Tambayoyi da ƙilawaƙala kan yarjejeniyar Iran da Amurka

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sanarwar cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ake yi tsakanin Amurka da Iran ta kasance wata kyauta ta musamman ga Donald Trump yayin da ya ke shirin yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa - ko da yake dai rigar rashin tabbas ta ƙanannade yarjejeniyar.

Shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumunta inda ya shelanta yarjejeniyar cewa za a buɗe mashigar Hormuz inda za a ci gaba da safarar jiragen ruwa na kasuwanci kuma Amurka za ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba.

"A Bari man fetur ya kwarara!" Trump ya furta a ranar Lahadi.

Ya ci gaba da bayyana cewa, saɓanin gazawar shugabannin Amurka da suka shuɗe, ya yi nasarar ƙulla "muhimmiyar yarjejeniya" da za ta samar da "zaman lafiya da tsaro a yankin baki ɗaya".

Irin wannan iƙirarin dai ba sabon abu ba ne ga Trump. Bugun ƙirjin da ya yi game da yarjejeniyar da aka cimma a bara da ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza wadda ya bayyana a matsayin- "zaman lafiya da zai ɗore har abada" kuma "farkon zamanin samun aminci da imanin ga Allah" - duk da cewa dai lamarin da ke ƙasa ya sha bambam da kalaman na sa.

A yayin da ake neman ƙulla irin waɗannan manyan yarjejeniyoyin na diflomasiyya, nasara ko rashin ɗorewarsu yawanci yana dogara ne akan samun cikakkun bayanai. Kuma a kan wannan batu ana fuskantar ƙarancin cikakkun bayanai.

A cikin wata hira da ya yi da yammacin Lahadin da ta gabata da gidan talabijin na Fox News, mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya bayyana cewa i cikin wannna yarjejeniyar akwai batun cewa Itran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba, kuma Amurka za ta iya tabbatar da cewa an bin sharuɗɗan yarjejeniyar.

Amma duk da haka akwai alamar tambaya kan batutuwa masu mahimmanci da suka haɗa da yadda za a tabbatar da takunkumi kan shirin inganta Uranium da kuma abin da ya kamata ya faru da tarin Uranium ɗin da Iran ke da shi a yanzu.

Tabbas za a tattauna wasu daga cikin waɗannan batutuwan yayin cikin sabon wa'adin tsagaita wuta na kwanaki 60 da ake ciki yanzu. Amma idan akwai abin da ya bayyana ƙarara bayan kwashe shekaru da dama ana ƙoƙarin shawo kai ko tursasawa Iran ta yi watsi da burinta na mallakar makamin nukiliya, shi ne rashin tabbas, duk kouwa da duk abubuwan da Amurka ke iƙirarin ta cimma a cikin wannan sabuwar yarjejeniyar.

A wani lamari da ke tabbatar da hakan, kwamitin ƙoli na tsaron ƙasar Iran ya fitar da wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata yana mai cewa "za a ɗage tattaunawar ƙarshe har sai bayan aiwatar da alƙawurran da ɗaya ɓangaren ya yi ƙarƙashin yarjejeniyar".

Yanayin waɗannan alkawuran- da kuma yadda Iran ke fassara su - zai taimaka wajen sanin ko wannan yarjejeniya ta ɗore.

Kwararru a kasuwar makamashi sun yi gargaɗin cewa zaii iya ɗaukar lokaci kafin jigilar ɗanyan mai ta mashigar Hormuz ya dawo kamar yadda ya ke kafin ɓarkewar rikicin. Za a iya kwashe makonni kafin a iya tabbatar da wucewar jiragen ruwan dakon mai da suka daɗe suna jira a bakin mashigar da kuma haƙo nakiyoyi da aka binne tare kuma da dawo da jigilar mai da zai wadata.

Yayin da ya rage kwanaki da dama kafin a rattaba hannu a hukumance kan yarjejeniyar, Iran da Amurka na da lokaci don daidaita muhimman batutuwa don tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar - amma hakan na nufin akwai lokacin da za ta iya wargajewa.

Wani abin da zai iya kawo cikas shi ne batun Isra'ila.

Wannan dai yaƙi ne na ɓangarori uku, kuma Trump ya shaidawa jaridar Wall Street Journal a ranar Lahadin da ta gabata cewa, ya fusata ne da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, bayan ya bayar da umarnin kai hare-hare kan Lebanon a ƙarshen mako, da ya yi imanin cewa, za ta iya ruguza yarjejeniyar da aka kusa kammalawa da Iran.

Yarjejeniyar ta ɗore zuwa aƙalla tsawon lokacin da aka sanar da ita ga bainar jama'a. Amma idan har Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a Lebanon, Iran za ta iya yanke shawarar rufe Mashigar Hormuz, lamarin da zai sake jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali.

A cikin kalaman nasa, Vance ya kuma yi la'akari da irin mummunan tasirin da wannan yaƙin ya yi kan Amurkawa sakamakon hauhawar farashin makamashi da yadda hakan ya haifar da taɓarɓarewar tattalin arziki.

"Sakona na farko ga jama'ar Amurka shi ne na godiya," in ji shi, yayin da ya yi alƙawarin cewa farashin makamashi zai fara sauka.

Samun hakan da sauri, da kuma yadda hakan zai iya kawo wa Amurkawa sauƙi daga mawuyacin halin da suka shiga, zai taimaka sosai wajen tabbatar da ko matsin lambar siyasa da ƴan jam'iyyar Republican ke fuskanta zai ragu kafin zaɓen majalisar wakilai na tsakiyar wa'adi na watan Nuwamba.

Trump da jam'iyyarsa na fuskantar matsin lamba a siyasance, kamar yadda ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna. Wani bincike na YouGov ya gano cewa kashi 63% na Amurkawa ba su yarda da yadda yake tafiyar da tattalin arzikin ƙasar ba, inda kashi 57% ke ganin tattalin arzikin ya ƙara taɓarɓarewa.

Duk da haka, ya kamata yarjejeniyar ranar Lahadi ta taimaka wajen rage wasu matsalolin tattalin arziki, idan ba ta kawar da su baki ɗaya ba. Idan farashin man fetur ya fara faɗuwa da gaske, zai iya zama wani alama na zahiri ga Amurkawa cewa sauki ya fara samuwa.

Wani muhimmin mataki ne komawa matakin yadda abubuwa su ke kafin ɓarkewar rikicin, ko da kuwa a halin da a ke ciki yanzu Trump bai samu cimma manyan manufofinsa ba, kuma har yanzu yana fuskantar barazanar siyasa a gida.