Nan muka kawo karshen shirin
Sunana Mohammed Abdu nake muku asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
Sunana Mohammed Abdu nake muku asuba ta gari.
Za kuma mu kawo muku karawa tsakanin Faransa da Senegal ranar Talata.
Kevin de Bruyne da Jeremy Doku sun fita daga wasan an kuma maye gurbinsu da Hans Vanaken da kuma Matias Fernandez-Pardo.
Karin minti biyar aka yi, kuma Belgium ta samu dama, amma ta kasa ratsa bayan Masar.
An yi karin minti biyar, kuma ana ta kai hare-hare, Masar na amfani da kwallon sama ko za ta samu ta kara na biyu amma Belgium ta gane wayon.
Masar ta yi korafin samun bugun fenariti, amma ba a tsayar da wasan ba alkalin wasa bai ce komai ba an ci gaba da taka leda, kuma masu kula da VAR ba su ce komai ba
Yan bayan Masar sai lallai kam sun kula da Lukaku irin damar da suke bashi.
Domin dodan raga ne baya wasa.
Tawagogin sai kai kora suke amma har yanzu babu abinda ya sauya daga samakon wasan na 1-1.
An fitar da wannan ya ci mata kwallo, Emam Ashour da Mohamed Salah, inda Ramy Rabia da kuma Zico suka maye gurbinsu.
Belgium ta samu kwarin gwiwa ta sauya wasanta tun bayan da Lukaku ya shiga wasan, yayin da Masar ta koma tare gida ta rage wannan guje-guje da kwallon da take yi.
Watakila tana ganin ba laifi idan suka raba maki a tsakaninsu.
Belgium ta kawo karshen minti 325 ba tare da cin kwallo ba a gasar cin kofin duniya, mafi tsawo tun lokacin da ta yi minti 244 ba tare da cin kwallo ba daga 22 ga watan Yuni 1982 zuwa 3 ga waatan Yuni 1986.
Daga shigar Romelu Lukaku wasan har ya farke kwallon, amma dai kamar Masar ne suka ci gida, bayan da aka sharo kwallon daga gefe ta shiga gidan Masar kuma tsakanin masu tsaro baya biyu ya mika kafa, amma dai shi ne ya ci kwallon.
Wasan ya dauki zafi sai zubar da damarmaki ake yi a karawar.
Youri Tielemans ya nemi Kevin de Bruyne a tsakiyar gidan Masar, amma yana cikin matsin lamba sosai kuma ba samu damar sarrafa kwallon ba.
Masar ta ruga da gudu da kwallo zuwa ragar Belgium, amma ƙoƙari da Omar Marmoush na gudu da kwallo ya kare da ya buga ta yi sama, kuma ya samu matsin yan wasa biyu.
Nicolas Raskin da Maxim De Cuyper sun maye gurbin Amadou Onana da Timothy Castagne.
Kadan ya rage a ci Belgium, bayan da aka bugo kwallo daga gefen hagu zuwa gidan Belgium, sai Salah ya sa kai nan da nan golan Belgium ya sa hannu ya doke kwallon daga nan ta je wajen Ashour, amma da ya buga ta yi fadi da yawa ba wani hadari.