An mayar wa Senegal kofin nahiyar Afirka bayan nasarar daukaka kara, Afcon Morocco 2025
An mayar wa Senegal kofin nahiyar Afirka da ta lashe a 2025, bayan Court of Arbitration for Sport (CAS) ta soke hukuncin da ya bai wa Morocco nasara da ci 3-0.
Senegal ta lashe wasan ƙarshe na AFCON da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci a kan Morocco sakamakon ƙwallon da Pape Gueye ya ci a ranar 18 ga Janairu na wannan shekarar.
Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Morocco ta shigar da ƙara ga masu shirya gasar, wato Confederation of African Football (CAF), tana neman a soke sakamakon wasan bayan da 'yan wasan Senegal suka fice daga fili, domin nuna rashin amincewa da bugun fenareti da aka bai wa Morocco a ƙarshen rabin lokaci a zagaye na biyu, jim kaɗan bayan an ƙi amincewa da ƙwallar da Senegal ta ci.
Zanga-zangar Senegal ta janyo jinkirin minti 15, kuma bayan da 'yan wasan suka koma fili ne, Brahim Diaz na Morocco ya kasa cin fenaretin, lamarin da ya sa wasan ya tafi ƙarin lokaci.
Da farko an yi watsi da ƙarar da Morocco ta shiga, amma daga baya wani kwamitin CAF ya amince da bincikar lamarin, inda ya yanke hukuncin cewa ficewar Senegal daga filin wasa na nufin ta yi watsi da fafatawar, sannan ya bai wa Morocco nasara da ci 3-0.
Daga nan Senegal ta kai ƙarar zuwa CAS, wadda ta saurari hujjojin ɓangarorin biyu a ranar 8 ga watan Oktoba. Yanzu kotun ta dawo da asalin sakamakon nasarar Senegal da ci 1-0.