Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin mace za ta iya haihuwa a duniyar wata?
- Marubuci, Daisy Stephens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƴan sama jannati sun yi wa duniya manyan alƙawura da dama.
A watan Mayu, NASA ta bayyana shirinta na dala biliyan 20 domin kafa sansani a duniyar wata da zai yi aiki da makamashin nukiliya da na hasken rana.
Nan da shekarar 2032, hukumar kula da sararin samaniya ta duniya na son ɗn'adam ya fara iya rayuwa a duniyar wata ko da ta wucin-gadi ce.
Tana kuma shirye-shiryen tura ɗan'adam zuwa duniyar Mars a karon farko, tafiyar da ta ce za a iya kwashe watanni 10 ana yin ta.
Amma idan muna son yin rayuwa mai tsawo a wajen duniyarmu, akwai bukatar mu iya haihuwa a can - abin da ke nufin cewa za a ga wasu abubuwan da ba a saba gani ba.
Saɓanin yadda duniyarmu take cike da iska da yanayi mai yalwa, duniyar Wata da Mars ba haka suke ba - domin ba su da sarari mai iska da ke kaɗawa.
Kuma ba su kai girman duniyarmu ba, shi ya sa babu wata isasshiyar iska ta yadda komai yana motsi ne a hankali da jinkiri.
Ko da a ce mace za ta iya ɗaukar ciki a wata duniyar ko a sararin samaniya, za a riƙa yi wa batun kallon almara da masana kimiyya kawai suke iya hasashe.
Daga ƙila-wa-ƙala zuwa binciken masana
Dr Nicole McPherson babbar malama ce a Jami'ar Adelaide a Australia, kuma ta na jagorantar ƙungiyar Nazarin Maniyyin Halittu a Cibiyar Freemasons da ke kula da lafiyar maza.
Ta fara nazarin yadda za a iya ɗaukar ciki a sama sararin samaniya bayan kallon wani shirin talabijin na musamman kan sama jannati tare da mijinta.
"Abin da ya faro kamar wasa da ƙila-wa-ƙala… a yanzu ya zama babban maudu’in bincike" in ji McPherson.
Ita da wasu masu bincike sun gudanar da wani samfuri kan tasirin ƙwayoyin halittar maniyyi a kan wasu abubuwa idan suka kasance a sararin samaniya.
Sun gano cewa wasu maniyyin sun ɓace, inda kusan kashi 50 na maniyyin suka gaza kaiwa can cikin ramukan saboda yanayin jinkirin da rashin wadatar iska.
Duk da yake binciken bai bayyana yanayin gudanar iska da motsi ba a waɗannan duniyoyin irin su Mars, McPherson ta ce hakan na nuna cewa ƙwayoyin halitta suna aiki yadda ya kamata a yanayin duniyarmu.
"Wannan ya nuna cewa maniyyi na amfani da yanayin gudanar duniya wajen tasiri da kuma hayayyafa,” in ji ta.
Ƙalubalen nauyin duniya ba wai kawai ya tsaya ga tasirin ƙwayoyin halitta ba ne ko ɗaukar ciki. Masu binciken sun kuma duba yadda maganaɗisun da ke riƙe mutane a duniyar ke tasiri a cikin awanni 14.
Dr Fathi Karouia, babbar mai binciken fasaha a NASA ta ce: "Maganaɗisun doron duniya na tasiri kan yadda ƙwayoyin halliya ke rarrabuwa da tsara su domin su yi aiki - wanda hakan na da tasiri wajen girmansu."
Ƙarfin sinadaran da ke yawo a iska
Babban ƙalubale na biyu shi ne sinadaran maganadisu da ke yawo a iska (radiation) - da ke kaɗawa a iska kima na iya zama haɗari ga lafiyar ɗan'adam.
An riga an san cewa yana da illa ga maniyyin ɗan'adam da ƙwayayen jikin ƴa mace.
Saboda akwai wasu abubuwan da ke kare mu daga waɗannan sanadarai da ke yawo a iska shi ya sa ake samun bambanci da wasu duniyoyin irin su Mars.
Kwararren likitan sararin samaniya a Jami'ar Kiwon Lafiya ta Turkiyya, Dr Abdurrahman Engin, ya ce sanadaran da ke yawo a sararin samaniya (galactic cosmic radiation (GCR) waɗanda ke samuwa sanadiyyar abubuwa kamar tarwatsewar taurari, da ake kira supernovas.
Waɗannan abubuwan fashewar da za su iya shiga cikin jirgin ƴan sama jannati, kuma hakan ya fi illa a kan sanadaran da ke yawo a iskar duniyar bil'adama.
A yayin tafiyar kimanin watanni shida daga Duniya bil'adama zuwa duniyar Mars, wata ƴar sama jannati mai juna biyu na iya cin karo da sanadarai masu illa na sararin samaniya.
Irin hakan kuma zai iya illa ga ƙwayoyin halittarta da kuma illata tsarin ƙwayoyin halittar bil'adama.
"Saurin rabuwar tantanin halitta da samuwar gaɓoɓi a farko farkon ciki yana nufin cewa ko tsarin ƙwayar halitta, na iya haifar da illar da za a dade ana shan wahalar ta," in ji Engin.
Waɗannan matsalolin za su iya haifar da ɓarin ciki da wasu illolin da za su iya kaiwa ga samun cutar daji (kansa) ga yaron da aka haifa.
Darussa daga halittar ɗan'adam
Ya kamata a iya fahimtar ko mutane za su iya haihuwa a wasu duniyoyi idan har ana tunanin wata rana bil'adama zai yi rayuwa a irin wadannan duniyoyi.
Sai dai kuma batu ne na yadda za a kare masu zuwa wasu duniyoyi, in ji Jan-Bernd Stukenborg, farfesa a fannin kwayoyin halitta a Jami'ar Uppsala da ke Sweden.
Ko da a ce mutane ba su fara hayayyafa a duniyoyin sararin subuhana ba, ya ce 'yan sama jannati na cikin haɗari game da ƙwayoyinsu saboda yadda suke cikin wannan yanayin, to amma ta hanyar bincike ne za a iya gano yadda za a kare su.
“Shi ya sa nake tunanin ya kamata a gudanar da wannan bincike mai matuƙar muhimmanci," in ji shi.
McPherson ta ce idan aka yi bincike sosai a wannan fannin, za a iya fahimtar yadda abin yake domin gano wasu muhimman abubuwa da suka shafi halittar ɗan adam.
Bambancin namiji
Masana na ganin cewa tunda ana samun ƙarin mata ƴan sama-jannati, ya kamata a yi nazarin yadda ƙwayoyin halittarsu za su yi tasiri ba a tsaya kan maza kaɗai ba.
Binciken da Stukenborg ta yi ya gano cewa mata ’yan sama jannati na amfani da ƙwayoyi idan za su tafi sararin samaniya domin dakatar da jinin al’adarsu.
To amma kuma akwai bukatar a yi wani binciken kan jinin al’ada a sama jannati, in ji McPherson.
“Ba mu taɓa nazarin wannan ba zuwa yanzu,” in ji ta.
Karouia ya ce akwai hujjojin da ke nuna cewa ƙwayoyin halitta za su samun matsala a sama jannati.
Abin da har yanzu ba a gama fahimta ba shi ne ɗaukar ciki, in ji shi.
"Kai tsaye ba za a iya cewa muna da alƙaluma ko bayanai kan yadda za a raini ciki a wata duniyar ba, musamman yadda mahaifa za ta yi aiki da kuma ginuwar sassan jikin ɗan'adam," in ji shi.
Amma kusan kowa ya aminta cewa akwai babban aiki sosai da ya kamata a yi.
"Bai kamata a bari a samu matsala ba… ya kamata mu yi tunanin a kan hakan yanzu," in ji shi.