Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun ga saran maciji a jikin mahaifinmu - Iyalan Janar Rabe
Iyalan Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya sun shaida wa BBC cewa suna da kyakkyawan zaton cewa maciji ne ya sare shi sa'ilin da yake hannun ƴan bindiga, wani abu da suke tunanin shi ne ya yi ajalinsa.
Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ta shaida wa BBC cewa saɓanin abin da yaɗa cewa Manjo Janar Rabe Abubakar ya rasu ne sakamakon hawan jini da ciwon suga, ɗiyar tasa ta ce ba shi da tarihin ciwon.
"Ba shi da tarihin ciwon hawan jini da suga gaskiya. Sarar maciji ne kamar yadda muka gani. Ƙaninsa da ya yi masa wanka ya tabbatar da saran maciji ne. Babu harbi ko wani abu a jikinsa," in ji ƴar Manjo Janar Rabe.
Dangane kuma da yadda aka samu gawar marigayin, ƴar tasa ta ƙara da shaida wa BBC cewa "kamar yadda muka sami labari sun bayar da location (wuri) inda aka je aka karɓe ta."
Ta kuma bayyana irin halin da suka shiga a makonni biyu na garkuwa da mahaifin nasu.
"Mun shiga cikin tashin hankali da damuwa da alhini tun daga ɗauke shi har zuwa mako biyu lokacin da ya rasu. Kuma mun yi imanin cewa ajalinsa ne ya zo da haka kuma muna fata Allah ya ba mu ikon cin wannan jarrabawa," in ji ƴar tasa.
'Muna roƙon gwamnati ta ceto mahaifiyarmu'
Ɗiyar ta Manjo Janar Rabe Abubakar ta kuma ƙara da yin kira ga gwamnati da ta yi bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta gaggauta sakin mahaifiyarsu wadda ƴan bindigar suka kama tare da mahaifin nasu, wadda kuma har yanzu ake tsare da ita.
"Gaskiya muna cikin damuwa tunda har yanzu ba a sake ta ba. Bayanin da hukumomi suke yi mana shi ne suna ta ƙoƙari. Kuma waɗanda suke garkuwa da ita ba su kira ba," in ji ƴar tasa.
A halin da ake ciki kuma, hukumomin jihar Katsina waɗanda suka tabbatar da mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar, sun ce ya mutu ne sakamakon wasu matsalolin lafiya da ke da alaƙa da ciwon sukari da hawan jini.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar Katsina ta fitar, ta ce mutuwar ''mummunan abu ne'', ta kuma ce ta nuna buƙatar a gaggauta ɗaukar matakan yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke yin barazana ga zaman lafiya a faɗin yankin.
Ƴan Najeriya da dama sun yi Alla-wadai da mutuwar marigayi babban hafsan sojin a hannun ƴan bindiga.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda ya bayyana kaɗuwarsa kan lamarin, ya ce yana gargaɗin ƴan bindigar da su gaggauta miƙa wuya ga hukumomi.
Ya ce gwamnati ba za ta miƙa wuya ga ƴan bindiga ba, kuam za ta ta ci gaba da daukarsu a matsayin makiyan ƙasar.
Shugaba Tinubu ya ce ƴan bandigan sun riga sun aikata abu mafi muni , amma "gwamnati ba za ta biya musu buƙatarsu ta ganin an sako ƴan ƙungiyar da ke hannun jami'an tsaronmu ba.
"Kamar yadda na faɗa a ranar 12 ga watan Yuni: Ƴan bindiga, da masu sace mutane , da masu daukar nauyin ta'addanci sun mika wuya a yanzu ko kuma su fuskanci fushin gwamnatin Najeriya."
A ƙarshen makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta bayyana mutuwar Abubakar wanda ya mutu a hannun ƴan bindigan da suka sace su.
"Hedikwatar tsaro ta yi jimamin sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar (Mai Ritaya), wanda ya rasa ransa a hannun ƴan bindiga da suka sace shi," in ji sanarwar.
Hedikwatar tsaro ta na miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan Abubakar da abokan aikinsa da dukkan ƴan Najeriya.
An yi jana'izarsa ne a ranar Lahadi da misalin karfe 6:00 na yamma a masallacin GRA na Katsina, iyalansa da sauran jama'a sun halarci sallar jana'izar.
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sun sace Abubakar wanda ya kasance kakakin sojoji tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017, a lokacin da yake tafiya da matarsa jihar Katsina a watan jiya.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa jami'in mai ritaya ya halarci wani ɗaurin aure a ranar 30 ga Mayu, inda wasu mutane ɗauke da makamai sun kai hari kan motarsa, suka kama shi tare da matarsa da direban motarsu.
Kwanaki kaɗan bayan rasuwarsa, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta da ke nuna Abubakar a tsare. Ya samu rauni a ƙafar hagu, yana tare da matarsa da wasu sauran mutane da aka kama.
Sace Abubakar da mutuwarsa ya nuna ƙalubalen tsaro da ake ci gaba da fuskanta a sassan arewa maso yammacin Najeriya, wasu gungun masu aikata laifuka na cikin gida da aka fi sani da ''yan fashin daji" su ke yawan sace mutane domin neman kuɗin fansa, da satar shanu da kuma kai hari a ƙauyuka.
Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da rikicin ya fi shafa.
Wane ne Manjo janar Rabe Abubakar?
A watan Agustan shekarar 2015 ne Abubakar ya karɓi ragamar mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, inda ya maye gurbin Janar Chris Olukolade bayan ritayarsa daga aiki bayan shekara 35.
An haife shi ne a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 1965. Ɗan asalin ƙaramar hukumar Batsari ne na jihar Katsina.
Ya yi karatun firamare da sakandare, sanna ya yi digiri a fannin tarihi, sannan ya shiga aikin soja.
Ya fara aikin soja ne a shekarar 1989, inda ya fito da muƙamin laftanal, inda daga nan ya yi aikace-aikace da dama a wurare daban-daban.
Daga cikin muƙaman da ya riƙe akwai kodinetan sashen watsa labarai na hedkwatar aikin soji na musamman a yankin Neja Delta da kwamandan makarantar horar da jami'an hulɗa da jama'a na rundunar sojin ƙasa wato NASPRI da ke jihar Legas da babban daraktan hulɗa da jama'a a kamfanin jin daɗi da walwalar sojojin ƙasan Najeriya.
Daga cikin ƙasashen da ya je samun horo akwai China, inda ya samu horo na musamman a kwalejin horar da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da sauransu.