Iran ta gargaɗi ƙasashe kan haɗin gwiwa da Amurka wajen kai mata hari
Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta Iran ta gargadi ƙasashen yankin da ke haɗin gwiwa da sojojin Amurka wajen kai mata hari tana cewa su sa ran fuskantar mummunan sakamako.
Gargadin ya zo ne bayan hare-haren da Amurka ta kai wasu yankunan kudancin Iran a daren Talata.
Iran ta ce dakarunta sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin Amurka da ke Jordan, Bahrain da Erbil na Iraqi.
Hedikwatar ta kuma yi gargaɗi ga ƙasashen da ke karɓar sojojin Amurka, tana cewa duk ƙasar da ta taimaka wa abin da ta kira sojojin Amurka masu kai hari, za su ɗanɗana kuɗarsu.
A gefe guda, Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe fararen hula aƙalla biyar tare da jikkata sama da 60 a ƙauyen Kohstak da ke Sirik, yayin da ake gudanar da bikin aure.
Rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran sun ce yara na cikin waɗanda suka mutu, yayin da mata da yara ke cikin mafi yawan waɗanda suka jikkata.