Jiragen yaƙi 5 na zamani da ƙasashen gabashin Afirka suka mallaka

    • Marubuci, Mariam Mjahid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Idan ka ɗaga kai ka kalli sararin samaniyar Gabashin Afirka, akwai wata gasa ta dabarun soji da ke gudana cikin sararin samaniyar yankin.

Ƙasashe daban-daban na yankin na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen jiragen yaƙi da horas da matuƙa jirage da inganta tsarin sa ido da leƙen asiri da kuma bunƙasa fasahohin yaƙi domin kare kansu tare da ƙarfafa yadda za su iya tinkarar barazanar tsaro.

Abin da ya fi jan hankali shi ne, kowace ƙasa a yankin ta ɗauki mabambantan hanyoyi domin cimman hakan.

Wasu sun mayar da hankali wajen mallakar jiragen yaƙi masu iya kare sararin samaniya tare da kai hare-hare kan wurare daban-daban.

Wasu kuma sun fi saka jari a jiragen da aka ƙera musamman domin kai hare-hare ta sama kan mayaƙan da ke ƙasa.

A gefe guda kuma, Rwanda ta zaɓi wata dabara ta daban, inda take gina ƙarfin sojinta na sama ta hanyar dogaro da jirage masu saukar ungulu fiye da jiragen yaƙi na zamani.

A wannan muƙala mun duba jiragen yaƙi biyar da ƙasashen yankin suka fi amfani da su domin inganta tsaronsu.

Su 30MK2 'Flanker' na Uganda

Uganda na cikin ƙasashen da suka fi ƙarfin jiragen yaƙi a yankin gabashin Afirka.

Rundunar sojin saman Uganda (UPDF Air Force) na amfani da jirgin yaƙi ƙirar Sukhoi Su-30MK2 wanda Rasha ta ƙera.

Jirgi ne mai nauyi da ƙarfin yaƙi, wanda ke iya gudanar da ayyuka iri-iri tare da yin dogon zirga-zirga ba tare da sauka ba.

Haka kuma yana iya ɗaukar makamai masu yawa, kuma an ƙera shi da na'urorin radar da kayan lantarki na zamani.

Ga Uganda kuwa, batun ba wai mallakar jirgin sama mai matuƙar sauri kaɗai ba ne.

Jirgin Su-30MK2 ya bai wa ƙasar damar sintiri da kare sararin samaniyarta, tare da kuma samar da goyon bayan hare-hare daga sama ga dakarun da ke ƙasa idan buƙata ta taso.

Saboda haka, ƙarfin wannan jirgi ba ya taƙaita ga girmansa ko ƙarfinsa kawai ba ne, ya kuma bayyana ne a yadda ake haɗa fasaha ta zamani, horo mai inganci da kuma ayyukan soji domin cimma manufofin tsaro.

Northrop F - 5E/F Tiger II na Kenya

Kenya kuwa ta ɗauki wata hanya ta daban wajen gina ƙarfin sojinta na sama.

Rundunar sojin saman ƙasar na amfani da jiragen yaƙi kirar Northrop F-5E da F-5F Tiger II, waɗanda aka fara ƙera su tun shekaru masu yawa da suka gabata.

Sai dai duk da cewa jirgin tsohon yayi ne, har yanzu yana kan ganiyarsa a fagen yaƙi.

Kenya ta ci gaba da amfani da waɗannan jirage tare da inganta su, inda suke taka muhimmiyar rawa wajen kare sararin samaniyar ƙasar da kuma gudanar da ayyukan soji.

Har ila yau, jiragen F-5 sun tara ƙwarewa sosai a fannoni daban-daban na aiki, ciki har da hare-haren soji da suka shafi yaƙi da ƙungiyar al-Shabab a Somaliya.

Masana na cewa horar da matuƙa jirgi da kula da gyaran jirage da ƙwarewar gudanar da ayyuka da samun kayan gyara cikin sauƙi da kuma iya tabbatar da cewa jirage na ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Duka waɗannan abubuwa ne da za su iya zama masu muhimmanci kamar sabunta jiragen kansu wajen ƙarfafa ƙarfin soji.

Jirgin yaƙin Chengdu J 7 na Tanzaniya

Rundunar sojin saman Tanzania na cikin rundunonin da ke amfani da jiragen yaƙi ƙirar Chengdu J-7 da ake ƙera wa a ƙasar China.

An ƙera jirgin J-7 ne bisa tsarin jirgin yaƙi na tsohuwar Tarayyar Soviet mai suna MiG-21, kuma ƙasashe da dama sun yi amfani da shi tsawon shekaru.

Tanzania ta karɓi sabbin nau'o'in wannan jirgi, ciki har da J-7G, waɗanda aka kammala miƙa mata a shekarar 2011.

An ƙera jiragen ne domin kare sararin samaniya, kuma suna ɗauke da na'urori da kuma makamai masu linzami da ake harbawa daga ƙasa zuwa sama.

Ga Tanzania, waɗannan jirage wani ɓangare ne na faɗaɗɗen tsarin tsaro na ƙasar, wadda ke da faɗin ƙasa mai yawa da kuma doguwar gabar teku a Tekun Indiya.

Saboda haka, samun damar sanya ido kan sararin samaniya da kuma ɗaukar matakin gaggawa idan buƙata ta taso, na daga cikin muhimman ginshiƙan dabarun tsaron ƙasar.

Jirgin yaƙin Su 25 na DRC

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fuskantar manyan ƙalubalen tsaro a yankin, musamman a gabashin ƙasar inda rikice-rikice suka daɗe suna ƙamari.

Rundunar sojin saman ƙasar na amfani da jiragen yaƙi kirar Sukhoi Su-25, waɗanda aka ƙera a tsohuwar Tarayyar Soviet.

Ba kamar wasu jiragen yaƙi da aka fi tanada domin fafatawa da jirage a sararin samaniya ba, an ƙera Su-25 ne musamman domin taimaka wa dakarun ƙasa da kuma kai hare-hare kan wuraren da ke ƙasa.

Saboda haka, babban aikinsa shi ne ƙarfafa ayyukan soji da dakarun ƙasa ke gudanarwa a fagen fama.

Ga ƙasa mai faɗi kamar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, samun damar amfani da ƙarfin sojin sama a yankuna masu nisa da wahalar isa na da matuƙar muhimmanci a fannin dabarun tsaro.

Jirgin yaƙin Mi -17 na Rwanda

Ba kamar Uganda da Kenya da Tanzania ba, Rwanda ba ta amfani da jiragen yaƙi na zamani wajen gudanar da ayyukan rundunar sojin samanta.

Maimakon haka, ta gina ƙarfin sojinta na sama ne ta hanyar mayar da hankali sosai kan jirage masu saukar ungulu.

Daga cikin jiragen masu saukar ungulu da rundunar sojin saman Rwanda ke amfani da su akwai Mi-17, wanda ake amfani da shi wajen jigilar dakaru da sauran kayan aikin soja, da kuma Mi-24 da Mi-35, waɗanda ke da ƙarfin kai hare-hare.

Wannan tsarin ya nuna wani muhimmin al'amari game da ƙarfin rundunar sojin sama.

Ƙarfin sojin sama ba lallai ne auna shi da yawan jiragen yaƙi kaɗai ba.

Ga ƙasar da ke buƙatar saurin tura dakaru zuwa wuraren aiki da kwashe waɗanda suka jikkata ko tallafa wa dakarun ƙasa da kuma gudanar da ayyuka a yankunan da ke da wahalar shiga, jirage masu saukar ungulu na iya kasancewa masu matuƙar muhimmanci.

Wace ƙasa ce ta fi ƙarfi a sararin samaniya?

Babu takamammiyar amsa guda ɗaya game da wannan tambayar.

Idan za a auna ƙarfin fasaha da kuma irin nisan da jirgin yaƙi zai iya kaiwa wajen gudanar da aiki, jirgin Su-30MK2 na Uganda na daga cikin waɗanda ke da ƙarfi sosai.

A nata ɓangaren, Kenya na cin moriyar gogewa mai tsawo wajen amfani da jiragen F-5, tare da ci gaba da kula da su domin su kasance cikin yanayin aiki.

Tanzania kuwa na dogaro da jiragen Chengdu J-7, yayin da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango (DR Congo) ke amfani da jiragen Su-25, waɗanda aka fi sani da ƙwarewa wajen kai hare-hare da kuma tallafa wa dakarun da ke fagen daga.

Rwanda kuma ta nuna wata dabara da ta sha bamban da sauran ƙasashen yankin, inda ta fi mayar da hankali kan amfani da jirage masu saukar ungulu da sauran kayayyakin aikin soja na sama domin inganta safarar sojoji, saurin kai ɗauki da kuma ayyukan tsaro, ba tare da dogaro da jiragen yaƙi na zamani ba.

Wace ƙasa ce ta fi mallakar jiragen yaƙi na zamani?

Ƙarfin sojin sama na zamani ba ya taƙaitu ga wanda ya mallaki jirgin yaƙi mafi sauri kawai.

Ya haɗa da abubuwa da dama kamar na'urori da hanyoyin sadarwa da na tattara bayanan sirri da horar da matuƙa jirgi da kula da jirage da makamai masu kai hari daidai wurin da aka nufa.

Dan sanya sanya ido daga sama da kuma ikon juya bayanan da aka tattara don ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Jiragen sama su ne abin da aka fi gani a fili a rundunar sojin sama.

Sai dai a bayan kowane jirgin sama akwai cikakken tsarin fasaha da ababen more rayuwa da kuma ƙwararrun ma'aikata da aka horar domin tabbatar da cewa jirgin zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa a lokacin da ake buƙatarsa.

A ƙarshe tambayar ba ita ce wace ƙasa ce ke da jirgi mafi girma ko mafi zamani ba.

Muhimmin abin tambaya shi ne:

Idan aka fuskanci barazana ga tsaron sararin samaniyar wata ƙasa, cikin wane lokaci za ta iya gano barazanar?

Cikin wane lokaci za ta iya mayar da martani? Kuma yaya ƙarfin da take da shi na sarrafa da kuma kare sararin samaniyarta?