Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Janar Rabe da ya rasu a hannun ƴanbindiga?
A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun ƴanbindiga a jihar Katsina.
Gwamnatin Katsina ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasiru Mu'azu ya fitar, inda ya ce tsohon hafsan ya rasu ne sakamakon ta'azzarar ciwon siga da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Sanarwar ta bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar tare da jami'an tsaro suka yi na ganin an kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya, ba su samu nasarar ceto shi da rai ba.
Mutuwar tasa ta jefa iyalansa da al'ummar jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya cikin alhini da jimami.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da bayyana lamarin a matsayin babbar asara.
Ya ce wannan wata alama ce da ke nuna buƙatar a ƙara haɗa kai domin tunkarar matsalar tsaro da ke addabar al'umma.
Yadda aka sace Janar Rabe
A kwanakin baya ne dai ƴanbindida suka sace Janar Rabe da matarsa a Katsina, inda suka nuna su a bidiyo suna kira ga hukumomin Najeriya su ceto su.
Ƴanbindiga sun sace tsohon janar ɗin tare da maidakinsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Jim kaɗan bayan samun rahoton garkuwa da shi ne hukumomi a ƙasar suka ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin yadda za su amso sojan, wanda ɗan asalin jihar ta Katsina ne amma ya fi yawan zama a Kaduna, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Nakeriya Janar Michael Onoja ya sanar.
Katsina na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, sai dai a baya-bayan nan lamarin ya yi sauƙi bayan matakan da al'umma da kuma gwamnati ta dauka.
Sai dai ci gaba da irin wannan garkuwa da mutane na nuna ƙaruwar wannan matsala ta rashin tsaro wadda ta addabi arewa maso yammacin Najeriya.
A baya-bayan nan irin wannan garkuwa da mutane sun faru a wasu makarantu da ke jihohin ƙasar, lamarin da ya tayar da hankula, kuma har shugaban ƙasar ya sha walwaahi karbo wadanda aka sace.
A ranar 25 ga watan Disamban 2025 Amurka ta kaddamar da wani hari kan jihar Sokoto mai makwaftaka da Katsina, kan sansanin wasu masu dauke makamai waɗanda aka ce suna da alaƙa da ƙungiyar IS.
Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da wannan matsala.
Wane ne Janar Rabe?
Manjo Janar Rabeh Abubakar, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2017, an sace shi daga cikin matorsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta shiga Katsina daga Kaduna a ranar Asabar.
A watan Agustan shekarar 2015 ne Abubakar ya karɓi ragamar mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, inda ya maye gurbin Janar Chris Olukolade bayan ritayarsa daga aiki bayan shekara 35.
An haife shi ne a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 1965. Ɗan asalin ƙaramar hukumar Batsari ne na jihar Katsina.
Ya yi karatun firamare da sakandare, sanna ya yi digiri a fannin tarihi, sannan ya shiga aikin soja.
Ya fara aikin soja ne a shekarar 1989, inda ya fito da muƙamin laftanal, inda daga nan ya yi aikace-aikace da dama a wurare daban-daban.
Daga cikin muƙaman da ya riƙe akwai kodinetan sashen watsa labarai na hedkwatar aikin soji na musamman a yankin Neja Delta da kwamandan makarantar horar da jami'an hulɗa da jama'a na rundunar sojin ƙasa wato NASPRI da ke jihar Legas da babban daraktan hulɗa da jama'a a kamfanin jin daɗi da walwalar sojojin ƙasan Najeriya.
Daga cikin ƙasashen da ya je samun horo akwai China, inda ya samu horo na musamman a kwalejin horar da manyan hafsoshin tsaron ƙasar da sauransu.
Najeriya ta yi rashi - Rundunar tsaro
A saƙon jaje da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyaa rashin a matsayin babba, inda ta ce za ta ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya.
"Muna miƙ saƙon ta'aziyya da jaje kan rasuwar abokin aikinmu Manjo Janar Abubakar ga iyalansa da sauran ƴan Najeriya baki ɗaya. A lokacin da yake aiki a matsayin mai magana da yawun rundunar tsaro, ya taimaka matuƙa wajen yaƙi da matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta."
Rundunar ta ƙara da cewa jajircewarsa da ƙoƙarinsa wajen tabbatar a zaman lafiya da haɗin kan Najeriya abin koyi ne babba.
Sai dai rundunar ta ce sun yi shiru ne game da sacen shi da aka yi saboda yunƙurin da ake yi ne ceto shi, inda jami'an tsaron Najeriya sun kasance suna ta ƙoƙarin tabbatar da ceto shi cikin ƙoshin lafiya.
"Mutuwarsa za ta sa jami'anmu su ƙara ƙaimi wajen cigaba da aiki ba dare ba rana domin kare martabar ƙasarmu Najeriya da kuma tabbatar da kariyar al'ummar ƙasar baki ɗaya," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, "muna tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da tsaro a ƙasar, tara da cimma duk waɗanda suke da hannu a matsalolin tsaro."