Abubuwa 6 da za su iya haramta maka yin zaɓe a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da babban zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara karatowa, masu kaɗa kuri'a na ta rubibi wajen ganin sun karɓi katunan zaɓensu domin samun damar zaɓar ɗan takarar da suke so.
Hukumar zaɓen Najeriya dai ta sanar da fara raba katin zaɓe na dindindin a watan Oktoban da ya wuce.
A gefe ɗaya kuma, ƴan takara na ta yaƙin neman zaɓe domin tallata manufofinsu a wajen ƴan Najeriya.
Sai dai, akwai wasu abubuwa da za su iya haramta wa mutum kaɗa kuri'a, kamar yadda dokar zaɓen Najeriya ta bayyana.
Abubuwan da za su iya haramta wa mutum yin zaɓe sun kunshi:
Yan ƙasa da shekara 18

Asalin hoton, Getty Images
Dokar zaɓen Najeriya da aka yi wa garambawul ta ginɗaya cewa duk ɗan ƙasar da bai kai shekara 18 ba, bai cika ka'idar yin zaɓe ba.
Don haka wannan rukuni na mutane na cikin waɗanda ba za su iya kaɗa kuri'a ba a Najeriya.
Rashin yin rajista

Asalin hoton, INEC
Wane abu kuma da zai iya haramta wa mutum yin zaɓe shi ne rashin yin rajista a hukumar zaɓen Najeriya.
INEC na gudanar da rajista ne domin ɗaukar bayanan masu son kaɗa kuri'a.
Saboda haka, duk wanda ke son yin zaɓe dole ne ya yi rajista, ya karɓi katin zaɓe wadda za ta za ta nuna shaidarsa ta kaɗa kuri'a - su kuma tabbatar sunansu na cikin kundin masu rajista.
Waɗanda ke tsare
Kawo yau, INEC ta bayyana cewa duk mutumin da ke tsare ba shi da hurumin yin zaɓe.
Hakan na nufin cewa duk mutum da ya aikata laifi sannan aka aika shi gidan yari ko kuma ke tsare a wurin ƴansanda, to kaɗa kuri'a ya haramta a kansa lokacin babban zaɓe.
Ma'aikata na musamman

Asalin hoton, AFP
Ma'aikata na musamman ba su da damar zuwa wurin zaɓe don kaɗa kuri'a.
Duk da cewa doka ba ta haramta musu yin haka ba, amma yanayin aikinsu ba zai iya ba su damar zuwa rumfar zaɓe ba.
Alal misali, ma'aikata kamar jami'an tsaro, ma'aikatan zaɓe, likitoci da kuma ƴan jarida ba su da sukuni zuwa yin zaɓe.
Ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje
Dokar zaɓen Najeriya ba ta ware wa ƴan ƙasar mazauna waje wani gurbi nakaɗa kuri'a ba lokacin yin zaɓe.
Ana aika masu zaɓe zuwa wuri ɗaya ne kacal wato rumfar zaɓe don gudanar da zaɓe.
Babu wanda yake da ikon yin zaɓe a wani wuri na daban, wanda ba hukumar zaɓe ce ta tanade shi ba.
Wanda ba a tantance ba
Ko da kana da katin rajistar zaɓe a Najeriya, matuƙar ba a tantance ka a ranar zaɓe ba, ba za ka iya kaɗa ƙuri'a ba.
Dokar zaɓe ta tanadi cewa wajibi ne mutum ya bi matakan da aka tsara wajen ganin an tantance shi kafin ya samu damar kaɗa ƙuri'a.
























