Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda man bilicin ya lalata wa wata budurwa ƙoda
- Marubuci, Gurpreet Kaur Saini
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
'Yan sanda a jihar Kerala da ke Indiya sun shigar da ƙara kan wani kamfani da ke haɗa man shafawa na ƙara hasken fata, bayan rahotanni sun nuna cewa amfani da man ya jawo wata mummunar cutar ƙoda ga wata yarinya mai shekara 17.
Likitan da ya kula da yarinyar ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa ta kamu da wata cuta da ta lalata aikin ƙodarta na tace jini. A cewarsa, ana zargin cutar ta samo asali ne daga sinadarin mercury mai guba da aka yi amfani da shi wajen haɗa man.
Ba a bayyana sunan yarinyar ba domin kare sirrinta. Rahotanni sun ce ta sayi man ne bayan da ta ga tallarsa a kafafen sada zumunta, tana neman maganin ƙurajen fuska da tabo.
Masana harkokin lafiya sun yi gargaɗi cewa wasu daga cikin ire-iren waɗannan mayukan na iya ƙunsar abubuwa masu guba. Sai dai ana sayar da su ta WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta, lamarin da ke sanya wa hukumomin gwamnati wahala wajen sa ido kan kamfanonin da ke samar da su.
Asibitin Aster MIMS Mother Hospital da ke unguwar Malappuram ya bayyana cewa an gudanar da gwaji kan wani samfurin man da yarinyar ta yi amfani da shi.
Sakamakon gwajin ya nuna cewa man yana ɗauke da adadin 12,500 na mercury. Wato daga cikin sassa miliyan ɗaya na man, sassa 12,500 mercury ne. Wannan adadi ya ninka iyakar adadin mercury da aka amince a samu a kayan da ake amfani da su wajen haskaka fata, wanda bai kamata ya wuce guda ɗaya kacal ba.
Likitan cututtukan ƙoda na asibitin, Dr Satish K, ya ce an gano yarinyar na fama da wata cuta da ake kira Membranous Nephropathy. Cutar tana lalata ƙoda ta yadda ba za ta iya tace jini ba, kuma yana zubar da sinadarin protein mai gina jiki da yawa ta hanyar fitsari.
Ta yaya yarinyar ta fara rashin lafiya?
Matar ta ce ta fara sayen man ne ta kafafen sada zumunta kusan shekara guda da ta wuce. A cikin wannan lokaci, ta sayi robobi uku na man.
Ta shaida wa Onmanorama cewa kamfanin ya yi iƙirarin cewa man, wanda ake shafawa kowane dare, zai taimaka wajen kawar da ƙurajen fuska da daidaita launin fata. Kamfanin ya kuma ce za a ga sakamako idan aka ci gaba da amfani da shi a kai-a kai.
Sai dai bayan watanni da dama tana amfani da man, yarinyar ta fara fama da gajiya, ciwon kai, jiri da rashin barci. Haka kuma fuskarta da ƙafafunta suka fara kumbura. A cewarta, a wani lokaci har ta fara samun wahalar tsayuwa da kyau.
Asibitin ya ce iyayen yarinyar ne suka kawo ta asibiti bayan da ta kamu da matsananciyar kumburi da wasu matsalolin lafiya.
A lokacin fara jinyarta, bayan likitoci sun lura cewa matslalointa na ƙara tsananta fiye da yadda aka saba gani, sai suka fara zargin cewa akwai wani sinadari mai guba a jikinta.
Gwaje-gwajen jini da sauran binciken lafiya sun nuna cewa akwai sinadarin mercury mai yawa sosai a jikinta. Daga nan ne likitoci suka ɗauki samfurin man da take amfani da shi domin a yi masa binciken ɗakin gwaje-gwaje.
Asibitin ya ce gwajin ya tabbatar da cewa adadin mercury da ke cikin man ya zarce nesa ba kusa ba na matakin tsaro da Hukumar Kula da Ka'idojin Magunguna ta Indiya (CDSCO) ta amince da shi ga kayan kwalliya.
Daga nan likitoci suka ba ta magungunan da za su taimaka wajen fitar da gubobi daga jikinta, tare da kula da matsalar kodarta.
Bayan kusan wata guda a asibiti, an sallame ta zuwa gida. Yanzu haka tana gida tana hutawa tare da ci gaba da samun sauƙi.
Sai dai yarinyar ta shaida wa BBC a ranar Litinin cewa har yanzu tana fama da wasu matsalolin lafiya, kuma tana fuskantar ƙalubale wajen ci gaba da karatunta.
Dakta Satish ya ce lafiyarta na ci gaba da inganta a hankali tun bayan fara magani. Amma har yanzu ba ta murmure gaba ɗaya ba, kuma ana sa ran zai ɗauki lokaci kafin ta samu cikakkiyar lafiya.
'Yan sandan jihar Kerala sun fara bincike kan lamarin. Haka kuma Hukumar Kare Haƙƙin Yara ta Jihar Kerala ta shigar da ƙara a kan kamfanin da ya ƙera man.
Mene ne Mercury? kuma ta yaya yake da illa ga jikin ɗan'adam
Mercury wani sinadari ne da ake samu a muhallinmu.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), mercury na iya haifar da illa mai tsanani ga tsarin jijiyoyin jiki, tsarin narkar da abinci da kuma garkuwar jiki.
Haka kuma yana iya lalata huhu da ƙoda da fata da idanu.
WHO ta sanya mercury cikin jerin sinadarai goma da suka fi haddasa damuwa ga lafiyar jama'a a duniya, saboda haɗarin da suke tattare da shi.
Saboda haka masana lafiya suna gargaɗin mutane da su yi taka-tsantsan wajen amfani da man shafawa ko kayan kwalliya da ba a tabbatar da ingancinsu ba, musamman waɗanda ake tallatawa ta kafafen sada zumunta, domin wasu na iya ƙunsar sinadarai masu guba kamar mercury da ke iya yin illa ga lafiya.
Me ya sa ake amfani da sinadarin mercury a man ƙara haske?
Mayukan ƙara hasken fata ko sauya launin fata wasu mayuka ne da ake tallatawa da ikirarin cewa za su sa fata ta fi yadda take a da haske.
Fata tana ɗauke da wani sinadari mai suna melanin, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bai wa fata launinta.
Wasu daga cikin mayukan sauya launin fata suna amfani da sinadaran mercury domin daƙile samar da melanin a jiki.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana abubuwan canza launin fata da ke ɗauke da mercury a matsayin barazana ga lafiyar jama'a. Kasashe da dama sun haramta irin waɗannan kayayyaki, amma har yanzu ana ci gaba da sayar da su tare da tallata su ta intanet da sauran hanyoyi a wasu sassan duniya.
Masana lafiya sun yi gargadin cewa amfani da man da ke ɗauke da mercury na iya janyo matsaloli masu tsanani ga lafiya, ciki har da lalacewar koda, jijiyoyin jiki, fata da idanu.
Ta yaya mercury ke lalata ƙoda?
Ƙoda na tace datti da da jiki ba ya buƙata daga cikin jini, sannan ya fitar da su ta hanyar fitsari. Ƙananan sassan koda da ke gudanar da wannan aikin tace jini ana kiransu glomeruli.
Waɗannan sassan suna tace datti daga jini, tare da taimakawa wajen riƙe sinadaran furotin masu muhimmanci da jiki ke buƙata a cikin jini.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), amfani da sinadarin mercury a jiki na iya lalata ƙoda. Illolinsa na iya kasancewa daga zubar da yawan furotin ta hanyar fitsari har zuwa gazawar ƙoda gaba ɗaya.
Dakta Ravi Bansal, babban ƙwararren likitan cututtukan ƙoda a asibitin PSRI da ke Delhi, ya shaida wa BBC News Hindi cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata ya ga marasa lafiya da dama da suka yi amfani da mayukan ƙara hasken fata, inda jikinsu ya samu matsala wanda ya shafi kododinsu.
A cewarsa, a wasu daga cikin waɗannan marasa lafiya, an gano suna fama da cutar Membranous Nephropathy.
Dskta Bansal ya ce abubuwa irin su mercury na iya shiga cikin jiki ta fata. Daga nan kuma su lalata ƙoda da sauran sassan jiki.
Ya kuma ce idan mutum ya fara fuskantar: kumburin ƙafafu ko hawan jini ko yawan tashi da dare domin yin fitsari, musamman idan waɗannan matsalolin sabbi ne a gare shi, ya kamata a yi masa gwajin duba lafiyar ƙododinsa domin gano ko akwai wata matsala tun da wuri.