Pochettino ya fara jan ragamar United da fuskantar kalubale, Manchester United

Asalin hoton, Getty Images
Mauricio Pochettino ya fara aikinsa na farko a matsayin kocin Manchester United da rashin nasara 4-0 a hannun Liverpool ranar Lahadi a gasar Premier League a Anfield.
United ta buga mafi yawan lokacin wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan an kori Leny Yoro saboda laifin da ya yi wa Alexander Isak a minti na takwas da take leda.
Liverpool tana matsayi na huɗu a teburin Premier League, maki bakwai tsakani da Arsenal mai jan ragamar teburi.
Ita kuwa United tana matsayi na 19, maki ɗaya kacal sama da ƙasan teburin gasar.





