunuka ne a wani hari da Isra'ila ta kai yankin Al-Mawasi da ke birnin Khan Yunis a safiyar ranar Lahadi.

    Bayan an kai su asibiti domin jinya, daga bisani suka rasu sakamakon munanan raunukan da suka samu.

  3. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC.

    Za ku iya leƙwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta sauran labaranmu da kallon bidiyo, tare da tafka muhawara.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.